18

587 24 1
                                    

1️⃣8️⃣

Free page
Wuraren 3 na rana yafarka, ahankali yake bude idanunshi yanabin dakin da kallo jin anrike hannunshi yasa yajuyo da kanshi ahankali wata yar budurwa ce da zatakai 22yrs zaune gefen gadon dake bala'in kama dashi kana ganinta kasan kanwanshi ce takama hannunshi gam tarike tanadan gyangyadi, tana sanye da doguwan rigan atampa, Meena kenan he's sure Gwaggo ce tagayamata baida lafiya saisa tataho daga dawowanta daga school, dan murmushi yayi sanan ya fizge hannunshi da karfi afirgice tabude idanunta takalleshi tana kara ware idanu tace "Ya Hydar katashi sannu yajiki" hararanta yayi yace "meya kawoki dakina" cikeda damuwa tace "yanzun nan muka dawo daga school muka tarar Gwaggo na kuka wai batada lafiya shine nazo naga kana bacci, cha tayima na sata a keke nakawota wurinka nasan damunka kawai zatayi saisa naki" dan jim yayi yace "jeki cemata tadena kuka I am fine" murmushi tayi sosai tana kallonshi tana kokarin tashi  dagakan gadon tace "Ya Hydar kanason Gwaggo amman kullum fada kukeyi baka nuna mata kana sonta maisa" hanyar bathroom dinshi yawuce yace "kafin nafito kibarmin daki inba hakaba jikinki zai gayamiki" tashi tayi ranta namata dadi ganinshi lafiyanshi kalau tace "Ya Hydar zaka kaimu Jabi lake mall din? Kagama sai Gwaggo takara yarda lafiyanka kalau ko" "go and get ready" yafadi murya chan kasa duk ya gaji yakosa tabar dakin dansai sashi surutu take, shigewa bathroom din yayi abinshi yamaida kofan yarufe, tashi tayi cikedajin dadi tai hanyar fita, sai yanzu tama lurada riganshi akasa dakin tsugunnawa tayi tadauka sanan tamakalamai a hanger tabude wardrobe dinshi tasaka tawuce tafice danta gayamusu su shirya.

Yadade abayin sanan yafito wani simple jallabiya yasaka yay salla sanan yatashi ahankali har yanzu kanshi namai ciwo sosai daurewa kawai yake, shiryawa yayi cikin wani milk yadi mai bala'in taushi danshi baya iyasaka kaya masu karfi, feffesa turare yayi sanan yadauki wayanshi yana dubawa ganin baida miss calls yasa yafito yana tafiya one one, tundaga gaban kofan dakin Gwaggo Meena ke kallonshi ganin yay wani kalan kyau tana murmushi ohh God duk duniyan nan batada wanda takeso kaman Yayanta Hydar, hararanta yayi alamun kallon fa wuce kigayamusu su shirya hakan yasa tawuce tashiga dakin Gwaggo tana kallon Gwaggo dataci gayu itama tana zaune kan tabarman data shimfida akan lafiyayyen carpet din dake falon, girgizakai kawai yayi baitaba ganin rigimammiyan tsohuwa irin Gwaggo ba, gatada carpet amman tsabagen kauyanci saita shimfida tabarma akai, idanko yawone ko jikokin nata wani zubin da gangan sukekin gayamata zasu fita dan tsohuwarnan Allah ya zubamata son zuwa yawo kaman taci kafan kare.
Wasu yammata guda biyu ne zaune agefenta suma kyawawa dasu Amal dakuma Khadija duk sunci gayu kansu daya, zama yayi abinshi Gwaggo tabishi dakallo bata kulashi ba shima bai kalleta ba yakalli su Amal dake kallonshi suna gaidashi yace "kawomin abinci" tashi Amal tayi dasauri zata fita yace "ina zaki"? Ahankali tace "falon Mami zani nadebo maka" girgiza mata kai yayi yakalli fuskan Gwaggo yace "bani na Gwaggo" daure fuska Gwaggo tayi takalli Amal tace "jeki uwardaka na abincinshi na cikin kula sabida ku na boye kafin ku cinye mai yara saikace mayu barinma wanchan mai idanun kutaren" tanuna Meena tabe baki Meena tayi daga ita har Khadija, Amal tawuce tadauko mai takawo, kafinma Gwaggo tai magana Khadija ta tashi tadauko mai ruwa da drink daga fridge na Gwaggo ta kawomai bude abincin yayi dambu ne lafiyayye yanasan dambu hakan yasa yaci ba laifi Gwaggo tana zaune tana kallonshi ganin yadanji sauki yasa hankalinta ya kwanta sosai saida yagama ci sanan suka kwashe kayan sukai kitchen dashi shikuma yafice suka biyoshi abaya suka fito Gwaggo natafiya ahankali dan kafafun sun dawo a lallaba bata iya tafiya sosai saisa ko'ina za'aje da ita da keken guragun ta tareda ita.

