28

740 21 1
                                    

2️⃣8️⃣

Free page
Shiga motan Aliyu yayi dasauri sanan yatada motan wani irin jan motan yayi da bala'in gudu yayi tafiya mai bala'in tsayi sanan ya gangara gefen hanya ya kashe motan kafin yawani irin daki siterin motan yace "noooooo" he just wish zai iya shiga cikin gidan yaganta, wayanshi yaciro dasauri idanunshi sunyi ja baimasan mezaiyi ba text yashiga turamata.
"Rashin uwa is not something I wish for even my enemy, but muna plan dinmu ne Allah is the master of all planners. Ummulkhair nasan mekikeji, I know abinda zuciyanki kije because I was once there, just know this wherever Mama is she's resting, tana cikin jannatul Firdaus, I want you to calm down, pray for Mama, cry but just little sabida nasan it hurts alot, babu wanda zai gane how it hurts sai ke, so cry little and pray lot, be strong for me Khairy, and kisani cewa I am here for you koda bana wajen presently but my love and my heart is there with you, I love you to the moon and back Ummulkhair, Allah ya yassaremiki wanan nauyin dakikeji aranki"
Turamata text din yayi yadade ahaka sanan yafuzar da iskan yatada motanshi yawuce.

Bayan sallan magrib Mom da kanta tashigo dakin, Khairy na kwance kan gado tadagota tana kallonta tawani irin rame tace "muje gidan mu, bayan kwana biyu saiki dawo nan bari nakawo miki hijabin ki" bin Mom kawai take da idanu tadauko mata hijabin tazo har gaban gadon tasake dagota danta kara kwanciya tasaka mata hijabin dagota tayi tasauko kasa baya tayi kaman zata fadi dasauri Mom tariketa tana kallon fuskanta idanun idanunta sukai suntum har lokacin jikinta da zafi ahankali tace "kiyakuri Khairy, kiyakuri" fita da ita Mom tayi tana binta luuu kaman wacce tasoma zarewa duk su Baba da kowa na tsakar gida wajajen mota Mom tafito da ita binta da kallo sukayi, dafa Baba Baffa yayi dayaga yana kallonta cikeda tausayi yace "don't worry she will be fine" karasowa wajen Mom tayi tasata acikin mota bata musu duk yanda akai da ita, kowa shishiga mota yayi Baffa yana su Baba sallama sanan suka tafi da ita.

Suna kaiwa gidan parking suka yi, Zayn yafara saukowa daga motan Ammi side dinshi yawuce dan yagaji he needs rest, Mom kuma tafito da Khairy dahar lokacin take yanda take, Ahankali Baffa dake kallonsu yace "kitafi da ita side dinki tunda akwai Batool" gyadamai kai Mom tayi tawuce da ita itakuma Ammi tadaure fuska tawuce abinta Baffa yabi bayanta yana amsa wayan daya shigo phone nashi.

Kafin suma iso Batool tabude musu kofa tana kallon Khairy dan ita all this while bataje gidan rasuwan ba tana gida tana kulada kannensu, zata fashe da kuka ganin Khairy Mom ta ballamata harara hakan yasa tahadiye kukan taya Mom riketa sukayi sukai sama da ita zuwa dakinsu zaunar da ita kan gado sukayi kwanciya tayi sharaf Batool zatai magana Mom tace "ki barta jekimin tea yanzu zanzo nabata tasha yauma bataci komiba" Gyadamata kai Batool tayi tafito daga dakin tsayawa tayi nan bakin kofa tana kuka ahankali, bude kofa Mom tayi tafito ganinta yasa Mom taidan jim sanan tace "kinsan wahalan da akasha kafin Khairy tadaina kuka? Tana ganinki kina kuka yanzu zata fara" Mom tai maganan tana janta daga wajen kofa sukai stairs, cikeda da bala'in tausayi Batool tace "Mom kaman na Khairy mai surutu ba Mom kaman tazare Innalillahi, duniyan nan babu komi cikinta Mom, look at Khairy damuka sunan Ya Hafiz da ita muna wasa muna rawa, Mom I can't stand seeing her this way" ahankali Mom tace "then u should support her as ur sister, show her love abinda take bukata kenan yanzu, sanan mudena nuna mata muna tausayinta, kijata ajiki u will help her tadawo daidai" gyadama Mom kai tayi, Mom tace "good yanzu jekiyo mata tea kizo kibata tasha, lemme go and shower" wucewa tayi zuwa kitchen da sauri.

