24

506 23 6
                                    

2️⃣4️⃣

Free page
This book is 1k to join my group pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461

Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

Wuraren 11 tagama faten daya cika gidan da kamshi, fito da kulan falo tayi Mama tagani da Baba zaune afalo saisu Ya Manaf sunama Mama hira, tashi Maheer yayi yatayata suka fito da komi tsakar falo sanan suka zazzauna karban na Mama Baba yayi da kanshi yadinga bama Mama faten bashi kadai ba harsu Manaf sunyi mamakin yanda tasha faten dan tadena cin abinci, tass ta shanye sai dadi Khairy keji saida kowa yagama sanan ta kwashe komi itada Maheer sukakai kitchen tarema sukai wanke wanken tace "lallai yau mutanen mutuncin ka na nan kusa Maheer" hararanta yayi yawuce yafita daga kitchen din itama tabiyoshi tafito, Baba dake kallonsu yace "go and get ready Khairy malamin ki zaizo by 12" sama tawuce agurguje ta shirya tafito falo lokacin ba kowa Baba yakai Mama dakinshi, by 4 malamin yatafi su Manaf suka fita da ita basu dawo gidan ba sai around 10 tana zuwa lafiyan gado tabi.

Gabaki dayan gidan yau basuyi bacci ba sabida yanda jikin Mama yay tsanani, amai tadingayi na jini both tabaki da hanci, jikinta yay zafi sai maganganu take dabama sa ganewa, saida safen nan bacci ya dauketa.

6 ta tashi tana kallon agogo mamaki ma take ya akayi take lattin tashi late this days, wayanta dataga yay haske yamika hannu tadauka 2miss calls tagani na Aliyu saikuma message dayamata bude message din tayi. "I miss you" murmushi tayi ta ijiye wayan sanan ta tashi tawuce bayi wanka tayo tareda alwala Dan yau tanada morning lectures, tana fitowa tasa kaya tai salla sanan tabude kofa tafito su Ya Manaf tagani a falon sama kwakkwance kan kujera suna bacci, mamaki tayi amman ta tabe baki tai hanyar dakin Mama bude kofan tayi zaune taga Baba kan kujeran dakin yabude Al Qur'ani yana karantawa itakuma Mama na kwance kan gado tana bacci yarufa mata bargo, saida yakai ayar sanan ya kalleta tace "Good morning Baba" murmushi yamata yace "morning daughter, Mama is sleeping jiya dukanmu bamuyi bacci dawuri ba munata hira yayyinki na nan falo suna bacci suma" gyadamai kai tayi tace "eh nagansu" Gyadamata kai yayi yace "jeki breakfast yau Monday 8 kikeda lectures i want you to be serious kigama da good grade" gyadama Baba kai tayi sanan tajuya tafita tana kallon fuskan Mama dake bacci peacefully sanan tasauka falo ahankali, kitchen taje tea tadafa musu duka sanan ta soya chips zama tayi dinning zataci amman hakanan taji takasaci jikinta yamata wani irin sanyi kodan ita kadai ke yin breakfast dinne oho, tashi tayi tawuce sama tana kallon su Manaf da still ke bacci ta shiga dakinta dan shiryawa.

Shiryawa tayi tsaf cikin wani black abaya mai bala'in kyau tai rolling gyalen akanta ko kadan batai kwalliya ba but she looks kaman wata Somalian queen, jakanta tadauka sanan tafito, dakin Mama tabude takalli Baba dake karatu har lokacin tace "Baba natafi" saida ya idasa Ayan sanan yadago kudi yaciro yamika mata karba tayi tana murmushi tace "thank u Baba, kacema Mama natafi idan ta tashi bye" murmushi Baba yayi yace "to yarinyar Mama" maida kofan tayi tarufe yasauke ijiyan zuciya Noo yagaji Khairy deserve to know Maman ta is sick, he's tired of hiding it from her, bari Maryam ta tashi zai gayamata is time sufadi ma Khairy, Khairy is grown up she can handle it.

