6

619 27 2
                                    

💫  PROMISE OF THE HEART 💫

     ALKAWARIN ZUCIYA 💔

        ✍🏻M SHAKUR

6️⃣

Wajajen 3 aka wuce da Amarya Kano, ita kanta Khairy saida tadanyi kuka cus Besty tabata tausayi, bayan an wuce da ita  tama Maman su sallama tawuce dan zuwa chan gidan dasukai party inda motanta yake a pake, ahankali take tafiya ta bala'in gaji sabida rawan dasuka sha, ita kadai kemagana tace "yanzu inda Baba yabarni da hardani za'akai Zainab Kano, gashi akwai more event a Kano" dan murmushi tayi ita kadai tace "Allah kaimu bikina wlh 2 weeks zaayi ana event hmm" dan murmushi tasakeyi tace "nidako saurayi banda shine nake planning biki na" ahankali ita kadai tace "saikace wata mara farin jini, inada samari dayawa but duk mazan Nile ne, basu hadu ba gasu yan rainin wayau saisa i don't even talk to them" tai maganan tana murguda baki daidai lokacin ta iso wajen motan, ahankali tace "I want to marry hadadden namiji, classic , handsome, miji dat will make mata jealous of my catch" tsayawa chak tayi takalli motan gabanta yadan fadi, saikuma chan tace "don't be scared Khairy you have to show Baba u can drive sabida yabarki kidinga jan motarki" tana maganan tabude gaban motan tashiga tazauna tana sauke ajiyan zuciya sanan tamaida kofar motan tarufe kafin ahankali tace "Ohhkay let's see" sitbelt tasaka still gabanta nafaduwa bata taba tuki bafa kawai tasha ganin yanda akeyi sanan Maheer idan tashiga mota dashi yana nuna mata yace "kihaka kihaka this and that" ahankali tace "Bismillahir Rahmanir Raheem" sanan ahankali takunna motar gently gabanta na dum dum tashiga yin reverse kadan kadan kana gani kasan wacce bata iya tuki bane acikin motan nan sanan ahankali taja motan tana tafiya ahankali wani irin murmushi tayi cikeda jin dadi tace "see ba gashi nan na iya ba ina tuki perfectly like a pro" Ahankali takejan motan feeling a bit too sad sabida su Mama basu Bari takai Zainab ba ahaka hartakai gate din estate din tasa kan motarta tafice tana kalle kallen main road din gabanta na faduwa, ganin motoci kowa na zuba gudu na wucewa yasa sabida irin karfin hali irin nata tasa motan ta shige cikin titin sanan tafara gudu Adan hankali, ganin tana gudu kan titi smooth babu wani tangarda yasa tai murmushi tace "wlh na iya" sanan tawani kara uban gudu tana murmushi, ko kadan bata lura dawani keke napep dake bullowa daga wani layi da mahaukacin gudu ba kawai danno kan keken shi yayi batare dayama kalli titin ba rawa jikinta ya dauka dudda da akwai tazara kadan tsakaninta dashi amman sabida yanda jikinta ke rawa tanason takara kara rage gudun datake kawai ta danna sauri before the blink of an eye jikake kwarap!! Motanta yadaki bayan keken da bala'in karfi tacigaba da tura keken gaba jikinta nawani irin rawa tama kasa taka burki. "Innalillahi wa innailaihi raji'un" tafadi arude kaman walkiya sanan ta ci wani mahaukacin burki dayasa dabata saka sit belt ba data buga kanta a siteri, ganin motan ya tsaya chak yasa dawani irin sauri ta murza key ta kashe motan gabaki daya tana wani irin sauke ijiyan zuciya da sauri dasauri tana kallon keken dake manne da gaban motanta zufa nawani irin keto mata daga goshi takasa ko motsi still in shock.

Dawani kalan sauri direban keke napep din yafito yaci Kwalli a idanunshi yana sanye da Yar singileta daya koma brown tsabagen datti da jeans passengers shi maza biyu suma dake baya duk suka fito yana kallon yanda bayan keken shi yay condemn, sauran motoci sukuma sunata wucewa abinsu tunda dai Allah yakawo sauki hatsari ne da babu wanda yaji ciwo to su karata chan anata wucewa ta gefensu.

Saida mai keken yagama duba kekenshi tass yakalli yanda duka kwan fitilan dake bayan keken suka faffashe sun fadi akasa sanan ahankali yadaga kanshi yakalli glass din gaban motan ranshi amugun bace yana kallon Umma dahar lokacin takasa motsi sai numfashi datake maidawa ita kadai tasan yanda cikin jikinta ke rawa, kafinma mai keken yay magana daya daga cikin passenger yace "durun uwanchan amman matar nan yar bala'in rainin wayau ce Auwal, muna tuki abinmu lami lafiya tazo ta dakan mana keke tamana Wanan uban asaran sanan ta zauna hankali kwance a motanta batama fitoba balle ta duba asaran datayi mana ba"........


