Zumumcin Zamani.
Na
Nazeefah Sabo Nashe
(Typing: Fad'ima Sabi'u D'ankaka. Ku mata addu'a Allah ya saka da alheri yasa ta koma saudiya kwana kusa.😊❤️❤️ burinta kenan a gareku.)
08033748387
(Kyauta ne.)
Gabadaya suka hada baki wajen fadin "innalillahi wainna ilaihir raji'un"
Y Mahmud ya ce "Abba garin ya ya?l
Abba ya ce "Allahu a'alamu Mahmud, mu k'arasa mu gani."
Sauda na jin haka ta zira hijab d'inta haka nan Umman Sauda Abban ne ya watso musu wani kallo ya ce "Ku kuma ina za ku?"
Cikin rawar murya umma tace, "Zuwa za muyi mu gani"
Abban ya girgiza kai kafin ya ce "Ku je ku ga me? Ku ga tashin hankalin, bayan haka ma da mutane dank'am a wurin ku koma ba na son shirme da shiririta"
Jikin Umma a salub'e ta juya ta zauna. Haka nan Sauda ta bi bango ta rakub'e tana hawaye. Umma tace "Sauda yi kukanki ba zan hana ki ba wallahi, don dole ne abin kuka ya samemu innalillah wainnah ilaihir raji'una!"Mata ne mak'ota suka shishshigo kowa fuskarsa d'auke da taysayi, ya ku bayi ne kamar gisansu Sauda. Kuma suna zaman mutunci da su suka zauna suna taya su jaje. Inna Sahura ta fara zuwa da danginsu, sananan Inna maryma. Sai sha biyun rana sauran suka fara zuwa, duk wanda ya zo kuma ba ya zama sai dai ai jaje a tafi hakan ya tunzura zuciyar, Saudat saboda ta tabbata da wani ne haka ya same shi da wuni Ummanta zata ce su je su yi.
Jajen kawai ake zuwa a yi ba tare da an miko ko sisi an ce ga shi a bawa Abba ba, duk da babbar asarar da ya tafka. Sai yammah Y.Hisham ya zo gidan afujajen ya shigo a lokacin yake fad'a musu ba ya gari sai sha biyu ya samu labari ya je Abuja.
Yayi musu jaje sosai, sannan ya dauki naira dubu dari (#100,000)ya ba Abbansu, ya ce kuma insha Allah zai mayar masa da kayan shagon.
Sosai akayi godiya har da Saudat, don bai tab'a burge ta kamar yau ba, ya kara k'ima da mutunci a idonta.A nan yake sanar da su Y. Mahmud duk sanda ba su da karatu su dunga zuwa kamfaninsa, ba zaa rasa inda za a saka su ba, Sa'eed da Sa,ad kuwa ya ce su tsaya tare da Abba a shago.
Bai bar gidan su ba sai dare, yana tafiya kuwa suka dira faifan yabonsa tare da matuk'ar girmama k'ok'arinsa, Abba kuma yayi alk'awarin aura masa Sauda da son iyayensa ko babu. Don ya yaba da k'ok'arin sa matuk'a da gaske, tunda abin ya faru babu wanda ya d'auki ficika ya bashi daga danginsa duk da bai ba wanda bai sani ba, amma bai sani ba ko sai nan gaba.
Sauda ta shiga d'aki ta d'auki waya ta kira shi karo na farko a rayuwarta ,don kam yanzu ta aminta da shi kuma ruwa da iska babu mai hanata auransa. Bugu d'aya wayar ta yi Hisham ya d'auka cike da farin ciki yau Saudat ta kira shi. Cikin murmushi ya ce "first in life, yau Saudatuna ta kira ni da Kanta."
Murmushi ta saki ta ce "Y. Hisham ya ka je gida?"
Shiru ya yi yana sauraren tattausar muryarta,ya saki ajiyar zuciya ya ce "Sweety, please! ba na son Y.Hisham d'in nan ki dinga kirana da Dear Hisham."
Lumshe idonta ta yi ta ce 'wannan sunan ya fi k'arfin bakina yanzu."
" Sai yaushe?" Ya cillo mata tambayar
Tsit ta yi
"Sweety,ba kya ji ne?"
Yace, "ok, fad'a min sai yaushe?"
Can k'asan makoshinta ta ce, "sai mun yi aure."
Ai ji yayi tamkar ya nutse don tsananin taushin muryarta "Hello!" sai ya ji d'if, ta kashe gaba d'aya hakan ya tabbatar masa da kunya ta ji ya saki murmushi ya tura mata sako
"Ina son ki sweety"
Da kyar ya samu ya yi barci saboda tsananin soyayyar sauda. Hakan ya sa ya kudurce a ransa gobe zai samu mahaifinasa a yi wacce xa ayi, shi kam babu abinda zai Hana shi auren Saudatunsa.....A dining room ya samu mahaifin nasa Yana zaune Yana cin abincin kala-kala wanda Hisham ya tabbatar sun fi 'karfin cikinsu,A nutse ya gaishe shi shima cikin kulawa ya amsa wa Hisham, don kam yana ji da shi a cikin y'ay'ansa saboda dollars d'in da suke hannunsa.
