Zumuncin Zamani
Night posting.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Daga k'ungiyar Elegant Online Writers. (Ha'din kai shine takenmu."
Mommy Laraba ta sanya mayafi ha'de da 'daukan jakarta suka rankaya suka fice suna sake jajanta al'amarin.
Mamaki ne ya kamasu ganin gidan da direban ya tsaya wannan ta kalli wannan kafin Inna Falmata cikin mamakin ta ce "Kai ka gane kwatancen inda aka ce ka kaimu kuwa ka kawo mu wannan k'erarren gidan?"
Kafin ta rufe baki sai ga raba gaddama ya fito Abba Mustafa ne cikin shirin tafiyarsa masallachi. Yana kawowa gaf da su ya shaida motar Falmatan da drivern nata kafin ya hango Inna Falmatan da suka kafa masa ido a cikin mota.
Fuskarsa da yalwar fara'a Ya k'araso daf da su yana fa'din "Maraba lale da Hajiya Falmata, yanzu ku ke tafe?" Falmata ta 'd'an saki fuska ha'de da 'daga kai "Wallahi kuwa, na je can gidan sai aka ce min kun taso kun dawo nan."
Yana girgiza kai alamar k'warai kuwa ya ce "To bismillah mu k'arasa daga ciki."
Da sanyayyan jikinsu suka fito zungwui-zungwui suka bi bayansa mamaki fal cikin ransu.
A zaune saman kujera 3 Seater suka samu Umman tsaf da ita cikin shigarta managarciya ta sabuwar atamfarta chiganvy da Abban ya 'dinka mata kala biyu a cikin ku'din. Tana ganinsu ta 'd'an saki fuska ka'dan tana mamakin me ya kawo su Falmatan da ko gaisuwa bata zo mata ba.... Ta 'd'an gyara zamanta tana fa'din "Barkanku da zuwa ku zauna mana."
Ba kallon gatsinen da suka Saba mata sai kallon mamaki suka zauna kan manyan kujerun k'afafunsu luntsum cikin carpet mai gashi. Madadin gaisuwa kallon gidan suka shiga yi suna ganin yarda ko ina ya ji tiles da alama an narka ku'di sosai a gidan. Gida sai shek'i yake kamar mudubi.
"Ina yininku?" Ta ce musu tana son matse dariyar da ta zo
Mata.
Da borin kunya suka amsa gaisuwarta ta, Inna Falmata ta k'ara "Da ya k'arin hak'uri? Ai sanda aka yi rasuwar bana jin da'di ne shi yasa ban lek'o ba." Umma ta gya'da kai a zuciyarta tana fa'din "Ai sai dai lek'en, ba zuwan wuni karb'ar gaisuwa ba." A fili kuwa sai ta murmusa ta ce "Bakomai Wallahi, ai komai sai Allah yayi." Ta mayar da kallonta ga Hajiya Laraba da bata da niyyar gaisheta ta ce "Laraba Ina yininmu?" Laraba ta juya tana mamakin sunan da ta kirata da shi Eeh Lallai Maryam karonta Ya kai tsaiko yau Laraba take kira ba gatsal sab'anin da da take Hajiya sama Hajiya k'asa. Ta saki ajiyar zuciya kafin ta ga tsine fuska ta ce "Lafiya Lau"Umma bata bi ta kallon da take mata ba ta mik'e ta shige kitchen in da suka sake binta da kallo har ta dawo suna kalle-kalle. Tray ne babba a hannunta ta shak'o shi da lemo ha'de da cincin da peppe chicken." Suka bi tray 'din da kallo wannan karan Laraba kasa shiru ta yi ta ce "Ba shakka"
Umma ta 'd'ago tana murmushi ta ce "Me fa?" Ta girgiza kai "A'a wai da mamaki nake wannan fa shine dare 'd'aya Allah kan yi bature..."
Falmata ta mele baki "Ai kuwa kam, Shi Khalilun wane aiki yake har ya tara uwar dukiyar da ya mallaka muku wannan gidan cikin k'an k'anin lokaci kamar Wanda ya shiga k'ungiyar asiri ko fashi da makami. Ku dai bincikeshi kafin ku ji da'din dukiya kuna zaune a zo a kameku a banza.." "Ba zata kai ga haka ba In sha Allahu don mun san tarbiyyar da muka basu ba alfahari ba..." Umman ta fa'da cikin murmushi da son tura musu takaici duk da a k'asan ranta ta ji haushin maganganunsu. Suka kalli juna suka tab'e baki, kafin Falmata ta mik'e ta ce "Mu bara mu k'arasa dama gaisuwar nan nazo saukewa." Umma ta kalli kwanonin da ko ruwa basu tab'a ba ta ce "Ko ruwan ai kwa sha." "Bar abinki ki bawa mabuk'ata, kin san mu ba bak'in abin bane." Laraba ta ce cike da izza da hassada.
Umma ta 'daga kai ha'de da cewa "Haka ne mantuwa na yi da karambani na na k'arawa mai k'arfi k'arfi a yi hak'uri a gaida mutanen gida." Ta fa'da tana rakasu bakin k'ofa. Har sun kusa fita gate Falmata ta juyo "Ina hakimar y'ar taki sarkin Fankama, ba mu isa ta fito ta gaishe mu bane?" A diririce Umman ta ce "Saudatu tana nan lafiya bata nan ne da kin ga ta fito."