Fitowa tsakar gida tayi tana tafiya ahankali hakanan jikinta kawai yamata sanyi yasaki tarasa mesa kawai she's feeling sad and week ma yanzun nan, karasawa wajen motanta tayi Adamu na shiga itama tana shiga baya daidai sunajin horn mai gadinsu na budewa, motar Baffan ne ke shigowa gidan Hafiz ke tuki, sai motar Ammi biyeda su da driver ke parking sai kuma motan Mom, bude kofan motar tayi tafito tana murmushi da saurin ta tai wajen motan Baffa, daidai lokacin Baffa na bude baya yana fitowa yana mata murmushi yace "yan makarantan bokoko" dariya tadanyi tace "Baffa ina kwana, Ya Hafiz Baban Baby ina kwana, Laaaa Ya Hassan da Ya Hussain harda ku akazo yau" kafinma suyi magana Baba yace "wuce tafi school karki latti" yanuna mata motarta da Adamu yatada yana jiranta shiga motan tayi tana waving Mom dake saukowa daga motanta dan har yanzu motan Ammi bama abude ba kuma bamata iya ganin cikin banda driver shima ta glass din gaba taganshi dan motan tinted ne, jan motan Adamu yayi suka tafi nai gadi yamaida gate din gidan yarufe daidai lokacin Baba da Manaf suka fito.

