15

527 26 1
                                    

💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫

          ✍🏻 M SHAKUR

Dan magana da M shakur
wa.me/+2347012181461

1️⃣5️⃣

Yasa hannunshi daya awajen kanta ya daki tafin hannunshi bayan hannunshi yadaki stairs din sanan yakai dayan hannunshi yakama waist dinta yajuyo da ita hakan yasa ta mirgino side tafado jikinshi.

Daga yaran, security, iyayensu dasuka biyosu da sauri, Gwoggo dakekan wheelchair duk sandarewa sukai danba karamin faduwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba, yanda yakeji yanda take nishi a hannunshi yasa ahankali yazare hannunshi daga waist dinta gently yakai hannun kan fuskanta yadago fuskanta yana kallon face dinta yanda ta kankame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples dinta na lotsawa tana nishi sama sama dayake jinshi akan hannunshi, murya chan kasan makoshi while looking into her face yace "are you okay"? Muryan dataji yadaki dodon kunnenta yasa kadan kadan tashiga bude idanunta danta gasgata abinda taji kafin tabude su tass tadaura white fararen idanun nan nata manya manya dasukenan kaman an wanke da madara tadaura su akan fuskanshi, jitayi numfashinta ya makale somewhere in her throat ganin fuskanta dab da nashi yana kallonta as if he's trying to check something, yatsanshi yakai saitin nose nata jin bata numfashi  kawai takafeshi da manyan white eyes nata yasa dasauri yakalli security man din yanunamai jakanta dake kasa chan yace "give me her bag" dasauri yakawo jakanta yamikamai juye jakan yayi kasa inhaler ta yafado dasauri ya dauka yacire marfin yakai bakinta ahankali yace "breathe in Ummulkhair!" Wani irin bugawa zuciyanta yayi jin yanda yakira sunanta kaman sunanta dayakira ne yay reviving nata batasan lokacin datawani saki numfashinta data rikeshi amakogoronta ba yafito mai kara sanan taja inhaler, zagayesu mutane sukayi barinma parent din yaran da jikinsu yay sanyi ganin Yarinyar da yaranta suka ture is even asmatic, ganin yanda mutane suka cika kansu duk ana kallonta yasa ahankali takai hannunta batare data kalle fuskanshi ba tana kokarin karban inhaler daya rikemata abaki, ganin haka yasa gently yasakin mata ahankali yaran dasuke tsaye sukace "Anty sorry" dan murmushi tayi tana cire inhaler daga bakinta duk dasauri tana kokarin tashi tsaye, tsugunnawa Maman yaran tayi tace "rest a bit please" tai maganan tana maida mata kayan jakanta back aciki tareda daukan mata jakan ice cream dinta da sauri ta mike tsaye tana karban abubuwan ta daga hannun matan tace "I am okay thank u" Gwaggo dake kallonta tace "sannu kinji inane gidanku mukaiki nida jikana" dasauri tace "direbana na nan nagode Ma" sanan tawuce da sauri hartana tuntube tai wajen motansu da Adamu ya kwantar da kujera yanata hira awaya abinshi batare dayamasan meke faruwaba, saida yaga tabude motan ta shiga sanan yakoma wajen Gwaggo yatura keken sukai ciki tace "ohh yara da rashin wayau Hydar, inda badadan kaiba da sunja Yar yarinyar nan tafasa goshi wlh, itama yarinyar uwa batacin abinci yoo nakema wanan maganan haka rainon indomie ce daga ganinta, ace daga yan yara sun bangaje budurwan yarinya haka kawai sai faduwa uwa lagwani, ace yara suci tuwo suki duk irinku ne ai gashinan kaga yara  sun taso basu da karfi ko kadan, kai Allah dai ya wadaran naka subaci, Allah dai yasa kai aure ka haihu, wlh tun yaranka na wata biyu zan fara basu lafiyayyen tuwo da miyan kuka dataji daddawa" hararanta yayi baima cemata komiba ya sassayi ice cream din sanan suka fito tace "minene Wanan abin danaga kanata matsamata abaki" kin kulata yayi yasa ta amota ya maidata gida sanan yafito yatafi aiki.

Har suka shigo anguwan su badaidai takeba yau sau uku kenan tana ganin mutumin nan, saida suka shigo gida tukunna sanan taji wani kalan dadi, parking sukayi sanan tafito dasauri tana kwaso kayayyakin ta tana kwalama Mama kira. "Mamaaaa! Mama nadawo" daga Mama, Baba, Baffa da yayyinta da Hafiz duk suna zaune a falo dan basu dade da dawowa daga asibiti ba babu wanda yama iya wani kwakkwaran motsi, ita tsabagen murna batama lura da Karin mota kan tagidansu ba tai hanyar flat dinsu tana shouting Mama. "Mama nayomiki tsaraba yau nasayo miki ice cream kuma best flavor naki mint ban miki adding any thing ba ayanda kike sonshi plane" tai maganan tana bude kofan falo tana shiga tana kiran Mama. "Maaaam......" kasa karasa kiran Mama tayi ganin mutane a falon ga Mama zaune kusada Baba tana kallonta tana murmushi, hararanta Hafiz yayi yayi yace "inda ace ke kadai keda Mama aduniyan nan Khairy da munsha takaici" cikeda wasa Baffa yace "kagamin d'a kai kanama namiji ka more taka Maman balle ita mace kuma auta, ina tsaraban dakika kawoma Maman bazaki zo kibata ba kin wani tsaya awajen" akunyace takaraso cikin dakin wani irin rungume Mama tayi tana murmushi akunyace ganin duk ana kallonta yasa tadaurama Mama paper bag na ice cream din akan jikinta akunyace ta sauko dagakan jikinta tace "Baffa ina wuni" murmushi yayi yace "diyar Mamanta ya makaranta" ahankali tace "fine" sanan takalli Hafiz tace "Ya Hafiz ina yini ya baby kuma, dan Allah ya Hafiz kasa mata sunana" dasauri yazaro idanu yace "waaaa niii rufamin asiri Khairy sokike y'ata tazama fitinanna irinki" dariya aka hauyi adakin ahankali Khairy tace "Baffa kaga Ya Hafiz ko" kafin Baffa yay magana Baba yace "karya yayi to Khairiya" turo baki tayi kaman zatai kuka Baffa yace "sharesu Yar albarka, sun lashe basusan baiwan dake tattare da sunan ki bane saisa suke magana ahaka" wani kalan murmushi tayi tace "yauwa Baffa" sanan tajuyo takalli Mama tace "Mama kin sha maganin kan yadena miki ciwo muji" takai hannunta tana taba goshin Mama with so much care, gyadamata kai Mama tayi tace "yadena, cikani maza tashi kai ice cream din kisa a fridge kije kiyi wanka kiyi salla idan bakiyi a school ba saiki sauko kici abinshi" gyadama Mama kai tayi sanan ta tashi tana kallon yayyinta dataga sunyi wani iri harzata wuce tace "Ya Manaf kungaji ne haka naga kunyi wani iri, Ya Maheer idanunka sunyi ja kaman kayi kuka" hararanta yayi hakan yasa ta murgudamai baki tawuce abinta sama itama, dayake yana takanshi dayaji ciwon Mama yatashi yau baima biyemata ba.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now