20

534 20 1
                                    

2️⃣0️⃣
Free page

Wucewa yayi daidai lokacin wayanshi na ringing ganin Meena ce ke kiranshi yasa yamaida kanshi kan tukin inda yasan zai gansu chan yawuce, atsaye ya gansu da alamu shi suke jira, kashe motan yayi yafito yana kallon Gwaggo dake binshi da kallo ganin ya wartsake sosai yace "lpy" hararanshi tayi tace "munafuki nidai sani a mota" sata yayi a mota yana murmushi kasa kasa sanan yamaida kujeran boot su Meena suka saka ledojin abubuwan dasuka siya a boot sanan yarufe kowa yakoma yashiga motan yaja motan zuwa gida yana parking yafito baima tsaya bi takansu ba masallaci yawuce dan yasan zasu tafi da Gwaggo ciki.

Tareda Abba suka shigo gidan daga masallaci magidancin mutum ne yana sanye da suit baki dan daga wajen aiki yake, falo suka wuce, duk su Mami da yaran na falo gaida Abba duk sukayi, ganinshi yasa Mami tace "akawo abincin yanzu Alhaji" girgiza matakai yayi yay hanyar stairs yace "I am coming tukunna muje Aliyu" binshi Hydar yayi har zuwa sama wani babban falo suka shiga wanda kana gani kasan na Baban shine, zama yayi akan kujera Abba yazauna kusada shi yakai hannunshi yabude idanunshi yana haskawa dawani dan tocula dankarami yana dubashi, dan jim yayi sanan yace "you have typhoid Aliyu, I think zan saka on injections tunda bakason magani" yatsine fuska yayi ahankali yace "Abba wlh naji sauki, kainafa kadai ke ciwo kuma yadena" "yimin shiru my friend" Abba yay maganan yana tashi wani babban first aid box yadauko yabude sanan yahada wani allura Aliyu naji yana gani Abba yamai allura, sanan Abba yace "Aliyu this work is draining you, akan me u are a Barrister kawani kama kashiga aikin police with just mukamin ASP eh, why will you choose a police man job Son common talk to me" yay maganan yana kallon Aliyun cikeda damuwa, Aliyu ne kadai danshi namiji, yaranshi duka takwas aduniya, Aliyu ne nafarko he's 32yrs sai kannenshi mata guda bakwai hudu sunyi aure dukansu baa Nigeria suke aure ba Saura 3 agida suna school, ganin yay shiru yakasa cewa komi yasa ahankali Abba yace "tashi katafi, but make sure kaci abinci kafin ka kwanta kaji" gyadamai kai yayi sanan yatashi yawuce yabude kofa shikuma Abba yashiga cire kaya dan yay wanka duk bayajin dadi.

Yana fitowa da Mami yaci karo anan falon sama tana zagaye, kallo daya yamata yadauke kai yashiga sauka kasa itakuma tawuce tashiga falon Abban da sauri tanabin ko'ina da kallo dan Abba yariga yashiga bayi, ganin allura da first aid box abude yasa tasauke ijiyan zuciya taje gaban wardrobe tana budewa dan samoma Abba kayan dazai sa....
**