Mami suka gani a tsakar gida kan wani hadadden chair da table agabanta tadaura kafanta kan table din Yar aikinta na gyaramata nails na kafa tana danna wayanta tana tauna cingum tana murmushi, jin sahun tafiya yasa tadago kanta binsu tayida kallo tace "Hydar daga kannenka sai Kakar ku kakeso nibaka sona saisa ba'a taba fita dani ba" tai maganan tana kallon Aliyu dayamayi gaba abinshi kaman badashi akeba, kaman jira Gwaggo take taballamata harara tace "akanme zai soki ke kika haifeshi jimini ikon Allah" dan dariya Mami tayi tai kara da cingum dinta tace "Hajiya Gwaggo maida wukan a dawo lpy" "Mami mun tafi" yaran suka mata sallama, "saikun dawo" Mami ta amsa yaranta tana murmushi tabisu da kallo  tana hararan bayan Gwaggo, saida sukai nisa sanan ahankali tace "Allah yakasheki mayyar tsohuwa kawai na huta, mata takai kusan shekaru dari amman taki mutuwa" tana zaune tana kallonsu yaja mota suka wuce sukabar gidan.

On a normal speed yake tuki yau danji yayi kanshi yasoma ciwo sosai amman yadaure dan baiso Gwaggo tagane ballema tadamu, ahaka harsukakai jabi lake mall din wuraren 5:30. Parking yayi wurin parking sanan suka fiffito, ganin yazauna aciki yasa Gwaggo tace "muje mana" yatsine fuska yayi yafito yabude boot yaciro kekenta yana sata akai yace "zan jiraku anan akwai wayoyin office dazanyi" yay maganan yana bama Meena ATM card dinshi yace "idan kuka kararmin dakudi Abba zansa yabiyani da monthly allowance dinku" dariya sukayi sanan Meena ta tura Gwaggo suka wuce tace "bye Ya Hydar" shiga mota yayi yazauna tareda kwantar da kujeran yana kara karfin Ac sanan ya kwanta kanshi najuyawa ya tsani rashin lafiya saisa baimaso ya kwanta ma wanan, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yanaji zuciyanshi natashi cikinshi najuyawa kaman zaiyi amai, jin amai yazomai dawani irin sauri ya yunkuro yabude kofa yafito sai amai, kwaro amai yashigayi anan wajen motanshi sosai idanunshi sukai ja.....