Ko a mota zancen da suke kenan fa'da suke suna sake jaddadawa tabbas ku'din nan ba na halak bane.. Laraba ta ce "Ina jiye musu ranar nadama da dana sani.." Inna Falmata ta ce "A na me zaki jiye musu? Ina ruwanki sanda zata kacame musu kina gadonki a kwance sai dai ki ji labari ba dai an ci ana wage baki ba." Daga can direct gidan Malamin suka wuce.
________
A nutse cikin shagon suke tafiya cikin shigar alfarma. Kayan babies suke jida kamar me? Har sai da Sauda ta rik'e hannunsa tana fa'din "Haba Yaya Hisham ka bar shi haka sun isa." Ya janye hannunsa "Baki san yarda nake son yara ba kenan, don haka ki shirya haihuwa ko wacce shekara."
Bakinta ta turo alamar shagwab'a. Murmushi ya saki yana kaiwa bakin sumbata hakan ya sata ta yi shiru don dole, ta kuma janye jikinta tana tura trolley da kayan da suka siya yake ciki. Duk da k'asar masu jajayen kunnuwa ce da ba su mayar da hakan komai ba ita tana jin kunya.
Cikin kulawa Ya bita da nasa trolley 'din yana fa'din "Wai ban gane ba, ba za ki yi tsaraba bane?" Cikin farin ciki ta Ware ido tana mamakin surprise 'din da yake shirin mata "Wow! Yaya Hisham Nigeria za mu koma? Amma fa ina jin tsoro." Ya 'daga gira yana kallonta "Me yasa zaki ji tsoro?" "Ina tsoron a raba mu" ta fa'da cikin marairaicewa. Cikin jin da'di a zuciyarsa Ya ce "An zo wajen na San yanzu ko me za'a yi ba zata iya rabuwa da ni ba, na riga na narka mata zuciyarta da soyayyata. Zata iya fuskantar kowane k'alubale game da shi. Ya nuna mata shi 'din namiji ne na gaske musamman ta fannin mu'amalar aure Har wani suna take kiransa da shi "SADAUKI NA." Sunan da yake alfahari da shi yake kuma saka shi jin isa da girma, idan ta kira shi da hakan a wancan yanayin na ma'aurata.
"Ya kamata na waiwayi gida haka Saudatu, ko bakomai akwai hak'kin y'ar uwarki a kaina tsawon wata biyar muna tare da ke duk da ina yi mata waya ina kuma bata duk ku'da'den da take so Amma hakan kuskure ne a musulunci, ke ma kuma kamata ya yi ki k'arfafa min gwiwa Babu abinda zai faru Insha Allah sai alheri. Ko kina son ki gan ni da shanyayyen b'arin jiki ranar alk'iyama." Ta gamsu da jawabin sa kuma dama ba gidan ne bata son zuwa ba, bata son Iyayensa su yi yunk'urin sake raba su ne. Ya fahimci damuwarta don haka ta dafa ta "Ke Tawa ce Saudatu, da ikon Allah Babu mai raba mu sai k'udirar Izza Wanda itama 'din ina fatan ta ha'da ta 'dauke mu rana 'd'aya, ciki da bai 'din Saudatuna Mallakin Hisham ne ko? Ni ka'dai na San sirrin zumarki." Ya fa'da yana 'daga mata gira ta kuwa fa'da jikinsa tana 'd'an dukansa a hankali cikin Soyayya. Shi kuwa ya dinga yi mata kirarin da yake mata sau tari a kunnuwanta. Ta dinga jinjina kai tana jinta kamar sarauniyar mata. Daga haka suka cigaba da siyayyarsu ta tsaraba da za su yiwa y'an uwa da iyayensu.
_____________
Cikin sauri da azama ta ture Mahmud daga jikinta, a razane take kallonsa bayan gama wayarta da Hisham da ya sanar da ita yana tsaye a k'ofar falo ta bu'de masa ya dawo. Dukan tara-tara gabanta ya dinga yi ba ma uku-uku ba. Cikin rawar murya tana tura shi da sauri tana fa'din "Mahmud Hisham ya dawo tashi ka yi ta kanka."
Ya zaro ido yana kallonta kafin ta ture shi da k'arfi "Ka yi ta kanka nace maka, babu lokaci.
K'arfe ta duba agogon da yake bangon 'dakin tana k'ok'arin zura rigarta tana mamakin yarda suka da'de suna barci haka. Ta tattare gashinta ta k'ulle da band kafin ta sauko daga gadon ko tunanin gyara shi bata yi ba ta fice da sauri.
Sai da ta aro jarumtar dole ta yafa a fuskarta sannan ta bu'de masa k'ofar, bayan ta rufe Mahmud 'din a wani 'daki daban.
Gaba 'd'aya ta fa'da jikinsa ta k'ank'ameshi tana masa oyoyo cikin murna. "Oyoyo Sweety isowa ba notice.." "Just to surprise you." Ya fa'da yana hugging 'dinta sosai don shi kansa ya san ta yi missing 'dinsa. A haka tana jikinsa ya yi hanyar 'dakinsa da ita so yake tun yanzu ya rage mata k'ishirwar tasa da tayi.
Tsakiyar 'dakin ya tsaya cak Ya dinga bin 'dakin da wani irin kallo, da yasa hanjin cikin Fareeda ta mur'da sosai ta bi inda yake kallo da idanuwa itama, ta dafe zuciyarta da take shirin tarwatsewa bayan idanunta Sun gano mata gajeran Wandon Mahmud, Singiletinsa da agogonsa gefe guda kuma ga under wears 'dinta.........
Cab'di jam.... Ya take ne? Hakan take😂😂

YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
Fiksi UmumLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...