30

1.9K 47 4
                                    

3️⃣0️⃣

This book is 1k pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank. Saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461.

LAST FREE PAGE
Bayan 3 weeks!
Yau 3 weeks kenan chip chip da rasuwan Mama, an dage sosai da addu'a akanta she's very very much better yanzu, tadena koke koken nan she's doing everything dakanta saidai she hardly speak, kome aka cemata saidai ta gyadakai tariga ta yarda Mama tarasu and babu abinda zata iyayi dazai dawo da ita, har yau bata iyacin abinci at all, saidai kadan kadan kuma shima liquid, once in a while Besty nazuwa har gidan Baffa dubata dan su Ya Manaf nema suka kawota gidan tasani, sanan Baba yabata number shi yanzu ma haka ance gobe zata koma school danta kira Baba next week zasu fara first semester 400 level exam sauran ta one semester tagama school hakan yasa aketa shiryamata har sababbin dinki Baffa yamata hadadun gaske Mom ma haka, just to cheer her up amman ina bin kowa take da ido dakuma kalman godiya shikenan.

Yau tun safe Mom dakanta ta shigo dakin ganinta zaune kan dadduma yasa tace "laaaa yar nan Oya maza tashi ki shirya yau kinada lectures 8 kika zauna yanzu har 7 yi maza tashi ki shiga bayi" batai musu ba tashi tayi tai bayi wanka tayi tafito, gani tayi Mom tamata arranging kayan dazata saka akan gado, wasu Riga da skirt ne na atampa cikin sababbin da aka dinka mata orange color ne atampa yanada flowers yan kanana brown, sai brown gyale tahada mata jakan makarantan ta da book sai wayanta da tuntuni aka kawomata gidan bata taba tabawa ba shima Mom dukta saka mata, shiryawa tayi tsaf, Mom tashigo dakin dauke da tea da chips tana kallon yanda kayan suka mata kyau dudda tarame sosai takalli kitson kanta tace "satin nan zamu kwance kan nan ayi wani kitso Khairy" takarasa ta ijiye abincin akan carpet sanan tadauki dan kwalin kayan tamata dauri mai kyau kafin tadauki tea tabata, karba tayi da kyar ta iya shan dan kadan sanan ta ijiye, ita kanta Mom batama iya tursasata taci abinci tashi tayi tadauki jakan a hannu da gyalen ahankali tace "natafi" binta Mom tayi tace "dan Allah Khairy kiyi karatu da kyau kinga jarabawa zaku fara next week karki fadi" Baffa suka gani afalo shima wa'azi yamata sanan yakaita har mota saida tashiga sanan yama Adamu alamun yatada motan yatada suka tafi, titi kawai takebi da kallo, jitayi hawaye ya gangaro mata dasauri ta share, she use to kullum saitaga Mama take tafiya school, school sukakai Adamu yay parking ganin taki tashi yasa Adamu yace "tashi kije class Khairy" kukan datake rikewa taji yazo mata fashewa da kuka tayi sosai tasa gyalenta akan fuska tana kuka shiru Adamu yayi takai kusan 20min sanan ta share fuskan nata da gyalen idanunta sunyi jazur tabude kofa tafita tana tafiya kaman iska ya kadata tafadi tarame babu abinda yarage ajikinta sai nono da hips, su kadai ne basu rame ba but wuyanta duk kashi idanunta sun fada ciki sosai, ahankali take tafiya yan makaranta su natareta suna mata gaisuwa gyadamusu kai kawai take tana wucewa dasauri dan bataso taita kuka ta tarama kanta mutane ahaka hartakai aji da lecturer ma aciki, baa hanata shiga ba hakan yasa tashiga taje tasami chan baya karshe chan tazauna ko abu daya bata ganewa ahaka aka gama lectures din lecturer tafita by 10, basuda wani lectures kuma sai 2, zagayeta yan ajin sukayi ana mata gaisuwa gyadamusu kai take tana danne zuciyanta, ganin yanda takeyi yasa class governor dinsu yace "dan Allah kubar Khairy tahuta let's go guys" fiffita daga ajin suka shiga yi, su Amal sukace "tashi