23

493 20 0
                                    

2️⃣3️⃣

Free page
Gidan Ya Hafiz yacika makil da mutane sabida suna, duka yaran Baffa na wajen, Yaran Baffa takwas, Ammi ta haifi hudu duka maza, Zayn ne babba, sai Hafiz, sai yan biyun da Ammi ta haifa maza da Hassan da Hussain, dukansu manya duk sun gama makaranta suma aure yau ko gobe, dan Ammi da Baffa sunyi aure tun suna yara, haihuwan yan biyun yazo mata da complication da dole aka cire mahaifanta gabaki daya data haifi sama da haka, itakuma Mom yara hudu ta haifan ma Baffa, mata biyu Batool da Zara'u wacce itace auta dan maza biyu kebin Batool kafin Zara'u, Abdulhamid da Abdullahi sai Zara'u, Zara'u ce kadai ke primary school su Abdulhamid yanzu suke SS1 boarding school, Batool itace ke university, dayake ana hutu dukansu suna gidan ga mamakinta harda su Ya Manaf da Maheer, dukansu sun hadu dasu Ya Hassan suna gaggasa raguna, mantawa ma tayi tayi kuka suka shiga shagalin suna ga Matan Ya Hafiz badai kirki ba sunan Moon yabita hakan yasa kowa Anty Moon yake cemata.

Sai Bayan sallan isha'i sanan suka baro gidan itadasu Ya Manaf, tagaji iya gajiya bacci ma tasoma abayan motan tadaura kanta kan kafadan Ya Maheer, bai tadata ba ganin tagaji yacigaba da danna wayanshi abinshi.

Bude musu gate akayi ganin motocin su Baffa yasa daga Ya Manaf har Mu'az din kowa yasha jinin jikinshi, parking sukayi hakan yasa tabude idanunta jin tsayuwan mota ta tashi zaune tana kallon compound dinsu sanan tabude kofa suka fito zata wuce Ya Manaf yace "ke ina zaki"? Dasauri tajuyo takalleshi kafin ma tabashi amsa yace "kibi Maheer kuje flat dinmu su Baffa sunzo magana akeyi" batai musu ba danta gaji tabi Maheer sukai flat dinsu shikuma da Mu'az sukai flat dinsu Mama da saurin su, bude kofa sukayi suka shiga sunabin kowa na falon da kallo, Baffa ne da Baba zaune kan kujera daya, sai Ammi da Mom zaune tareda Ammi akasa da fuskanta ya kukkumbura kaman ba ita suka Bari this morning fuskanta looking normal ba, Mom na rikeda handky tana share idanunta dan takasa rike kuka itakuma Ammi idanunta sunyi ja dan ciwo is something dako enemy naka don't wish it on him, duk wanda yaga Mama saiya koka mata, kallonsu Mama tayi lurada kaman magana takeso tayi yasa Manaf yakaraso inda take hannunta yakama yarike yace "na tura Maheer da Khairy chan side dinmu Mama" ahankali yace "Mama meke miki ciwo"?  Kafin ma wani afalon ya iya magana aka bude kofa aka shigo Dr ne, rikeda wata karaman Leda a hannu yana zuwa allura yahada yazo wajen hannun Mama yakama yamata alluran a jijiya sanan yakalli Baba da Baffa dake kallonshi yace "can I talk to you sir in private"? Girgiza mai kai Baba yayi yace "likita duk duniya banda family daya wuce Wanan circle din dakake gani anan u can say anything, I think we are ready to hear kome zakace right wife" gyadamai kai Mama tayi kaman ba ita ke wahala ba, huci Dr yayi yakalli Mama yace "alluran nan zai saukar da kumburin fuskan nan da wuyanta, but at this point all I can say is make ur wife as comfortable as possible dan koda ankawota asibiti babu abinda zamu iyayi kuma, daga yanzu kome zaku gani kawai hakuri zakuyi har Allah yayi ikon shi dan komi na hannunshi, just make her comfortable and happy, please kudena kuka agabanta kowani abu dan Allah, that's all bari nakoma hospital" tashi yayi yafita babu wanda ya iya cemai kala, Manaf yayi yayi yarike kukan nashi but yakalli Mama yaga yanda tadawo but dudda haka she's still faking smile musu kawai yaji zuciyanshi yay breaking, fuskanshi yakifa akan kujera kusada Mama sai kuka yake da Mu'az dahar lokacin shi yama kasa shigowa cikin falon yana wajajen kofa, ahankali Mama tasa hannu takamoshi wani irin rungumeta yayi sanan tamikama Mu'az hannu alamun yazo zuwa yayi shima kuka wiwi ajikinta babu wanda ke iya magana cikinsu har Maman dan kumburin da fuskanta da wuyanta yayi yasa bata iya magana.

Ranan dukansu suna zaune a falon nan babu wanda ya iya motsi har asuba sanan tai bacci, daki suka Kaita suka keantar da ita sanan Baffa ya kwashi iyalinshi suka tafi gida, suna shiga alwala yadauro kawai yawuce masallaci.

