Zumuncin Zamani
7.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
Ku karanta kyauta
(Jazakillah mai Typing Fateemah Sabi'u Dankaka, mata a gidan Isa Allah ya saka da alheri ya raya mana Meenah, ya kawo k'annenta don girman zatinsa godiya dubu.)
Da d'an takunsa isarsa ya iso ya
mikamin card d'in ni kuma na mika masa kudin."Mayar mata da kudinta" ya fada yana kallon k'wayar idona har na fara tafiya naji yace, "Ina yarinyar da na bari anan?"
Na girgixa kai, "Wallahi bansan inda tayi ba." Ya shafa kumatunsa Yana murmushi. yace "Ok jeki."
Na sake tafiya sai kuma naji ya sake cewa "Sauda"
Na sake juyowa.
" Karfe nawa za ku tafi?"
Nace, wallahi ban sani ba"
Ya girgixa kai, sannna ya juya ya fice.
Koda na shiga falon na hango bakuwar Hisham kusa da Inna falmata gabana ya fadi,sai da na karasa na mika mata kati da kudin
Tsaki tayi Kafin ta ce "To mara kunya,haka kike mikawa ubanki Abu a tsaye k'ikam?"
Sosai na zuba mata ido don kam na ji zafin furucinta.
"Ko zaki dake ni ne fitsararriya.?"
Girgiza Kai nayi kawai.
"Uban waye yabaki wannan katin naga kin maido min da kud'in?"
Sai da na had'iye Wani yawu mai matuk'ar d'aci sannna nace "Ya Hisham" a zabure naga sun had'a Baki wajen cewa "Hisham fa kika ce? Meye had'inki da shi?"
Cikin matuk'ar had'e rai da gajiya da tambayoyin rainin hankalin na ce "Bakomai" Don na ga an fara yi min tambayar rainin hankali.
Tab'e baki tayi tace. "Ko da yake me ma Zai yi da ke ga d'iyar arziki wacce tayi gadon arziki gaba da baya iyaye da kakanni ubanta senator ne, kuma shi da kansa Hisham d'in ya ce yana sonta, don haka idan ma da wani abu a ranki ki batar da shi don Hisham mijin ' Y'ar manyan mutane ceeee---------"
Ban k'arasa jin sauran zancen ba na yi saurin b'acewa daga wurin,Ina ji 'Yan matan wurin suna yi min dariya. Zuciyata kam a kufule take sosai
Wannan wacce irin rayuwa ce?don ba ka da shi k'annenka ma su rainaka?
Sai dana share kwalla, sannan na koma gurin Ummata don ba na son na b'ata mata rai sam. Koda ta ganni kallo kawai ta bi ni da shi da alama ta fahimci damuwa karara a tare da ni, ba tace komai ba kasancewar tana tare da masu aikin abincin biki ta saje a cikin su, kai ka ce ba ta da alaka ko kad'an da masu Taron bikin.
K'arfe 4 :00 na yammah aka fita harabar gidan don gudanar da yinin bikin.Umma ce ta lallab'ani ta sakani na fita, koda naje wajen rakab'ewa na yi acan Wani gefe ina kallon masu rawa da yadda ake watsar da kud'i tamkar ba a so, kai ko nace tamkar mabukata sun k'are a duniya. Mhmn rayuwa kenan!
',ya'yan inna sahura na gani sun taho gurina da yake su ma ya'yan yaku bayi ne don Inna sahura ba ta da wadatar arziki, kuma mijinta ya mutu . Dama can kuma ba mai wadatar ba ne,ita take bin babanmu a d'akinsu daga ita sai Inna maryam, ita kam mijinta yana da rufin asiri, don haka ita ake damawa da ita a danginmu don ko ba komai an san idan anyi mata tana da abun mayarwa.,babu laifi tana d'an kula da mu ita, dai sam ba kamar yadda ya dace ka yi wa jininka ba.
Da fara' arsu suka tare ni su ma sun ci kwalliyar su kamar ni irin ta yaku bayi,Zainab ce tace "laah saudat ashe kin zo?"
