9

578 21 0
                                    

💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫

        ✍🏻M SHAKUR

9️⃣

Wuraren 5 Baba ya shigo da kanshi yatadata don sallan asuba, da kyar ta tashi saida yaga tashiga bayi sanan yajuya yafice, tana idar da salla da kyar ta iya lallabawa takoma gado sai wani baccin.

Wuraren 11:30 ta tashi daga bacci, ita kanta wani dadin jikinta taji taji, ahankali ta tashi zaune tasauke kafanta kasa tana kallon dakin, dakinta very clean and very fine kana ganin dakin kaga dakin wacce akeji da ita, tashi tayi ahankali dagakan gado tai wajen window dakinta bude window tayi haske yawani daki fuskanta lumshe idanu tayi kafin ahankali tabudesu starring into compound dinsu that is very fine  idanunta suka sauka kan motar ta da ake pake agidan, faduwa gabanta yayi ganin yanda gaban motan yay completely baci, maida labulen tayi tarufe window feeling sad sai yanzu ta tuna abinda yafaru sanan tawuce tashiga bayi, wanka tayi tafito daure dawani pink towel, karasawa tayi gaban madubi takalli kanta kodan tayi bacci sosai ne gani tayi tana wani kalan sheki, fatarta nawani kalan glowing and sparkling, yatsine fuska tayi sanan tawuce tadauko kaya a wardrobe tasaka wani pink half gown na cotton, batama tsaya daura dan kwali ba tasaka slippers kawai tafito gabanta na dukan uku uku tsayawa tayi wajen bene taleka falo ganin Mama bata falo yasa ahankali tajuyo tai gaban dakinta, tsayawa tayi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tasa hannunta tai knocking ahankali, jin baaa amsaba kuma ta tabbatar Mama naciki yasa ahankali tabude kofan dakin tadan leka tana shiga ciki, hada idanu tayi da Mama dake zaune kan couch na dakin tana karanta wani Littafin zikiri dake hannunta, babu ko alamun wasa akan fuskanta tace "fitan min daga daki Ummulkhair" dan rau rau tayida idanunta kaman zatai kuka murya chan kasa kaman na Yar baby amugun shagwabe tace "Mamaaa sorrry please, kinj...." "Get out of this room Khairy" gyadama Mama kai tayi ahankali sanan tajuya tana tafiya kaman wacce ke koyon tafiya tana tunanin abinda zatayi Mama tahakura kaman daga sama Mama kawai taji Khairy taja wani uban nishi tana bubbuga kirjinta tayi baya zata fadi, wani kalan salati Mama tasaki tawani ijiye Littafin kan kujera ta taso dasauri ta tareta da hannayenta tace "Subhanallahi Khairy, Khairy, ina inhaler ki"? wani kalan dadi taji ya lullube ta ganin yanda Mama harta tsorata ta taso, kawai Mama gani tayi yarinya ta kankameta tafashe dawani sangartaccen kuka ajikin Mama tace "Mama please kiyakuri wlh wlh bazan kara abinda nayi jiyaba I promise Mummy, kikai fushi dani ina zansa kaina eh kinaso in mutu ne da ciwo? U are my best friend Mama, u are my happiness kika shareni I will be shattered, Mama dan Allah kinji smile for me haba my world best, best of the best, bestest, the best Mama in the world, Mama dan Allah kiyafemin" tai maganan tana kara kankame Mama kaman wata yar yarinyar da baa dade da yayewa ba, dudda yanda ran Mama yake abace amman saida jikinta yay sanyi sosai, ahankali tadaga hannayenta taciro Khairy daga jikinta ta tsare fuskanta da idanu hardan rama tayi ga hawaye sun cika idanunta, Mama takai hannunta ta share mata idanu sanan takama hannunta tajata zuwa bakin gadonta zaunar da ita tayi sanan tazauna agefenta tana kallonta ahankali tace "Ummulkhair bakiji, ba fushi nake dake ba I am only trying na nuna miki kuskurenki, ke y'a mace ce bazaki dawwama agidan mahaifinki ba dole zakiyi aure kije gidan mijinki, i want to teach you not just life but how to live life Khairy, inaso nakoya miki rayuwa dakuma yanda ake zaman duniya lafiya, ke mace ce Baban ki da yayyinki cannot teach you abinda ni mahaifiyar ki mace zata iya koyamiki, akwai mutuwa, akwai ciwo, akwai kuma