Zumuncin Zamani.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
__________
Dariya Fareeda take sosai, fuskarta cike da nisha'di ta mayar da kallonta kan Mahmoud tana dukansa da filo yana k'yak'yata dariyar. Sosai shauk'in soyayya ya 'dibesu Har Mahmoud 'din bai san sanda ya zuba mata ido ba, yana hango tsananin kyawun fuskar da Fareedan take da shi. Soyayyarta kullum k'ara shiga jikinsa ta ke, yana tsoron ranar rabuwarsu yana tsoron ranar da hankalin Hisham zai dawo kan matarsa, a ranar shi kansa ya san barci sai dai ya saceshi saboda tsananin kishin kasantywar Fareeda da mijinta.
A hankali ya sa hannu Ya shafi gefen kumatunta, Ya lumshe ido, ita 'din ma hannu tasa ta rik'e tsintsiyar hannunsa tana shafawa a hankali kafin ta shammaceshi ta sakar masa cizo a dantsen hannunsa.
Da sauri ya cukuikuyeta yana fa'din sai na rama ko ina kai masa wawura yake a jikinta yana bata hot romance kafin ya ja lab'banta Ya ciza. "Na rama." Ya furta a hankali cikin wani salo.
Fareeda ta b'ata fuska tana harararsa cikin wasa. Ya lakaci hancinta da yatsanta ya jashi sosai kafin ya furta "Fareeda your love gonna make me crazy. Har bana son na wuni ban jiki a jikina ba, ranar wuni nake kamar 'dan maraya, please ki kashe aurenki mu yi aure is better than wannan rayuwar da muke ciki." Ta lumshe ido tana shiga jikinsa cikin wani salo kalamansa suke amsa kuwwa a kunnenta, da gaske itama burin ta kenan itama burinta Mahmud 'din ya zama mallakinta uban yaranta. "Kada ka damu da wannan soon In sha Allah." Cikin annashuwa Ya sake damk'arta yana shafa gashin kanta "Yauwa dear, yana dawowa ki shuka masa rashin mutuncin da zai saka Ya sakeki ko bai shirya ba." Ta runtse hannunta a cikin nasa "Ni dai ina son ka yi min alk'awarin duk runtsi kana tare da ni ba mai raba mu." Ya kai mata sumbata Wanda yake tabbatar mata da d'aukan alk'awarin sa.
(Haka dai suke shek'e ayarsu tun bayan tafiyar Hisham Mahmud ya mayar da d'akinsa kamar na sa suke bajakolinsu a can sune kallon batsa wuni suke abu 'd'aya bayan ya kaita an 'dirka mata allurar hana 'daukan cikin gujewa afkuwar matsala. To za mu gani ko za'a yiwa Allah wayo. Allah ka shiryemu kasa mu gujewa afkawa komar shai'dan da muk'arrabansa."_____________
Bayan kwana hu'du da mutuwar Sa'ad gidan ya 'da'de ba kowa kamar an yi ruwan sama an 'dauke. Daga Umman Sauda sai y'arta da suke zuwa kullum su tafi. Su kuwa dangin Abba Mustafa biki ma aka fara a dangin duk suka 'da'de a ranar kwana uku suka tafi dinner. Duniya kenan zancen banza, in dai baka da shi zaka sha kallo.
Bak'in Hisham Wanda ya aiko ya samu zuwa a ranar akan Machine 'dinsa kamar yarda Hisham 'din ya ba shi umarni.
Ya dinga bin gidan da kallo yana mamakin yarda nan 'din ya zama muhallin surikin Hisham Maishadda, baya ga haka kuma gidan k'anin Babansa ne. Ya kawar da wancan tunanin daga ransa don ba huruminsa bane.
A wajen gidan ya ga an shimfi'da tabarma baya tantama mutuwa aka yi. Don haka ya k'arasa wajen da suke yana musu sallama. Jin wasu mutane suna fa'din ta hak'uri ya tabbatar da zarginsa na rasuwa aka yi. Don haka shima ya bi Ayari wajen gaishe da tsirarin mutane da fa'din ya hak'uri Allah Ya ji k'an rai."
Gaba 'daya suka amsa har Abba Mustafa da ya 'dan zuba masa ido yana nazarin inda ya san shi sai dai bai canka ba.
Cikin k'asa da kai ya ce "Don Allah nan ne gidan Malam Mustafa mai shadda?"
Abba ya jinjina kai "K'warai nan ne 'd'an samari, kana magana da Mustafa ne. Amma ni ban wayeka ba?"
"Baka ma san ni ba Baba, ni abokin 'danka ne Khalil Mai shadda shine ma Ya aiko ni."
Cikin karsashi Mustafa ya ce "Yaro Khalilu yaron wajena kake nufi?" Ya jinjina kai "Shi fa Baba, Khalil Mustafa."
Fara'ar fuskar Abba Mustafan ta k'ar yalwata Ya shiga fa'din "Alhamdulillah Ala kulli halin, wa astagfirullah min kulli zanbin yaro Khalilun a wane gari yake ko ya Samu labarin rasuwar 'dan uwan sa mafi soyuwa a gareshi ne?"

YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
Ficción GeneralLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...