16

549 32 1
                                    

1️⃣6️⃣

Free page
😉 enjoy

Kofan dakinta tabude ahankali ta shiga tanabin dakin da kallo yanda ko'ina tsaf tsaf an gyaramata sai kamshi dakin yake, shiga ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin awani irin gajiye cikeda sanyin jiki tasaki handbag dinta akasan dakin tafada kan gadon batare data cire takalmin kafanta ba tawani kalan kankame jikinta tanajin wani irin sanyi na shiga jikinta, she don't even know why amman hakanan fuskan police man dinan take gani a idanunta muryan shi namata yawo a kunne  da kanta gabaki daya yana kiran sunanta Ummulkhair breathe in, runtse idanunta tayi gam gam tana feeling yanda bones nata ke cringing to each other tana ganin fuskanshi namata yawo a idanu kafin idanunta suna hasko lips dinshi wani kalan ihu tayi. "Ahhhh stop!"  dasauri ta tashi zaune tana wurwurga kafafunta cikeda damuwa tace "Stopppp noooo what's wrong with me"? Wani irin zabura tayi ta tashi tsaye kawai tawuce dasauri tafada bathroom, wanka tayo sanan tafito daure da towel tana tunanin yaushe Mama zatasa amata Kitso dan gashin ya isheta daga tsifemata jiya, wani simple dogon Riga tasaka sanan tasaka hijabi tai salla tana idarwa tafito falo tawuce ganin duk basu tasan sun tafi masallaci sallan magrib, dinning tawuce zama tayi tana bubbude kula rice tazuba kadan sanan tasa nama tafaraci saida tacinye sanan takai plate din kitchen kafin tafito ahankali tai stairs, knocking dakin Mama tayi sanan tabude kofan ganin Mama akan gado ta lullube da bargo yasa tashigo da sauri tace "Mama menene" wani kalan kallo Mama tamata tace "bacci zanyi nagaji" hawa gadon tayi tana kallon fuskan Mama tace "Mama kibari ayi isha'i tukunna nima bacci nakeji" gyadamata kai Mama tayi tana kallon gashinta tace "weekend zakiyi kitso tunda ke kin dawo yarinya daga tsife miki kai kanki yadawo kaman na mahaukaciya" gyadama Mama kai tayi tana hamma, ganin haka yasa Mama tace "Oya tashi kije kiyi sallan to gashinan ana kira saiki kwanta tunda kin gaji, kinmasha ice cream din" girgizakai tayi agajiye tace "gobe zan sha Mama nagaji, gud night world best" night my baby girl, Mama tai maganan tana binta da kallo wucewa tayi tafice daga dakin tana salla ta kallabi tahau gado sai bacci.