muje cafe Khairy" ahankali tace "kuje ina zuwa" dan jim sukayi suna kallonta babu maison yatakurata hakan yasa duk suka tafi ajin aka watse ita kadai tarage aciki hakan yasa takifa kanta akan desk tahau kuka ita kanta she wants to stop the cry amman bata iyawa tadade ahaka ita kadai a class kaman aljana kanta akife akan table, kaman daga sama taji ance "Ummulkhair!!" Awani irin hankali take dago kanta daga table kafin tadaura jajayen rinannun idanunta kan Aliyu dake tsaye agaban ajin yana sanye da uniform na yan sanda yana kallonta, yarame shima idanunshi sunyi wani kala yana mata kallonda only heart dinshi zai iya sanar da mai kallon ke nufi, jitayi duniyan ya tsayamata chak duk wani bakin ciki emotions, tausayin kanta da sauransu sun taso mata sun tsayamata awuya, jikinta harwani rawa yake ganinshi dan she can't believe shine, wani irin tashi tsaye tayi tana kallonshi kaman yanda yake kallonta kallon dayana mata zuciyanta nafassaramata dawani irin gudu gyalenta na faduwa akasa tai wajenshi kaman dama shitake jira batai wata wata ba kawai tawani kalan fada jikinshi sai kuka sosai as if she ne dama asalin wanda takeso tama kukan, ahankali ya lumshe idanunshi yana feeling kukan datake in every single bone of his flesh, hannayenshi yadaga gently yay wrapping nasu around her back kafin yakai bakinshi saitin kunenta murya chan kasa yace "I am here for you Pickle, I am here" sake kankameshi tayi sosai cikin kuka tace "Ya Aliyu Mama....." murya chan kasa dake nuna he's with her, he's feeling what she's feeling yace "I know Pickle" takai almost 3min tana kuka ajikinshi sanan ahankali yacirota daga jikinshi yana kallon yanda take kuka hannunta yakama zuwa first kujeran dake ajin zaunar da ita yayi sanan ya tsugunna agabanta still yana kallonta, jikinta ko'ina rawa yake na kuka, hannunshi yasa a aljihu yaciro clean handkerchief dinshi yakai kan fuskanta yafara share mata hawayen murya chan kasa yace "shiiiiiii" shiru tayi tana kallonshi still, tass yashare mata fuskan harda hancin sanan yamike tsaye yay inda take zaune a ajin da, tsugunnawa yayi yadauki gyalenta daya fadi a tsakar class din sanan yakarasa yadauki handbag dinta sanan yadawo har zuwa inda take a zaune, gyalenta ya yafa mata aka yasauka har kan kirjinta sanan yamika mata hannunshi yace "let's go" kallon fuskanshi tayi kafin ahankali tasa soft hannunta cikin nashi yariketa gam sanan suka fito daga class din suna tafiya ahankali sai kallonsu ake amman ko ajikinshi har zuwa parking space, gaban motan yabude mata zama tayi tana kallonshi da jajayen idanunta sanan ya maida kofan yarufe kafin yazagayo yazauna wajen mazaunin direba yarufe motan yatada motan yafice daga school din da ita, sunyi tafiya mai nisa sannan taga ya tsaya gaban wani eatry ya shiga batasan meya siyoba yadai bude bayan motan ya ijiye komi sanan yadawo yatada motan, wani waje yakaita ita kanta duk zamanta a Abuja batasan wajen ba, duwatsu ne masu kyau ga kamshin ruwa awajen da alamun akwai water fall ciki, parking yayi sanan yakalleta yace "I am coming" fitowa yayi yabude baya yadauki ledan daya siyo musu dawani babban dadduman dayake dashi mai taushi sanan yashiga wajen baiwani dade ba yadawo, bude inda take yayi yasake saka hannu yadauki jakanta sanan yamika mata hannu ahankali tasaka nata ciki, saukowa tayi yamaida motan yarufe sanan suka shiga wajen, cikin dutse ne kaman cave sanan ga ruwa atsakiyan wajen yana gangarowa daga dutse babu kowa wajen, wajen is so serene and peaceful bakajin karan komi saina tauntaye dana karan ruwan dakuma kamshin ruwan dutse dakakeji.

