1

842 28 1
                                    

A sunkuye kaina yake a tsakar gida, ina d'auraye kwanuka. Da sauri nake tayi don na san muddin Ummata ta dawo ban gama wanke-wanken nan ba tabbas kashi na ya bushe. Ai kuwa sallamarta na ji hakan ya sa ni saurin janyo ragowar kwanukan.

Umma dake tsaye a bakin k'ofa ta rafka salati "Sauda me zan gani haka? Yanzu da tun safe da na fita ba ki k'arasa wanke-wanken nan ba har yamma sakaliya? Anya Sauda ba zaki nutsu ki yi hankali ba, duk da gama secondary School da kika yi?"

Muryata cikin shagwab'a na ce "Umma wallahi wuni nayi kaina na ciwo."

Ta zabgo min harara ta ce "Haka kika iya, ba ki da zance sai na cuta, shegen son jiki kamar mage, wallahi ki kiyayeni." Ta bankad'a labule ta shiga cikin d'akinta.

Ni ko na saki ajiyar zuciya. A zuciya ta na ce "Umma kenan."

A daidai lokacin wani yaro ya kwad'a sallama, na amsa masa ina nazarin inda na san fuskar yaron. Sai can na tuno d'an maigadin gidan Baba Hamza ne haka yasa na had'a rai na kuma bi shi da harara, don ko magen gidan na ga ni wallahi zan harareta. Na tsani ahalin gidan gaba d'aya. Wannan tabbas haka ya ke.

"Ina wuni?" Naji ya ce dani.

Ko kallon sa ban yi ba balle na amsa masa. Umma ce ta fito daga d'aki tana tamabayar "Waye mai sallamar ne?"
Da sauri yaron ya amsa, ko don ya fuskanci ni d'in ba zan amsa ba ne oho! Ya gaishe da Umma sannan ya mik'o mata chewing gum guda uku. Ta ce " Na menene?" Ya gyara zamansa, sannan ya ce "Wai na sunan munirat ne gobe. kuma wai ta ce don Allah ki zo da wuri akwai aiki a can gidan."

Umma ta amsa ba tare da wata damuwa ba. Ni kuwa zunduma ashar na yi na ce, "Gidan uban wa za ta zo? Saboda sun mayar da ke jakarsu, babu mai nemanki sai irin haka ta taso, saboda sun san za ki je ki wahalar da jikinki a wajen yi musu bauta da aikin banza aikin wofi.......

Wani kallo Umma ta wurga min ta kuma cillo min wani mafici cikin b'acin rai ta girgiza kai, ta kalli yaron da ya yi sugud'i yana yi min kallon mamaki da alama tijarata kawai ya ke ta'ajjabi. Ta ce "Kai yaro, ya sunanka?" Ya ce "Najibu"
"Yauwa Najibullahi, maza kaje ka ce Allah ya raya, sai mun zo insha Allah." Ya mik'e ta mik'a masa Naira Ashirin, "Ungo wannan ka sha alawa kayi maza ka wuce gida."

Ai yana karb'a na fisge cikin tsawa na ce "Wannan matsiyacin cingam d'in da suka kawo shine zaki ba shi har Naira Ashirin?"
Wannan karan cikin jin haushi Umma ta zabga min dundu a gadon baya na, tana salati ta ce "Sauda ina raba ki da wannan bak'in halin ba kya ji ko? Kin ba shi ko sai na mare ki shashashar yarinya har abada ana gaya miki amma kan ki ba ya d'auka? Wanda ka bayar har abada shine naka, zaki ba shi ko sai na mangareki?"

Fuskata a d'aure cike da k'unk'uni na mik'a masa Ashirin d'in idanuna har suna tara ruwan k'walla.

Shi kuwa ya karb'a ina kallon fuskarsa yana min dariyar mugunta. Hararar da na zabga masa ce tasa ya k'unshe dariyar da alama mamakin masifata ya ke.

Yana fita kuwa Umma ta hau kaina da masifa da bala'i tana cewa "y'ar banzar yarinya mai bak'in hali. So kike tilas sai kin yanke zumuncinmu da mutanen nan tamkar yarda suka yi, to bara na sanar da ke, ke ma kun zama d'aya da su. Ina ruwanki idan ma wahalar na musu, na yi d'in jikin ki ko nawa? Shashashar banza. Kuma ki sani, ki kwana da shirinki ke ma tilas sai kinje sunan tabbas! Sai dai ki kashe kanki don haushi.., shashashar yarinya mai d'abi'ar mutanen banza, duk mai yanke zumunci ai mutumin banza ne.."

Wai! Ai zuciyata tamkar ta fashe don tsananin zafi. Ba fad'an bane ya b'ata min rai sai cewa da ta yi ni ma sai na je gidan sunan. Ni ko da zuwa na wani sha'ani na danginmu wallahi gwara ta kwana tana yi min fad'a. Me za'a yi da danginmu Ko Dangin masifa da jaraba.

Har dare ina ta rok'on Umma a kan ta kyaleni da batun gidan sunan nan, amma Umma ta yi burus da ni. Kuma fuskarta babu alamun sassauci don ta d'inke tsaf ta had'e rai kamar hadarin kaji. Hakan yasa ko da na kwanta barci da batun na kwanta na fara tunanin su wanene Dangin mu?

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now