Da asuba tana tashi salla tafarayi sanan takoma bacci dan yau batada lectures sai 10 and she wants to sleep sosai cus kanta yay clearing tadena all this banzayen tunanin nan datakeyi.
Karan wayanta yatadata by 9, da kyar ta iya bude idanunta ta kalli wayan rabon data danna wayanta hartama manta one thing dabai dameta aduniya kenan ba waya, she's not just a phone person, itadai barta da physical surutu, yawo rawa haaba anan ake samin Khairy, hannunta tamika da kyar tadauko wayan ganin Besty yasa taji duk wani kalan bacci datakeji yafice daga idanunta dasauri tai picking call din tace "Iyye su Besty Amarya ai nadauka kin manta dani yar rainin hankali saisa na shareki banma nemekiba" kuka Besty tasaki awaya dayasa dasauri ta tashi zaune adan tsorace tace "ke menene Besty, what happen? Kinasa inajin tsoro why are u crying?" Cikin wani kalan muryan ban tausayi Besty tace "Khairy wlh nafasa auren mutumin nan kasheni zaiyi tun ranan da aka kawoni abu daya ake har yau nagaji" dan ware idanu Khairy tayi tanajin maganan wani banbaram itadai barta da rashin ji but duk wani harka na maganan banza da Iskanci bata aciki, adan kunyace cikedajin nauyin magannan tace "to ba ance ana sabawa ba" tai dan shiru saikuma ta turo baki tace "idan yaki kihadashi da Maman ku" wani gajeren tsaki Besty taja cikeda masifa kaman tabugama Khairy dundu tace "I don't even know why I called u you are crazy Khairy, da zancen party ake da yanzu kingama tsara komi, lemme call Amal" tana maganan ta katse wayan, hararan wayan Khairy tayi ta ijiye saikuma chan kaman ta tuna wani abu wayan ta dauka dailing number Besty tayi back ringing daya tadaga, ahankali tace "sorry Besty kinji I seriously don't know what to tell u or how to advice u" cikin muryan damuwa Besty tace "wai Khairy when will you learn all this stuff eh, u are just hella wired Umma, u are just leaving life kaman bamace ba gashi duk munata aure Khairy keko saurayi bakida shi sai wanan Wizzy dake binki" hararanta Khairy tayi tace "nacemiki kidena hadani da wanan yaron" dan dariya Besty tayi kaman ba itane mai kuka yanzun nan ba tace "naji nadena, yanzu dai kinyi wani saurayin"? Dan shiru tayi kaman mai tunani harta bude baki zatai magana saikuma tai shiru hakan yasa Besty tace "ohhh wowww, Khairy this is something new, tell me who is he? Dan tunda nake dake duk aka miki tambayan saurayi direct kike cema mutum baki dashi wanan dakika kasa magana tell me wayeshi" dan murmushi tayi tayi dan juyi akan gado tana dan lumshe ido saikuma ahankali tace "wlh Besty banda kowa kawaidai wani Police man ne naketa haduwa dashi this days amman ko magana bamayi kawai dai he always saves me from trouble ne I don't know if that means anything amma dai ba soyayya muke ba ko magana ma bamayi" ahankali akuma natse Besty tace "ohh my Goddd! Khairy kinji yanda harwani natsuwa kikayi kina bani labarin police man dinnan kuwa, My world Khairy you love me! Wlh...." Dan yatsine fuska Khairy tayi dasauri tace "stop it! Mutumin dabanma sanshi ba, yaushe zaki dawo school nidai" dariya Besty tayi sosai tace "tunda u are avoiding maganan ai ba matsala, this weekend zai dawo dani but every weekend zai dinga zuwa" gyadamata kai Khairy tayi tace "sai kinzo bye" tai maganan tana katse wayan da sauri dan tasan Besty bazata taba hakura da topic dinan ba, ijiye wayan tayi ahankali sanan ta mirgina zuwa dayan gefen gadon tana tunani.

Ajiyan zuciya tasauke sanan ta tashi tasauka daga kan gadon zatai bathroom wayanta yashiga kuka cikeda masifa tadawo tace "mekuma kike sake kirana eh" wayan tadauka ganin Glory yasa tai picking wayan takai kunne kafinma tai magana Glory tace "hello fine girl, melanin goddest, pop skin with those sexy milky eyes" dan dariya tayi, Glory is her friend masters ita take a school nasu ta girmeta far far amman tana bala'in son kawance da Khairy, dan murmushi Khairy tayi tace "Hey! Where have u been i haven't seen u in school this days" dan dariya tayi tace "I travel naje PH chan gida, Khairy u don't know I am angry with u ba" dasauri Khairy tace "what happen? Why" kaman zatai kuka tace "today is my birthday Khairy" Adan kunyace Khairy tace "ohhh Glory, sorryy happy birthday darling" dasauri Glory tace "come to my party and wish me there, zamuyi a jabi lake mall a cikin jirgin ruwa, dress code is red 4pm sharp" wani kalan juya idanu Khairy tayi tace "ohh okay then bye see u later" ta katse wayan sanan tawuce bayi da gudu wanka tayi agurguje sanan tafito cikin wata doguwan rigan atampa ta shirya tafito tana tunanin yanda zatai planning zuwa party zata dawo gida by 2 wuraren 5 saita tafi tadawo 6.

Tea kawai tasha sanan tawuce school dan tayCi latti sosai.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now