"Hisham ya aka yi yau ba ka fita da wuri bane?"
Hisham yace, "Wallahi kuwa sai kuma ka ji abinda ya faru."
Abbansa ya d'aga kai cike da rud'ani ya ce, "Na me fa?"Hisham ya ce , "Na gidan Abba Mustafa, wallahi Daddy na matuk'ar tausaya masa."
Tsaf Alhaji ya gintse fuskarsa ya ce" Eeeh haka ne, Allah ya kyauta, ita rayuwa ai ta gaji haka, samu da rashi"
Hisham ya ce. "Haka ne." Bayan d'an shiru ya ci gaba "Daddy Dama nazo sanar maka wata magana tare d amincewar ka."
Ya d'ago Yana kallon sa, "Ina jin ka Hisham"
"Daddy daman so nake a yi min izinin auren yar gidan Abba mustap ...."
Da sauri Alhaji Hamza ya d'ago har cokalin hannunsa Yana fad'uwa, cikin matuk'ar mamaki yake kallon sa, "Hisham ban ji me ka fad'a ba, ba tare da fargaba ba, Hisham ya ce "Izinin auren 'yar gidan Abba mustapha.""kaiiii dakata!! Wane Mustafan kake nufi!!?
Hisham ya ce. "Abba mustapha k'aninka nake nufi"Alhaji hamza ya girgiza kai had'e da cewa "Cab' amma kuwa Hisham yau na tabbatar ba ka san ciwon kanka ba. 'Yar Mai k'ashin tsiyar za ka aura?Wanda duk abinda ya tab'a ba ya albarka kowa ba yaso ya rab'e shi saboda ba shi da k'ashin arziki? To wallahi ba ka isa ba!! Ka sake ka rab'e shi komai naka sai ya tsiyace ban da abinka yanxu zamani ne da kowa ya sani Mai kud'i sai mai kudi, talaka sai talaka d'an uwansa zamani ne da auren soyayya a wajen masu kud'i ya zama tarihi sai na wanene Ubanki? Ina hankalinka yaje Hisham? Muna nan muna Neman maka aure gidan manyan mutane ka b'ige da neman d'iyar Mustafa toh ba zai yiwu ba wallahi, ka sake zance."
Hisham ya lumshe idonsa yace, "Dan Allah Daddy ka duba batun nan, Abba mustapha fa jininka ne, wannan kuwa bare ne."
"Kai rufe min baki yaron banza kawai. To akwai wani bare a wajen mai kud'i yanzu da ya wuce talaka ko uwarku d'aya ubanku d'aya da mutum,yanzu wa yake ta zuminci?Kawaii inda za ka huta zaka nema, shi ma Mustafan da ba ka da shi ba zai ce zai ba ka d'iyarsa ba. Kuma wallahi zan same shi sai ya san ya shigo gonata."
Hisham ya d'ago da kyar ya ce "A'a Daddy ni ne na ce Ina sonta ba shi ya bani ba"
Cikin matuk'ar fushi Alhaji Hamza ya ce, "Tashi ka bani wuri ba na son maganar banza yanzu haka mustapha asiri ya yi maka, ni ban san yaushe kuka d'inke da shi har haka ba. Kowa yana gida sai kai kana lik'e masa, idan ya tsiyata ka kai ka sani, waye bai san k'ashin tsiya ne da Mustafa ba. A can danginsa uwarsa ya gado kashin tsiya, saboda haka ka fita idona, Kuma maganar aurenka zan dawo da ita nan da wata d'aya. Zan samu honourable muyi maganar, shashashan banza me aka yi akayi mustapha bare d'iyarsa gadon tsiya da talauci, garar arziki ba samunta za kayi ba idan ka auri y'arsa sai dai su kwashi nasu rabon a jikinka."Daidai lokacin hajiya laraba ta shigo falon tana fad'in "Ni Alhaji fad'an me kake ne ana jiyo ka fa tun daga can k'asa"Alhaji Hamza ya ja tsaki ya ce "To fad'an me zan yi Hajiya ban da ni da wannan shashashan d'an naki wanda arziki yake binsa shi kuma yana bin tsiya da gudu? Wai d'iyar Mustafa yake so." Hajiyar ta zaro idanu tace "Me? A,a wallahi wasa yake Alhaji ka san Hisham da tsokana."
Alhaji hamza ya ce. "Bilhakki da gaske yake gashi nan ki tambaye shi..."
Mommy laraba ta juyo ta karewa Hisham kallo ta ce "Hisham da gaske ne?"
Hisham ya d'aga kai "Haka ne Mummy"
Ta kuwa girgiza kai tace "To baka isa ba wallahi in dai ina raye ba ka isa ka aure taba shashanshan banza kuma na sake jinka ka je gidan ma sai na sassab'a maka, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani auren yar gidan Mustafa ai tamkar siyan talauci ne da kud'inka."Jikar Nashe! Mai tak'ama da ikon Allah.
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...