Wuraren karfe 8 nasafe yafito daga masallacin, gida yawuce dayake yana dakin Ammi ne nan yayi bata falo yasan ta kwana hakan yasa yay sama zuwa dakinshi, zama yayi kan wata kujera ta musamman dayake da ita adakin nashi datake nan kaman gado shiru yayi yana tunani, ahankali yamika hannunshi yadauki wayanshi yay dailing number dayay saving da Zayn dayake nan international number, wayan na gab da katsewa yadauka anatse yace "Abba" dan ajiyan zuciya ABBA yasauke anatse shima yace "Zayn nasan is late ko wajenku" gyadamai kai Zayn yayi yana ture shishan dake gabanshi yatashi daga wajen yay bedroom dinshi zama yayi kan study chair nashi jin muryan ABBA somehow couple with the fact Abba baima Saba kiranshi da night ba most time da safe ABBA ke kiranshi ko darana, ahankali yace "Abba what is it are u okay"? Ajiyan zuciya Abba yasauke yace "Zayn Maryam matan Baffan ku batada lafiya, she's seriously ill, inaso kome kakeyi yanzu kabarshi find any available flight dazaka samu dazai taho naija gobe be it PJ ko normal flight ne kadawo gida" tunda yafara school that's tun lokacin dayake degree Abba baitaba demanding yadawo gida ba sai this time hakan yasa ahankali yace "okay Abba, but meke damun Mama"? Zayn yay tambayan ahankali dan yanason Mama she's one humble woman da he admires alot dudda he's not that close to her shi aduniyan nan ma only Ammin shi ne he's close too. Ahankali Abba yace "she has blood cancer! Just few days takeda shi left inji Doctors, anyway just come home kayi few days Saika koma tunda baka fara finals dinka ba, good night son" "night Abba" yay maganan ahankali feeling down, yadade ahaka sanan yatashi.

Wuraren 8:00 na safe tabude idanunta ganinta adakin yayyinta saida abin yabata mamaki, murmushi tayi ta tashi zaune sanan ahankali ta sauko daga gadon lallai tagaji ko lace din jikinta bata chanza ba tai bacci, jakanta tadauka tawuce tafita daga dakin tana tafiya ahankali, flat dinsu tashiga babu kowa a falo sama tayi dakinta tashiga alwala tayi tai salla tukunna sanan tacire kayan wata doguwan rigan bacci ta tasaka sanan tafito direct hanyar dakin Mama tayi bude kofan tayi tace "Mama tun jiya nan ganki ba adakin su Ya Manaf na kwana" akan gado taga Mama ta jingina da hango ta sanya sweater tai fayau da ita da hulan sanyi akanta batasan mesa ba but gani tayi Mama tamata wani iri a idanu, karasowa tayi gaban gadon saikuma ta tsugunna takai hannunta tai tagumi tana kallon Mama, hararanta Mama tayi da kyar ta iya dagewa tabude bakinta tace "me haka"? Ahankali tana kallonta still tace "Mama wlh kin chanza, lips dinki are so dry, Mama wai bakida lafiyane kike boyemin kinyi wani iri eh sabida kinsan zan damu, bazan damu bafa Mama ai yanzu na girma saima na kula dake" dan shiru tayi tana kallon Maman dake kallonta tanaso tai magana amman azaban datakeji awuyanta yasa takasa, dasauri Khairy tace "zan damu kadan but zan kulada ke bakid lafiyane Mama" tai maganan idanunta na rau rau dan she's really believing Mama bata da lafiya,  ganin haka yasa Mama tamikamata hannu sanan tahadiye duk wani azaban datakeji tace "lafiyana kalau kawai gani nayi my little Khairy has grown so sooo big, yarinya na tai girma she can even take care of her Mama come here" dasauri ta tashi hannun Mama takama sai kawai tasaki hannun tafada jikin Mama ta kankameta sosai ahankali tace "Mama wlh ina bala'in sonki, without you bansan ya zan kasance ba, Mama ko idan na kalli wasu yaran ko sai inga they are not lucky sabida bakene Maman su ba, Mama u are the best Mama I the world, u are the coolest Mom, the softest, the sweetest, bakida fada, gashi kina sonmu, we are ur everything Mama, Mama kinsan menene" girgiza mata kai Mamantayi, Khairy tace "all mothers are mothers, but not all mothers are like Mamana, cus Mamana tafi takowa dadi, Mama kinga duk girman dazanyi I will always be ur baby, Yar autan ki, kinga na gama school nafara aiki zan dinga miki komi, Mama nasan kinje makka but zan kaiki makka da kudina da aka biyani albashi wajen aiki" dariya Mama tahauyi sosai dayasa Khairy wani kalan murna, sanan tace "Mama yauma ni zan miki breakfast mezaki ci na dafa miki" ahankali tace "fate nakeso" wani tashi tayi tasauka daga gadon sanan tai juyi tace "then fate it is bari naje" tajuya dasauri tai hanyar kofa hartasa hannu zata bude kofan ahankali Mama tace "Ummulkhair" faduwa taji gabanta yayi hakan yasa ahankali tajuyo takalli Mama tace "naam" dakai Mama tamata alamu tazo dasauri taje gaban gadon, hannu biyu Mama tasa tai cupping face nata tana kallonta kafin ahankali takai goshinta saitin bakinta sanan ahankali ta manna mata kiss a goshin, murya chan kasa tace "I love you Ummulkhairy, Allah yamiki Albarka, Allah ya haskaka rayuwanki, Allah ya tsaremin ke" ahankali tana kallon fuskan Mama tace "Ameen Mama" takasa tashi, ganin kaman she's trying to read something from Mamas face yasa Mama tace "Oya tashi kije kimin fate na yunwa nikeji Madam kokin fasane tunda kin tasani gaba kaman kin sami talavijin" da sauri ta tashi tana dariya tafice daga dakin.

Bana tagani agaban dakin murmushi tayi tace "good morning Bana natafi yima MaUma fate".

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now