Tana komawa gida kayan jikinta tacire tayo wanka sanan tai salla tasauko kasa gabaki dayansu duk suna zaune a falo suna dinner gaida kowa tayi sanan tazo kusada Mama tazauna tana kallon Mama dataga tasaka sweater turtleneck black daya rufe har wuyanta tasaka hulan sanyi shima baki kafanta da bakin safa, kallonta Mama tayi jin ajikinta ana kallonta hannu tasa taja hancin tace "ke abinci zakici ko kallona kikazo yi" dan dariya kadan tayi tace "Mama sanyi kikeji ne AC akashe" gyadamata kai Mama tayi batare data bata amsan tambayan ba tace "mezan zubamiki" kallon abincin tayi sanan takalli madaran da Baba kesha tace "Mama madara zansha banson naci abinci" Madaran da Baba Kesha a cup da zafinshi ma yamika mata da sauri ta karba tana murmushi tace "thank you Baba" hararanta Mama tayi tace "kwadayi Khairy, aikin ki kenan tun kina Yar kankanuwan ki sabida babban ki kullum yanashan dafaffen milk kema kikesha" mikewa tsaye Baba yayi yace "bagashi nan saisa she's so bright ba ga kwanya, milk is good for children barin ma Wanan na Shanu damuke sha dababu mix, bari naje nai salla" yakalli su Manaf da duk suka tashi suma sukawuce suka tafi masallaci, madaran ta shanye tass sanan ta tashi ta tattara kayayyakin dasukaci abinci takai kitchen sanan tadawo tana kallon Mama dahar lokacin take zaune inda tabarta tace "Mama tashi mutafi sama" ahankali Mama tace "wuce kitafi akwai wani program na wa'azi dazan kalla yanzu za'a fara" sanin Mama da kallon tashoshin wa'azi yasa tawuce stairs abinta tace "Mama gobe zani saloon kitso good night" ahankali Mama tace "Allah yakaimu Khairy" saida taji bude kofanta tashiga daki sanan gently tasa hannunta tadaura kan kujeran dake gefenta tana kokarin tashi tsaye amman takasa idanunta sunyi jazur kana ganinta kasan tana wahala ita kadai tasan metakeji, komawa tayi tazauna ahankali sanan tasauke ijiyan zuciya, hawayen daya zubomata takai hannunta tashare tanajan hancinta jin majina ya tsinke mata kafin tasauko da hannun ta share majinan, sanan ahankali tasauke hannunta kasa tana kallon tafin hannayen nata dasukai jajir kaman wanda yaji ciwo, ajiyan zuciya tasauke majina na gangarowa daga hancinta sanan tadaura hannunta kan hannun rigan tajashi sama tana kallon fatan jikin hannunta dasukai jaaa wasu kalan kuraje dasuka fitomata sunyi dabbare dabbare sunyi chaaaaa wanda is not just hannu ko'ina ajiki suka fesomata har wuya saisa tasaka Riga turtle neck dankar Khairy tagani, hannu takai tashare majinan dataji yana gangaromata yakai mata baki sanan tadaura hannunta kan baki tana kuka mai bala'in tabarai, she don't even know why she's crying, tana zaune a inda take aka turo kofan falon aka shigo dago kanta tayi takalli kofan Baba ne yashigo, kallo daya yamata yagane kuka take maida kofan yayi yarufe sanan yakaraso ciki ahankali yazo gabanta tsugunnawa yayi sanan yakai hannunshi yakama nata yakai kan kafadarshi kafin ahankali yadagata tashi tsaye tayi da taimakonshi dan ayanzu sai an dagata an kuma kwantar she can't really do anything da kanta sabida, har yakaita daki bai iya cemata uppan ba, zaunar da ita yayi akan gado sanan yashiga bayi yadauko baho da buta da kanshi yamata alwala sanan yasamata hijabi kwantar da ita kan gado yayi sanan yace "pray" gyadamai kai tayi da idanunta dasukai jajir sanan tashiga yin sallan isha'i yana zaune gefenta harta idar sanan yacire mata hijabin.
Kashe wutan dakin yayi sanan ya kwanta gefenta yarufa mata bargo kafin yadaura kanta kan kirjinshi yanajin yanda jikinta yay zafi sosai, murya chan kasa tana kara kankameshi tace "nagode Baban su Manaf" gyadamata kai yayi yakasa magana har lokacin, hannunshi takama takai kan kirjinta ta manna sabida yaji yanda zuciyanta ke bugawa ahankali tace "kaji yanda zuciyana ke bugawa ko, tunanin yarana yasa haka, dan Allah ka kara aure banso daidai da sakan daya yarana suyi maraici kaji Baban Manaf" wata kalan huci kai zafi Baba yasaki ahankali yace "Maryam at this junction danake in my life banma da natsuwan dazan iya neman aure, yarana bazasu taba maraici ba, I am here, Baffan su nada mata har biyu they are sounded with mata they can call mom, please tunane tunanin nan will keep on eating u harsai kin daina, please concentrate on your health kinji, gobe zan kira Dr" girgizamai kai tayi tace "please no kabarshi yaje yay saving those that still have chance not me nariga naji ajikina my end is nea....." Kankameta sosai yayi ajikinshi yana huci mai zafi wasu thick tears na neman fitomai daga idanu ya hadiye su ahankali yana jijjigata ahaka bacci yay awon gaba da ita saida ya tabbatar tai baccin sanan yatashi ahankali gyaramata bargo yayi sanan yawuce yashiga bayi alwala yadauro yazo yahau kan dadduma shafai da wuturi yayi yamata addu'a sanan yakoma gado kusada ita ya kwDanta.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now