Tea Batool tahado mata tadaura cup din a tray tadawo dakin nasu tana kwance sharaf agadon yanda suka barta, ijiye tea tayi tahayo gadon tadagota ta tashi zaune ahankalli murya chan kasa tace "Khairy zoki sha tea bakici komi ba" tsare Batool tayi da idanu da dazaran kaga yanda take kallon Batool kasan bata hayyacinta don ahankali tace "ina Mama"? Danne kukan datakeji tayi zatai mata magana taji kukan yatokare mata wuya hawaye yazubamata dasauri tashare daidai Mom tashigo hararanta Mom tayi tadauki tea tace "tashi kibani waje" da kyar Mom tasamu ta kurbi tea sau biyu sanan takara kwanciya dagata Mom tayi takaita bayi alwala tamata tasata a dadduma salla tajirata tayi Allah dai ya karba sanan tadagata, wani sabon kayan bacci na Batool Mom ta dauka tasamata bayan tacire mata atampan jikinta spaghetti hand ne dan kaman shimi yake iya guwiwanta ya tsaya mata pink color dan itama Batool nasan komi pink, dawowa tayi kaman wata Yar baby roba akayan looking damn cute, kaita Gado Mom tayi ta kwantar da ita tarufa mata bargo itama kaman abinda takeso kenan rufe idanu tayi dasauri, Mom tazauna abakin gadon tana tofamata addu'a bude kofa akayi Baffa ne yashigo yana sanye da jallabiya ganin Mom namata addu'a yasa ya tsaya yana kallonsu saida tagama sanan yace "tai salla"? "Eh tayi" "what about abinci" Baffa yatambaya anatse, ahankali Mom tace "tasha tea kadan ba laifi, shine na chanza mata kaya nakwantar da ita, karka damu she will be fine nan bada jimawa ba" murmushi Baffa yayi yana kallon Mom ahankali yace "thank you mace tagari" yakalli Batool dake bayanshi tai zuru zuru yace "dama kuka zaki dingayi kika dameni nadawo da ita nan kisami Yar uwa" dasauri ta girgiza kai tace "Bazan karaba Abba" murmushi yayi yashafa kanta yace "jeki kwanta" sanan yakalli Mom yace "jeki kwanta kihuta wife muje narakaki" murmushi tayi ta tashi, itakuma Batool taje gefen Khairy ta kwanta itama tashiga bargon Baffa yakashe musu wuta tareda jawo musu kofa sanan yaraka Mom zuwa dakinta kafin yafito yasauka kasa yakashe wutan falo sanan yaja kofan yawuce side din Ammi.


Wuraren karfe biyun dare tabude idanunta tass jin muryan Mama nakiran sunanta. "Ummulkhairy!" Hakan yasa tabi dakin da kallo ganin Mama tsaye jikin kofa tana sanye da Atampa mai kyau tai lullubi yasa ta yaye bargon data rufa dashi tawani tashi tsaye tai wajen kofan bakinta na motsi, gani tayi Mama tabi ta kofan tafice bude kofan tayi dasauri tafita ko'ina duhu but she could see Mama natafiya akan stairs dan fararen kayane ajikinta, hanyar stairs din tayi itama dasauri ganin Mama tai kofa tafice yasa itama tai kofan, hannu tasa tabude kofan tafice batare data rufe kofan ba, tsakar gidansu kaman rana sabida ko'ina hasken lantarki tashiga sauka daga stairs din gaban kofan tana mika hannu ganin Mama tamata nisa tai hanyar gate murya chan dake cikeda nuna alamun bacci tace "Mama jirani!"

Zaune yake kan daya daga cikin wasu hadadun kujerun dayake nan barandan flat dinshi, irin hadadun kujerun basket dinan da ake sawa a garden, dagashi sai wani gajeren wando dayakaimai guiwa da farin singlet tass yadaura kafafunshi kan class table din wajen yana shan shishi, tunda yadawo naija saiyau yasamu yakeshan shisha, yama fito waje ne yanasha sabida kar dakinshi yakama kamshin gashi Abba nashigowa dakin dakannenshi duka, jin karan kofa an bude flat din Mom dan daga flat din Mom sainashi at this hour of night yasa yasaki pipe din shishan kasa dasauri yana mika hannu yana sauke shisha pot din daga kan table din at the same time yana kallon kofan yaga wanda zai fito daga dakin.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now