Ni ma din cikin murmushi na ce "Yaushe kuka zo?"
Asma'u ce ta tab'e baki tace "Yanzun nan shigowar mu, kinsan ni ba kasafai na fiye son shiga Taron Dangin nan ba"Yanzu ma don umma ta kafe tace sai mun zo ne, Ina Ummanki?
Na d'an tab'e baki tare da cewa, Tana kicin gurin aikin abincin biki.
Zainab ta yatsine baki da cewa"Wallahi Umma tana son wahalar da Kanta gurin wad'annan matsiyatan mutanen da ba su san tana Yi ba yanzu fa da muka hadu da inna falmata baki ga wani kallon banxa da ta watso mana ba,da kyar ta amsa gaisuwar amma tana ganin wata k'aramar yarinya 'yar gidan B hamxa yarinyar ko gaisheta ba tayi ba,ta tare ta tana fad'in "Zahra,Zahra, yanzu Ku ka zo? Ina Ummanki?. Amman yarinyar nan ko kulata ba tayi ba duk da k'ok'arin cusa kanta da take."
Dariya muka tuntsure da ita sosai ganin yadda Zainab ta dage tana kwaiwakyon maganar Inna Falmata nace. "Har yau Zainab,ki na nan ashe da d'an banzan halinki?"
Asma u ta ce "In dai Zainab ce sai abinda ya k'aru."
Daidai lokacin na hango motar Y Hisham ta nufo inda muke da yake dama a parking space muke zaune d'an matsawa kad'an muka yi ya yi parking.
Cikin shan k'amshi ya fito daga motar. Idanunmu suka had'u sai na ga ya sakar min wani murmushi, su Zainab kuwa da sauri suka gaishe shi ya amsa musu cikin matuk'ar walwala a fuskarsa, sannan ya ce, "Ku me kuke yi a nan ba ku shiga cikin Y'an uwa ba?"
Asmau tace "Yanzu muka zo YHisham" Ya zuba narkakkun idanunsa kafin ya ce "Yanzu ku dai kuka zo ita kuwa ai tun d'azu tana nan" Murmushi kawai suka masa muna mik'ewa don barin wajen.Ranar litinin da safe nayi shirin makaranta,saboda a ranar ne nake shirin fara d'aukar lakca a makaranta B.U.K, inda zan karanci fannin likitanci b'angaren medicine. Tun daren lahadi Y.Hisham ya zo ya kawo min dogayen riguna kala- kala goma masu kyau da mayafansu, sai plat shoes guda shida da jakunkuna guda hud'u don haka nayi kwalliyata a cikin wata doguwar riga peach color mai adon baki da golden,na yane kaina da mayafi baki. Daman gashin kaina gammo nayi da shi ya xamana tamkar na saka a cuci.
Zuciyata fresh nake jinta da tsananin farin cikin fara xuwa makaranta,
Don kam karatuna masomi ne na cikar burina na son tallafawa iyayena. A tsaitsaye na sha kokon da k'osai na yi saurin mikewa ina cewa umma, "Bara nayi sauri na tafi kada na yi late."
Umma cikin murmushi tace "oh, sauda duk zumud'in ne haka? To Allah ya ba da saa.ga #150 ki shiga tasi yayanku ya ce ita ta fiyewa yan makaranta sauki."
Na saka hannu biyu na karb'a had'e da cewa. To Umma sai na dawo" ta girgiza kai kafin tace
" To don Allah sauda ki kiyaye mutuncin ki jami'a ba kamar secondary bace, banda b'ata garin k'awaye da za su saka ki a hanyar b'ata, su ma muna musu addu'a ubangiji ya shirye su na ce "Ameen Umma." na sa Kai na fita daga soron gidan namu
Adaidai lokacin na hango motar Y. Hisham ta yi parking a k'ofar gidan, tsawon mintuna na jira ya fito in gaishe shi amma bai fito ba, hakan yasa na saka Kai na fice ji na yi Yana danna min horn, na juya babu shiri.Ya sauke gilashin motar Yana k'are min kallo cikin k'ayataccen murmushi ya ce sauda kin yi kyau sosai shigo na sauke ki makarantar.