Wani hadadden hilux baka dakana ganinta zaka gane da security personnel ne ke gudu akan titin, ganin titin is congested go slow yasa yashiga  rage gudu yana kalle kalle, wani kyakkyawan saurayi ne ke tukin motar yana sanye da kayan yan sanda, daya bala'in haska farin fatan jikinshi, ahankali yake tuki yanabin titin da kallon ganin yanda motoci suka cika hanya tam ga daga chan gefe gefen titi haka  ya hango accident akayi tsakanin keke da wata mota dayaba iya ganin cikin motan cus tinted glass ne, ga masu keken sun fito suna duba keken su uku kana ganin yaran kasan irin rascals dinan ne, dan tsaki yayi ahankali sanan ya gangara gefe yay parking motan shi, murya chan kasa tace "I hate this job Dad!" sanan ya kashe motan yafito yanadan yatsine fuska tareda maida kofan motan nashi yarufe.......

Cikin wani kalan bakan zuciya mai keken da aka kira da Auwal da idanunshi sukai jajir danshi kadai yasan wuyan dayasha kafin yasami keken nan mezaicema mutanen dasuka bashi haya, cikin fushi ya nuna Umma dake kallonsu kuri ta glass din gaban motan da yatsa, irin warning dinan yama kasa magana tsabagen zuciya, hakan yasa ahankali Umma takai hannunta ta zare sitbelt sanan tabude kofan motan tafito ahankali jikinta na rawa tana kallon gaban motanta itama dayama bare yay kacha kacha saikuma bayan keken dashi ma ya baci wutan duk ya mutu sun faffashe sun fadi, sanan takaraso ta inda suke tsaye nesa dasu zata bude baki tai magana Auwal mai keken ya tare mata numfashi yace "ke dan ubanki dame kike takama agarin nan dazaki min condem din adaidaita sanan ki zauna cikin motarki batare dakinma fito kin duba barnan dakikayi ba balle kibani hakuri.." sosai kirjinta kewani kalan dukan uku uku hakuri tai niyyan tabashi amman yanda yazagi Babanta yasa taji ranta yabaci, cikin fushi tana kallonshi itama right in the eye tace "karka karayin kuskuren zagin ubana again inba hakaba wlh saina wanka maka mari, besides ma kai agidanku ba'a koyamaka kaduba hanya kafin kashigo ciki ba eh"? Cikeda wata kalan bakar zuciya Auwal yana kallonta da idanunshi da ita kanta taga bala'in dake cikinsu yace "ni kike gayama magana?" Dakewa tayi dudda kirjinta kaman zai tsage tace "ai kai kafara, dama ance idan Yaro bai koyi tarbiya agida ba zai koya a titi, dan haka from today karka kara ganin mutum kai kuskuren zaginshi ko iyayenshi" kafin ma Auwal dake dunkule hannu yay magana passenger sukace "ke wai kinada hankali kuwa kin bugemai keke kinmai asara bazaki bada hakuri ba" wani mugun kallo tamusu tace "kune marasa hankali bani ba, kuma hakurin bazan bayarba kuyi yanda zakuyi" tai maganan zata juya jitayi an wani irin fizgo bayan riganta fut tadawo baya hartana turgeda kafa sabida heel din data saka, wani irin bari jikinta yadauka tana kallon Auwal daya fizgota ganin yadaga hannu zai kaimata mari yasa tawani irin kwala ihu tareda kai hannayenta biyun tana kare fuskanta, shiru taji batare dataji saukan Marin ba akan fuskanta, hakan yasa ahankali kaman wacce tai sata ta shiga janye hannunta daga kan fuskanta tana nishi sama sama sanan tabude idanunta da kyau tana kallon gabanta inda su Auwal mai keken suke, wani mutum tagani dogo fari kal sanye da kayan yan sanda yasha gabanta yana rikeda hannun Auwal daya kawomata mari ya murde, dudda bataga fuskan mutumin ba dan yabata baya but she could see yanda bayan shi keda fadi, gawani kalan bakin suma dake kanshi sun kwanta suna kyalli sosai zuwa shi wajen yasa wajen yadauki kamshin dayakeyi. Daga Auwal har passengers din duka tsurewa sukayi suna mutumin, cikin wata kalan kakkausan murya yace "how dare you raised your hand zaka daki mace akan titi, are u mad!" Yadakamai tsawa yana murde hannunshi da kyau ihu Auwal yayi jin azaba yace "officer dan Allah kayakuri bazan karaba, wlh bugemin mota tayi opisa" cikin muryan nan nashi nabawasa yace "and u dare to lift your hand up zaka daketa, cause she is a woman, and she is helpless, alone! Inda kanwar kace fa? U deserve to sleep in jail dukan ku the three of you" sosai suka shiga bashi hakuri, tun tana kallonsu tanajin mesuke fadi har taji kanta nawani irin juyawa kaman tanajin jiri, bugawan da kirjinta keyi yay multiplying da kusan dari hakan yasa gently tajuya tana daura hannayenta akan kirjinta tana kokarin ta saita numfashinta dake mata wuyan kamawa tana kokarin tafiya kawai tafiyan taji ya gagareta wani irin zubewa tayi jikin motan, Karan faduwanta da bugewa da motan datayi yasa dawani irin sauri dagashi harsu suka kallo inda take, ganin yanda take nishi tana beating chest nata tana kokarin numfashi at the same time tana kokarin tashi tsaye yasa dawani irin sauri yasaki Auwal yay inda take.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now