Zumuncin Zamani
Da sauri Hisham Ya amshi Babyn a hannunta, sai sannan ta kece da wani irin kuka tana duban Hisham ta ce "Da gaske Sa'adu na ya rasu? Amma baka gaya min ba Yaya Hisham, wayyo Allah na..... " ta dinga Jin muryarta na sark'ewa saboda tsananin kuka numfashinta yana sama tana fitar da shi a galabaice.." Hisham ya mik'awa Baba yaron da ta fara salati tana fa'din "Maza Hisham ka kira likita kada ta sume mana, abinda iyayen suke tsoro kenan suka k'i sanar da ita da wuri."
Hisham sai da ya guntse ruwa a bakinsa ya fesa mata a fuska kafin ta dawo cikin hayyacinta idanunta na tsiyayar da hawaye ta zubawa Hisham ido kafin ta ce "Tun yaushe ya mutu?" Hisham ya gaya mata sanda ya rasun ya 'dora da cewa "Don haka baya buk'atar kukan ki, addu'a ya kamata ki masa ki kuma godewa Allah da ya dawo Miki da Sa'ad k'arami ga shi nan gaba 'daya Sa'ad ya 'dauko kamanni suke sosai kwabo da kwabo. Kada ki masa kuka don ba gata bane yiwa mama ci kuka."
Ta yi shirun sai dai hawayenta da ya cigaba da bulbula Wanda bata da ikon tsayar da su. Baba ma nasiha ta dinga mata sosai suna sake bata baki suna k'ara tabbatar mata da Sa'adu ya dace tunda ciwon ciki ne ya kashe shi.
Kukan bai tsagaita ba ta dubi Hisham cikin sanyaye muryar ta ta ce "Yaya Hisham don Allah ka amince na je gida wajen Umma na zan fi Jin da'di a can, anan ra'dadin mutuwar nan ba zai bari na nutsu ba."
Ya jinjina Kai shima ya amince da hakan amma sai ya ce mata sai kin yi min alk'awarin kin daina kukan da kike."
Tana sakin ajiyar zuciya ta ce "Ba zan daina kukan mutuwar Yaya Sa'ad ba har abada ni na sani shak'uwar da muka yi da 'Sa'ad duk cikin y'an uwa na ba Wanda muka yi shak'uwar da muka yi da shi." Hisham ya 'daga kai "Shikkenan ki dinga masa addu'a ita Ya fi buk'ata, bari na je na samar mana ticket 'din dama nima ina son zuwa Daddy ya takura min da zancen zab'ensa." Ya fa'di yana tuna ya ma manta bai yi posting 'din da ya ce zai yi ba a Maishadda group, wani tunani ya yi bari kawai ya k'yalesu sa ji labari daga sama ya ga da wani ido mak'iya auren za su kallesu. Daga haka ya musu sallama Ya tafi samo musu ticket ya bar Sauda lamo a kan gado cikin tsananin tunani da kewar Yaya Sa'adunta. Ashe ba za su sake ganawa ta lumshe ido tana tunano duk wani memory 'din su na dariya ta 'd'an murmusa tana hawaye tabbas mutuwar ta girgiza Sauda, sai ta ji 'dokin haihuwar da take ma ya ragu mata.
_________________
Da fara'a Umma ta tarbesu bayan isarsu gidan sam bakinta ya k'i rufuwa Wai Saudatu ce yau da 'da guda ta dinga tunanin wauta da tsiwar Saudan ko ya zata yi da rainon 'dan mutum sukutum da guda... Sauda dai fa'dawa ta yi jikinta tana son yin kuka Amma bata son tasowa da Umma sabon mikin da ta tabbatar ya fara warkewa. Kowa ya 'd'au yaron banda Umma da ta kasa mik'a hannu ta amsheshi kunya take ji sosai. Sai da Hisham ya kai mata shi da kansa yana fa'din "Umma amshi jikanki na farko ki kuma gano tsantsar kamarsa da Sa'adu don haka ma na saka masa Sa'ad junior."
Jin abinda ya ce ya sa Umma da sauri ta amshi yaron tana kallonsa, tabbas kamanninsa da Sa'ad Sun bayyana kamar Sa'ad yana jinjiri a sanda ta haifeshi. Ta dinga 'dauke k'wallar da take idonta tana jinjina girman k'udirar Ubangiji a ranta.
Saudat ta sake jujjuyawa tana kallon gidan cikin son zolayar iyayenta ta ce "Amma gidan nan ya yi kyau Abba, ka San ban tab'a zuwan sa ba. Yaya Khalil ka yi k'ok'ari." Ta fa'da tana 'd'an son murmusawa da k'ok'arin kawar wa da Umma damuwar da ta tabbata tana cin ranta. Abba ya 'd'aga kai "Ai kuwa sosai Sauda, kin ga Khalil ya saka mun huta da yawan haya." Khalil da yake gefe da sauri ya ce "Abba ni fa yau zan gaya maka gaskiya, wallahi ban san da wannan gidan ba sannan ban san waye yake amfani da sunana ba yake muku wa'dannan tarin alhairan ba, albishir 'daya zan muku a gobe za mu tare a gidan da na Gina mana da gumi na a unguwar tudun Yola." Baki sake Abban yake kallonsa jin abinda ya ce "Ban gane ba Khalilu? Ban gane ba kai ka ke mana wannan hidimar ba to wanene?"
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
Fiksi UmumLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...