Da sauri na girgixa Kai na ce "lah Y.Hisham ka bar shi kada na wahalar da kai. Ina fita titi zan samu mota."kallona yayi ya hade rai yace "Sauda ba na son gardama, shigo kawai abin da na fito yi kenan." Don tilas na bud'e motar gidan gaba na zauna wani sanyin Dad'i ya buge ni ga daddad'an k'amshinsa da ya xauna a motar.
Tunda muka fara tafiya bai ce komaii ba illa muna sauraran wani tattausan music har muka je makaranta na saka hannu zan bud'e motar ya kira ni cikin tausasa murya "SAUDAT"
Cak na tsaya.
"Dago ki kalleni"
Na dago ina duban idonsa
" Please, ki taimake ni ki tsaya ki yi karatu, ban da kula samari barkatai please." Yadda yayi abin ya bani mamaki,tamkar mai magana da budurwar sa. "Baki ce komaii ba saudat?" D'aga masa Kai kawai nayi
"Promise?"Ya fada yana sake tsare ni da Ido.lumshe idona yi kawai saboda wani abu da naji ya tsarga min cikin raina.Shi d'in ma jingina kansa ya yi a kujera ya lumshe Ido kafin naji muryarsa idanunsa a rufe na ji ya ce "Zuciyata da ruhina sun kasance a wani Hali tun a lokacin da na fara sanya kwayar idona a kanki All what I mean saudat l lo------------
Da sauri na d'ago ina kallonsa hakan ya saka shi gimtse maganar babu shiri.cikin dasasshiyar murya nace "Y Hisham me kake so ka ce?"
Ya daga gira Yana kallo na kafin ya ce "SO" na ce Ina sonki saudat."
Da sauri na bud'e motar na fice saboda wani kuka da yake son ya sub'uce min. "Wane bala'i y Hisham yake son dauko wa gidanmu? Wanann wace irin magana ce? Na ja innalillah wa inna ilaihirraji'una" ya fi a k'irga da kyar na iya controlling din kaina natafi gurin lacture din.
Babu mutane sosai a hall din sai dai da yawansu masu nutsuwa ne, ko da aka tashi da sauri na fita na samu mota na wuce gida don ba naso Y. Hisham ya riskeni
A gida kuwa ganina wurjanjan Umma ta ce "Duk gajiyar ce haka Saudat?" Na d'aga kaina don haka tace "oh,sannu yau daya kin ga yardda kika koma? Maxa dauko abincinki a kicin ki ci"
Cewa nayi, "To Umma bari na yi sallah tukunna" fatana kada Allah yasa y Hisham ya sake tayar da maganar ubangiji kada ka kaddarar min auren sa, Allah ka fi ni sanin masifar dake cikin danginmu, Allah ka sa ya janye xancen nan." Addu'oin da bake ta yi a raina kenan.
Abincin ma tura shi kawai nake yi da xarar na tuna kalmar "ina son ki sauda" sai na ji gabana ya fad'i ,umma kuwa cewa take,"'Maza ki ci kije ki kwanta,duk da rashin barci ma kin riga kin saba da shegen barcin safen nan." Ita a zatonta duk gajiyar ce ta firgitar dani haka.
Ai kuwan ina gamawa na mike naje na kwanta lamo, ba barcin nake ba sai tsabar tunanin da ya cushemin kwakwalwa.
Sallamarsa na jiyo na tsakr gida gabana ya sake yankewa ya fadi.ina jin yana tambayar Umma "Saudat kuwa ta dawo?"
Umma tace"ta dawo,gata can a daki a kwance ko ma tayi barci. Yar nema duk a gajiye ta dawo likis."
Yace, "Hmmm Saudat kenan.
Wa ya gaya mata karatun sauki ne musamman karatu irin nasu na likitanci"
Daga haka yayi mata sallama ya fita. Na yi hamdala a xuciyata da bai nemeni ba.
"NI SAUDA NA GA TA KAINA. Ina ni ina Kai Y.Hisham?"
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...