Ahankali aka bude kofar motar Ammi, wani clean white kafane ya sauko dake sanye cikin wani hadadden sandals na Prada black, nails na kumban kafan are so fresh and white, gently yakarasa saukowa daga cikin motan yana yatsine fuska yana gyara bakin sun glasses na idanunshi na kampanin rayban, yana sanye cikin milk color yadi dayay dinkin jumper dashi daya bala'in amsan jikinshi, yanada tsayi dan wajen gabaki dayansu yafisu tsawo babu wanda baya ganin kanshi, yanada cika dakuma fadin kirji, kana ganinshi kaga Ammi kaman tai kaki ta tofar saisa yafi kannenshi kyau dansu Hafiz da Baffa suke kaman, yanada wani irin black very very dark saje dake kyalli kaman na bature, lips dinshi is so pinkish, gashin kanshi a kwance suna shinning, hannunshi ya daura agogo Rolex akai, ita kanta Ammi anytime ta kalleshi she feels proud da Allah yabata Zayn as her son, Zayn is definition na handsome guy, kyakkyawan namiji da babu macen data isa tamai yanga, ganin Baba yataho wajensu yasa ahankali yakai hannunshi yazare eye glasses na idanunshi yadan sunnar da kanshi kasa Baba nazuwa cikeda mamaki yakama hannun Baffa yace "d'ana Zayn nake gani haka" murmushi daga Baffa har Ammi da Mom sukayi, Baffa yace "da asuban nan yashigo gida" anatse Zayn yace "ina kwana Abba"? Hannu Baba yabashi ahankali yasa nashi hannun cikin na Baba, daidai sukaji muryan Maheer yana ihu. "Babaaa" Dawani irin sauri Baba yasaki hannun Zayn yay ciki Baffa da kowama suka bishi sama sukayi, dakin Mama Baba yashiga yatarar da Mu'az yarike Mama dake aman jini sosai tai lakur babu karfi kodaya ajikinta, wajenta Baba yayi yakamata daga hannun Mu'az yadau tissue yana share mata bakin ganin tadena aman, shigowa dakin Mom tayi takalli Baba tace "Alhaji bari mu chanza mata kaya" girgiza kai Mama tayi ahankali tana rike Baba gam batare datai magana ba, kallonta yayi sanan yakalli Mom yace "abarshi tukunna" karasowa gaban gadon Baffa yayi yaja kujera yazauna yana kallon Mama dabata iya bude idanunta da kyau yace "Maryam mutafi asibiti"? Girgizamai kai tayi ahankali, ajiyan zuciya yasauke yay shiru, shigowa ciki Ammi itama tayi tasami gefen gadon tazauna ahankali tana kallon Mama murya chan kasa tace "kina bukatan wani abu Maryam mezaki ci?" Girgizama Ammi kai tayi hakan yasa itama tai shiru, ahankali Baffa yajuya yakalli Zayn daya tsaya chak abakin kofa shima yana kallon Mama sanan Baffa yajuyo da kanshi ya kalli Mama yace "Maryam ga Zayn dakika ce nakira miki yazo" dan yunkurowa kadan tayi da duka karfinta, dasauri Baffa ganin haka yasa yace "Zayn come" karasowa gaban gadon Zayn yayi ahankali sanan gently ya tsugunnawa gaban gadon yana kallon Mama dake kallonshi kallon dakasan baa hayyacinta takeba yace "Mama I am here" hannunta daya tacire daga jikin Baba data rikeshi gam gam jin haka yasa Baba yatayata , kama hannun Zayn tayi hawaye yazubomata daga idanunta sanan kadan tabude bakinta dasauri Zayn da zuciyanshi ta katse yace "Mama I am here mekike so tell me" yakai kunenshi saitin bakinta, magana tashigamai a kunne wanda harta Baba dayake rikeda ita baiji abinda ta Fadima Zayn ba sanan takoma jikin Baba ta kankame shi, Maheer dataga yana kuka sosai mara sauti abakin kofan ta kalla hannu tamikamai ahankali yataso yazo kawai kankameta yayi yahau kuka sosai ahankali yace "Mama dan Allah kiwarke, Mama please karki mutu kibarmu" motsi sosai bakin Mama yafara hakan yasa Baba ya janye Maheer daga jikinta kankame Baba tasake yi takama hannunshi tarike gam gam kaman dats the only thing dake mata dadi sanan cikin wata kalan murya dabata fita da kyau dan hakoranta sun datse tace "Baffa, Ammi, Mom, dukanku yarana ina rokonku gafara ku yafeni idan nataba bata muku, idan Ummulkhair....." wani kalan nishi tayi tana kuka sosai dabayama fitowa sosai tace "kuce mata nace tayakuri tayafema Maman ta, i hide everything sabida nasan idanda tasan banda lpy bazata dauki abin da kyau ba, Baban Manaf" tai maganan tana kankame Baba tace "ka kulamin da Khairy dan Allah, Baffa nabaku amanan Khairy da duka yarana, Khairy is fragile, and innocent please ku rikemin yarinyata amana ita nafiji araina, zanbar duniyan nan amman Khairy ce araina sabida ita kadaice diyata mace yayyinta maza ne" ajiyan zuciya Mama tasake saukewa sanan ahankali tace "idan narasu Khairy taki kwantar da hankalinta kabata Littafin nan danabaka ka ijiye mata Baban Manaf"  gyadamata kai Baba yayi ahankali hawaye na taruwa a idanunshi Baffa ya bubbugamai kafa alamun karyay kuka, ahankali Mama tace "Baffa kamishi aure dazaran na rasu banson yarana su rasa uwa, Manaf kurike Matar da mahaifinku zai aura kaman ni kada kubata ciwon kai" gyadamata kai Manaf yayi, Ammi kallon Mu'az yayi dake bakin kofa tayi ya tsugunna idanunshi sunyi jajir tace "zo wajen mahaifiyar ka Mu'az" mikewa yayi tsaye da kyar shigowa yayi zuwa wajen gadon kawai yadaura kanshi kan gado yadaura hannunshi kan nata dan that's what Maheer da Manaf duk sukayi, yanda tazo tana nishi yasa Baffa ya gyadama Baba kai ahankali Baba yasoma karanto mata kalman shahada, saukar da kanshi kasa Zayn yayi, ahankali Mama ta amshi kalman shahadan karfe 12:03 daidai tacika da imani daidai lokacin Khairy ta tashi daga kan kujera sun gama lectures zasu fita jitayi kafafunta sunyi sanyi kawai tai baya zata fadi kaman tai paralyze Rabi dake bayanta ta tareta tace "ke Khairy are u okay" ? rike Rabi tayi tana taba kirjinta tace "gabana fadi yakeyi sosai kafana ba karfi" zaunar da ita Rabi tayi tace "kinyi breakfast kuwa"? Girgiza kai tayi hakan yasa Rabi da sauran kawayenta sukai dariya tace "yunwa ce muje kici abUinci".

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now