tsufa any of the two can happen to me Khairy yaya zaki kare eh? Kin taba tunanin, wanan kawayen yau baki bikin wanan gobe baki bikin wanchan kene aganki achan gidan bikin kina tika rawa ko achan birthday kina tika rawa ko Micheal Jackson yaganki kina rawa saiya baki fili yarinya saikace rainon dujal, what are all this behaviors Khairy? Sabida ana cewa ke yarinya ce kinsan yara nawa wanda ma kin girmesu sukai aure suka hayyayafa eh? Yanzu abin haryakai kija mota dakanki ki shiga titi da daddare Ummulkhairy idan da wani abu yasameki how do you want me to cope? Kasheni kikeso kiyi da damuwa?" Dasauri ta girgizama Mama kai ahankali tace "Mama bazan karaba wlh" Ijiyan zuciya Mama tasauke ahankali sanan tai murmushi tana kallon yanda idanunta sukai zuru zuru long kalaban kanta duksun barbaje sun sauko fuskanta, hannun Mama takai ta gyara mata gashin sanan ta shafa fuskanta tace "ke kadai ne y'a mace da Allah yabani aduniyan nan Ummulkhair, inaso ki natsu, wisen up, anything can happen to me, and I want you to be able to take care of yourself, su Manaf, Mu'az da Maheer, you will be their Mum, kindaiga banda kowa, I told dukanku labarin nan agidan marayu Baban ku yaganni ya auroni ina gidanshi nai karatu, bansan any family naba dazance yau idan bani inada wata danasan zata rikeminku tsakani ga Allah so I want you to take after me kinji, ki natsu and know what you are doing" fashewa da kuka tayi ahankali duk zuciyanta namata nauyi da duhu, bayan hannunta takai ahankali ta share idanunta sanan cikin sheshekan kuka tace "Mama maisa duk idan namiki laifi saikitamin magana kaman zaki mutu eh? Wlh Mama bazan karaba na rantse da Allah kinji, dan Allah kayakuri kuma kawayena zan ragesu, Mama I love you a lot please kidena fushi dani kuma kidena magana haka kinji, Mama you will leave long har yarana zaki goya" murmushi Mama tamata she just wish zata iya daina mata magana hakan, kumatunta taja cikeda so tace "oya stop crying inba hakaba I will snap your face natura a group dinku na nunama friends naki sugan cewa the famous Khairiry dinsu is a crying queen agida" dasauri tasa hannu tashare fuskanta ta washe jerin white teeth nata kananu dakeda bala'in kyau tace "Mama nadena" dan dariya Mama tayi tace "oya je bude drawer nan nawa ki kawo comb da kipiya ayi wanan tsifan" da sauri tasauka dagakan gadon tai wajen drawer dakin Mama tabi bayanta da kallo wani irin girma Khairy keyi da batasan ina zatada girma ba ga shape kaman ita tai kanta, daukowa comb da kifiyan tayi tajuyo Mama tabi damemmen cikinta da kallo tace "wuce kidebo breakfast kidawo" tai maganan tana karban comb din hannun nata, juyawa tayi tafita daga dakin koba komi ta lallashi Mama tahakura saura Baba shikuma da Baffa zata hadashi simple.

Dinning taje, plate tadauka tana bude kula, chips tadeba da sausage batare data taba kwan wajenba sanan takada tea tajera komi a tray tadawo dakin Mama, ganin Mama na rubutu da pen a dairy dinta wanda inda sabo tasaba ganinta tana yan rubuce rubuce aciki yasa tai murmushi ijiye abincin tayi anan kasan carpet sanan ta taso tazo inda Mama take tana kallon abinda take rubutawa da sauri Mama tarufe dairy tadago kanta tana hararanta tace "lpy" turo baki tayi ashagwabe tace "Mama handwriting dinki nake kallo fa, wlh Mama handwriting dinki yafi harna Baba kyau, inama nine nakeda fine handwriting haka, amman rubutuna kaman tafiyan tsutsa" hannu Mama takai ta dakamata duka a kafa tace "kincikani da surutu wuce kije kiyi breakfast kizo namiki tsifan" wucewa tayi tana dan dariya sanan tazauna tanacin abincin tana wasadashi kaman wata yar yarinya Mama kawai ta tasata agaba tana kallo, saida tagama sanan ta kwasa tafita dasu kafin tadawo Mama tahaumata tsifan kan.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now