Zaunar da ita yayi kan dadduman sanan shima yazauna yana facing nata, ledan yabude yaciro take away na biryani rice da rosted lamb sai ruwa mai sanyi daya siya yabude, ahankali yasa spoon din aciki sanan yadebo abincin a spoon yakai bakinta yana kallonta jitayi zuciyanta yawani tsinke wani sabon kuka yazo mata ahankali tashiga reramai kukan, jaaa idanunshi yayi sanan gently ya girgiza mata kai bude baki tayi yasamata abincin taci saiyau tasan ashe tanajin yunwa, kadan tarage abincin all through harta koshi kuka take, yanabata abaki tanaci tanamai kuka sanan yadauki ruwa yabata shima sha tayi sanan ya ijiye.
Ijiye komi gefe yayi sanan ya matso kusada ita ganin taki daina kukan cikin muryan lallashi da murya dake nuna asalin so da tsantsan so yace "I know! and it's okay I am here for you okay" gyadamai kai tayi tana sauke ijiyan zuciya, hannunshi yakai yakamo hannunta ahankali yadaura hannun nata kan kirjinshi yana kallon idanunta yace "can you feel yanda zuciyana ke bugawa sabida yasan kina cikin damuwa?" Gyadamai kai tayi ahankali murya chan kasa yace "I came to your house tun ranan ban sake samin kwanciyan hankali ba because I know my Pickle is not fine, I lost sleep, I lost peace, bana iya komi sabida ke, kinason zuciyata tabuga because of you ne"? Girgizamai kai tayi ahankali tanajin maganganunshi har a bargon kashinta, murya chan kasa yace "I lost my Mom when I was 25yrs, I know what u are going through Khairy, but if anything yasameki bazan iya rayuwa ba I will die, I love you alot, Ummulkhair I Love You" wani sanyi taji ya ziyarci zuciyanta each magana dayake gayamata zuciyanshi datakejin bugunshi nakara tantance mata cewa gaskiya yake fadi, ahankali yace "when I lost my mum I was depressed but as time goes on nazo ma fahimci this is not abinda mamana keso, she wants me happy, tanaso na cigaba da rayuwana, tanaso nai fulfilling dreams dina and above all she wants me happy and praying for her, Pickle abinda kikeyi yanzu is that abinda Mama kiso"? Girgizamai kai dasauri tayi alamun aa ahankali yace "to mesa kike hakan"? Lips dinta na rawa kuka na neman kufce mata tace "because banajin magana and nasa Mama fushi dayawa, halama saisa taki fadamin she had blood cancer" tafashe da kuka tana kallonshi girgiza mata kai yayi yace "Mama taki gayamiki she's ill ne because you are her youngest daughter Khairy u can't handle it, and Mama wants wats best for you, that's is the reason, trust me pickle you are not stubborn, ke y'a ce dakowani parent will wish to have, I know Mama is so proud of you, ta haifi selfless and fearless yarinya that can stand for her self a ko'ina, karki kara tunanin Mama is angry with u iyaye basa iya fushi da yaransu, and Wanan kukan dakike da rashin cin abinci shizaisa Mama tai fushi dake, cus instead of kinata addu'a kina using time din to cry and not eating zai baki wani sabon ciwo u want to be sick" girgizamai kai tayi dasauri ahankali yakai hannunshi yakama dayan hannunta yace "promise me daga yau kin chanza, u will stop all this, take care of yayyinki and your Dad, do you have any idea yanda sukeji ga rashin Mama gaki" sake girgizamai kai tayi yace "promise me you will change daga yau, u will always pray for Mama, study well and pass exam dazaku fara next week, did u promise" gyadamai kai tayi ahankali tace "Uhm I promise" murmushi yayi he feels kaman yarungumeta yasata ajikinshi and just stay like that forever" ahankali yace "smile for me i finds it healing is my therapy, smile" dan murmushi kadan tayi ita kanta tamanta the last time datai murmushi.

To jama'a anan nakawo karshen free pages zan barku da tambayan nan ALIYU NE KO ZAYN NE???
Dan samin amsoshin nan kucigaba da bina awanan Littafin mai suna ALKAWARIN ZUCIYA!
Dan son cigaba da karanta Wanan littafin zaka iya turo 1k ta 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.

Dan girman Allah badan niba kubiya ku shiga group ku karanta. Support me🥰

You can chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

Thank you
M Shakur🥰

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now