Zumuncin Zamani.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Allah ya taimaka fuskarta a cikin nik'ab ta ke da sauri ta wuce Fareedan kamar zata bangajeta. Har Fareedan ta ji kamar ta shak'ota ta ji dalilin da ta mata hakan sai dai kawai ta yi tsaki ta saka kanta cikin 'dakin Hisham ba tare da lura da ita ma Saudan daga ciki ta fito ba.
Yana jin motsin shigowarta Ya runtse idanunsa kamar mai barci don sam baya son surutu a halin da yake ciki Mafita kawai yake nema. Ta zauna a bakin gadon tana k'are masa kallo tana kwatanta shi da Mahmud sai take ganin Mahmud 'din ma Ya fi shi kyau musamman yanzu da Shai'dan yake sake k'awata mata Mahmud 'din.
Har Magriba ta yi bai samo wata gamsashshiyar Mafita ba da ta zarce ya sanar da Abba Mustafa ko da ta cikin waya ne, don ganin yarda Sauda ta tunzira Ya San zata iya biyewa Umma suka aikata abinda suke so kamar yarda ta ce. Ya dinga jin zuciyarsa a k'untuce dole ne Ya zartar da hukunci na k'arshe da zuciyarsa ta amince da shi.
Fareeda tana tafiya Ya samu ya tura Usman samo masa Nama gasashshe da fresh milk. A sannan ya samu damar dannawa Abban Sauda kira a waya.
Tsawon lokaci wayar Abban Saudan tana ringing sai dai bai 'daga ba, yarda take ringing haka take tafiya da bugun zuciyar Hisham da gaske a tsorace yake a tsorace yake da hukuncin da yake son zartarwa.
A bugu na uku ne Abban ya samu ya dakatar da lazimin da yake na bayan Sallar Magriba Ya 'daga wayar yana mamakin kiran da Hisham 'din yake doka masa.
Hisham 'din ya gaisheshi with a cooler voice. Abban ma babu komai a ransa Ya amsa masa cike da kulawa yana sake tambayrsa yanayin jikinsa "Da sauk'i ina ga ma su ba ni sallama nan da kwanaki ka'dan." "To, to Masha Allah, me ya faru na ga kiranka da yawa haka?"
Murya a sark'e Hisham ya ce "Abba alfarma zaka min, ka tausar min Umma kada ta aiwatar da k'udirinta na amince a wannan gab'ar zan rabu da Sauda don naga ko ta ina Babu mafita."
Cikin rashin sani ya ce "Me kake fa'da ne Hisham? Me ita Maryamun take shirin aikatawa wane k'udiri ne da ita Wanda ni ban sani ba?"
Cikin kukan da bai San ya fara shi ba ya ce "Ta rantse sai ta salwantar da juna biyun da Saudat take 'dauke da shi..."
"Me?" Abban ya fa'da a ki'dime "Ita Maryamun ita ce ta furta hakan da bakinta? Yaushe kuma wa ya sanar maka don ni ban ma san Sauda na da ciki ba."
"Ni kai na Abba ban sani ba, nima jiya Saudatun take sanar da ni."
Tuni zufa ta fara karyowa Abba ya ma kasa furta komai sai jan hucin b'acin rai mamakinsa 'd'aya yaushe Maryamu ta zama mai kafaffiyar zuciya haka? Ashe haka mai hak'uri yake bai iya fushi ba? Cikin jin kunyar Hisham 'din da ta taso ta masa naso lokaci 'd'aya ya ce "Ka yi hak'uri Hisham, ban san da wannan maganar ba, Amma zan yiwa tufkar hanci Babu Wanda Ya isa ya aikata hakan a gida na Maryamu bata kyauta min ba ta yi aiki da sharrin shai'dan wannan ai rashin yarda da k'addara ne, Ka yi hak'uri ka ji ka yi kyan kai da baka sanar da kowa wannan maganar Mara da'din ji ba. Kai dai abinda nake so da kai ka cika alk'awarin ka na sakin Sauda da zarar ka fito daga asibiti."
Hisham Ya saki ajiyar zuciya Ya ce "Shikkenan, nagode Abba." Ya kashe wayar yana tauna leb'ensa ka'dan.
Abba yana kashe wayar ya mik'e ya nad'e tabarmar da yake kai da sauri ya shiga gidansa ransa a b'ace.
Yanayin da Umma Maryam zata ce ba ta tab'a ganinsa a hakan ba, tun tsawon aurensu don idan ba idonta bane ya gaya mata k'arya sai ta ce Har huci ta ga yanayi kafin ya shige 'dakinsa, don tabbas idan ya tsaya a wajen a take zai iya yanke hukuncin da za'a zo ana dana sani dan zai iya sakinta.
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...