Ahankali ita kadai take tafiya a parking lot din wayanta na kunnenta tana sauraron kwatancen da Glory kemata na inda venue su yake acikin wajen, bakaramin kyau tayiba tana sanye dawani english gown daya kaimata har kasa red yabi jikinta sosai ya bala'in fito da shape nata dudda bawani kamata yayi ba amman sabida kalan yadin yasa yanayin jikinta yafito, fuskanta yay wani kalan kyau yana glowing dudda bata shafa hoda ba dan ita hoda nasata kuraje a fuska saisa tama daina sawa but ta gyara eyebrows dinta sanan tasa kwalli dayawani irin haska fararen idanunta suka fito wallll, sai pink lipstick data kara kan pink lips dinta dayasa lips dinta yay wani kalan crazy baby pink daya kara fito da fuskanta sosai, ta gyara gashinta daya gama hargitsewa tai styling frontal hair din da gel dudda dama gashinta a kwance yake but karawa da gel datayi yasa tai kyau fuskanta yafito sosai takawo wasu simple pearls earring silver tasaka, tayana light peach karamin veil akanta dayadan zame kadan kasa sabida iskan da akeyi uwa za'ai ruwan sama gashi bahadari just that garin is looking damn cozy, tasaka heel dayama kafanta kyau silver dayafito da fine fine sexy toe nails dinta, tana tafiya ahankali tarataya wani karamin handbag na LV a shoulder ta sai goran bottle water na Eva data rike tasha kadan aciki dan she was thirty ahanya ma tasaya yanzun nan dazasuso.

Kaman daga sama taji kakarin amai na mutum chak ta tsaya at the same time taji kirjinta yawani buga dum! Tsayawa tayi chak sanan ahankali tace "ok I am coming now nagane wurin" katse wayan tayi sanan tajuyo tana kalle kallen inda take ganin bataga kowaba sai shiru dataji yasa tacigaba da tafiya abinta, karajin kakarin amai datayi yasa tasake tsayawa chak ita kanta she don't even know why take tsayawa amman kaman something is pulling her, komawa baya tashigayi ahankali tana waige waige kafin chan tahango wani Babban mutum dan that doesn't look like a small boy tsugunne in between wasu manyan jeeps guda biyu yabata baya yana amai, tsigan jikinta taji yawani tashi, tun tana Yar karaman Yarinya ta tsani taga mutum naciwo, part of the reason why kowa is her friend a school kenan inhar Khairy tasan u are sick to far she die there Khairy is damn caring idan mutum naciwo saitamafi mai ciwon damuwa.

Takai almost 20second tsaye tana kallonshi yanda yake amai tsigan jikintai natashi tun yana amai abu na fitowa har kawai amman yake babu abinda kefitowa, ahankali tadaga kafanta zata wuce ta tafi samin kanta tayi dasake juyowa takalli bayanshi sanan takalli bottle water hannunshi kafin ahankali tana tafiya gently tawuce lungun motoci adaidai bayanshi dab dashi ta tsaya tana kallonshi bakinta nadan rawa dan tsoroma takeji mutum na amai tazo meruwanta amman still tadaure ahankali tace "Sir do you want some help nakira maka security"? Batare daya kalleta ba koyajuyo ba ya girgiza mata kai alamun no, jitayi zuciyanta yamata wani nauyi kaman tai kuka tasake dukowa kanshi sosai anatse tace "but u are very very sick, do you want some water, I have water, here gashi" tai maganan da sauri tana budemai goran ruwan tana mikamai ta gaban fuskanshi, goran ruwan yabida kallo, murya chan ciki dabaya fitowa sosai yace "thanks" goran tabida kallo ganin bai karba ba yasa ahankali tace "ka karba ka wanke fuskan ka u will feel better, haka Mama kemin idan banda lafiya nai amai" jiyayi kanshi nawani irin ciwo, azuciye yawani juyo da jajayen idanunshi dake cikeda zazzabi yawani taso kaman zaki zai cinyeta baya tayi atsorace ruwan hannunta yafadi heel din kafanta ya turgude dawani dutse hakan yasa kafanta ya turgude tai baya zata fadi atsorace hannu daya yasa ya chapko hannunta dasauri yana kallon fuskanta da jajayen idanunshi kaman yanda itama a bala'in firgice take kallon fuskanshi kirjinta nabugawa fast fast lips dintaI narawa sosai ganin police man dinaCn ne.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now