Zumuncin Zamani.
Daga Taskar Nazeefah S Nashe
Ku karanta kyauta.
08033748387
📄6
Da safe ina d'aki a kwance nake sai dai ba barci nake yi ba. Waya muke da wani saurayina Bashir da nake matuk'ar so. Anan bayan layin mu yake trader ce dashi yana siyar da kayan masarufi. Mun dad'e mu na soyyah da Bashir ba tare da kowa ya sani ba hakan ya sa sam ba na kula kowa da sunan soyyah, duk da samarin da suke matuk'ar so na.
Bashir d'in ne ya Hana ni fad'awa kowa saboda ya CE so yake sai ya yi diploma ya samu aiki, sannan ya bayyanawa Kowa. Shi yasa ko zance ba ma yi da shi daga waya sai ko text message.
Umma ta d'aga labule ta shigo. Ba ki tashi ba ne?"
Da sauri na kashe wayar tawa kirar Nokia 3310 na ce " na tashi Umma."
"To maza ki shirya za muje bikin Nafeesa y'ar gidan Inna shukra.
Da sauri na ce" umma biki kuma? Dan Allah ki barni a gida ki je ke kadai."
Umma ficewa tayi kawai ba tare da ta sake yi min magana ba. Hakan ya sa na san na b'ata mata rai matuk'a da gaske. Don haka tsam na mike na fito tsakar gida na shiga toilet. Wanka na yi, sanan na dauro alwalar salllar wahala.A gaggauce na shirya, ganin umma har ta fito kofar d'akinta tana jira na. Wata shadda na sa pink color a sallar da ta gabata aka dinka min ita. Adon zaren dinkin blue aka yi mata. Don haka na yafa mayafi na blue.
Sosai na tsaurara kwalliyata don gudun kada a raina ni.yau ni ce har da eye shadow da jambaki.
Ko da na fita umma ta kalle ni fuskarta d'auke da murmushi take "Ko ke fa? Baki ga yadda kika yi kyau kika fito sosai ba, dan Allah idan munje kada ki yi k'uncin ran da ki ka saba musu ki saki jiki ki gaisa da kowa da fara'a kin ji?"
D'aga kaina nayi kawai ina mamakin sanyin hali irin na Umma ita kam taji dad'inta sosai, ba ta kullatar kowa a ranta. Zuciyarta fresh take akan Al,amarin duniya. Gata da son zumunci.
Adaidaita sahu muka tafi da yake gidan da nisa tsakaninmu chairman d'in hotoro take aure.
Kofar gidan dankam da mutane don ranar ne ake daurin auren, ga shi ba halin mu juya, da sauri na ja mayafina na rufe fuskata tamkar Zan fad'i haka k'afafuna suke harhard'ewa.
"Sannu da zuwa Umma." Muryar Y. Hisham na ji Yana gaishe da umma,bayan mun shiga farfajiyar gidan na d'an zame mayafina fuskata ta bayyana na d'an dubi inda yake caraf idona ya had'u da nasa. Ban tab'a ganin ya yi min kyau kamar na wannan lokacin ba.
Murmushi ya sakar min ya ce," kin gama boyon fuskar ta ki?"
Nayi murmushi sannan na gaishe shi
Umma ta ce "Har an d'aura auren kenan?"
Y Hisham ya d'aga kai idanunsa a kaina na rasa wani irin kallo yake bina da shi. Umma ce ta katse kallon ta hanyar cewa "To saudat mu shiga"
Na bi bayan umma muka tafi.
Koda muka shiga harabar gidan ba bu wanda yayi mana kallon arxiki bare mu samu kalmar sannu da xuwa. Da kyar muka samu muka ratsa babban falon gidan duk yayye da kannen mahaifina ne a gurin, sai y'ay'ansu da surukansu, masu ido da kwallli. K'alilan ne suka amsa sallamar mu, daga gefe muka durk'usa kan dole na gaishe su don gudun fad'an Umma.
Da kyar suka amsa kamar wad'anda aka yi wa dole babu wanda ya sake kallon mu muna daga gefe, sai can uwar bikin ta kallemu tace da Umma "Don Allah je ki baya gurin masu aiki ki taimaka musu "
Tsam umma ta mik'e muka nufi kofar da ta nuna mana. Aiki ne jingim don tuwo ne ake yi da shinkafa da jallop da alama abincin ya ku bayi ne, don dai jiga jigan na san sai dai ayi musu order hotel.
Nan da nan umma ta fara aiki ba ji ba gani.ni dai ido na zuba musu, don ban ga dalilin yi wa wad'annan matsiyatan bauta ba.
Ina gefe game nake a wayataa inna falmata ta shigo ta xabgan harara."To matsiyaciya, kina nan kina fama da shegen girman Kan tsiya ke ba y'ar kowa ba"
Sunkuyar da kai kawai na yi ba tare Dana tanka mata ba
Ta watso min kudi #2500 d'auki ki fita titi ki siyo min recharge card na min."
Na d'au kud'in ba don komai ba sai don ba na son b'atawa UMMA na rai, idan ban da haka duk ga k'annena a gurin ba a aika ba saboda su iyayensu suna da shi, ni kuwa da nake, y'ar fuk'ara'u dole na zama yar aike kamar yarda uwata ta zama y'ar aiki, madadin ta zauna cikin faccaloli y'an uwanta aka had'a min ita cikin masu aiki.
Jikina a salube na fita harabar gidan can gefen mota na hango Ya Hisham a tsaye da wata tsaleleliyar budurwa suna magana cikin nishadi har na gifta su na ji ya ce "Ke sauda."
Mamaki ya kama ni, don sam bai tab'a ambatar sunan ba. Na juyo da hannunsa ya min nuni da alamar na zo na k'arasa gurinsa don kuwa shi ma yana girmama iyayena.
"Baki lura da mu bane kika wuce?"
D'aga kai na yi kawai
"Ina za ki je to?" Ya sake jeho min tambaya.
Nace "Recharge card zan siyowa Inna falmata."
Ya d'ago kai ya dubeni kafin ya ce "Recharge card?duk ina yaran da suke aiki a gidan nan za'a aiko ki siyo recaharge card? Ke kuma ki ka fito siyowa ga maza haka za ki ratsa su?"
Cikin rawar murya na ce "To ya Hisham ya zan yi?"
Sak yayi Yana kallona.sannan ya zabga tsaki "mts:::::: wani layi take amfani da shi?
"Nace MTN "
Ya kalli bakuwaraa yace" bani two minute dan Allah " ya fice yana cewa" ke kuma ki tsaya ki jira ni anan, da ina da numberrta ma sai na mata vtu." Ya wuce bai lura da hararar da budurwarsa take zabga min ba......Jikar Nashe ce✍🏽✍🏽
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
Fiksi UmumLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...