Zumuncin Zamani
Part 2 free book
08033748387
Na Nazeefah Sabo Nashe. ✍🏽
1
Alh. Amadu ya zura hannunsa a cikin aljihu ya zaro kud'in y'an dubu-dubu ya zari guda ashirin ya ajiye masa a wulak'ance alamu suna nuni da tilashi aka masa. Murya a shak'e ya ce "Ga kud'in neman aure nan Naira dubu ashirin, wannan kuma Naira dubu talatin na saka rana idan ka had'e su jimilla za su baka dubu Hamsin kenan cif. Tunani muka yi gwara a kawo kud'in za su fi muku amfani akan kayan da ku wasu ne ma lefen ma kud'insa za ku karb'a. Kwa siya mata kayan d'aki da su tunda dai mun san baka ajiye ba ba ka bawa wani ajiya ba." Abba Mustafa kuwa murmushin takaici ya dinga jefa musu zuciyarsa cike da mamaki da lamari na duniya mai cike da rud'ani iri da kala. Kafin ya yunk'urin cewa wani abu tuni sun mik'e kamar dama akan k'aya su ke. Ahamdun yana cewa "Alh. Lawal sai mu wuce ko? Don ni ina da abubuwa masu muhimmanci fiye da
Wannan d'in da aka min tilas." Shima Alh. Lawal d'in mik'ewa ya yi yana sab'a babbar Riga yana cewa "Ai nima haka Ahmadu banda abinka zaman me za muyi anan d'in da dai wani gidan ne sai mu tsammaci tukuici amma nan mai na sama ya ci ma balle ya bawa na k'asa." Suna fita Abba Mustafa ya bisu da kallon mamaki kafin murya a sahhale ya ce "Jalla ya kyauta." Ya kwashi kud'in a hannunsa ya shige cikin gida, zuciyarsa fal da tunanin rashin son auren banda Yana ganin girma da mutuncin Baffan Wudil da bai amince ba to k'aunar da yake wa mahaifinsu ce ta koma kan Baffan, yana kuma jin ba zai iya k'in yi masa biyayya ba matuk'ar zuciyarsa zata dinga hasasho masa waccan wasiyyar ta mahaifinsu a bigire mafi girma a zuciyarsa.Ko a cikin gida zancen da suka dinga yi kenan, k'iyayyarsu ga auren sam bata kwatantuwa. Ita dai Sauda na jin su bata da bakin amsawa amma zuciyarta tafi tasu zafi da tafasa idan ta tuna tarin matsalolin da suke tunkaro ta, wala Allah ta ta jarrabawar kenan, sai dai fatan ta amsa ta da kyau tare da taimakeni addu'a da ta tabbatar itace takobin da ta rik'e.
Abba Mustafa cikin b'acin rai ya ce "Ficika ba Zan ci a kud'in nan ba, wajen mai kayan gado zan je na fara bashi wani abin kafin mu ga abinda Allah zai yi. In sha Allah yarda suke son na ji kunya Ubangiji ba zai jiyar da ni kunyarsu ba, shi lamarin Jalla ai girma gareshi matuk'ar zaka sakankance da cewa shi zai maka zai kuwa shayar da kai mamaki. Mu yi ta addu'a Allah ya fitar da mu kunyarsu duk da dai ba mu da arzikin da za mu basu mamaki amma za mu yi mata hana gori ko bakomai bahaushe ya ce "Da Hannau gwara Mannau kuma sandan da yake hannunka da shi ka ke kai duka."
Saudat runtse idanunta ta yi tana jin wani irin zazzafan tausayin iyayenta yana zagwanya a k'irjinta yana haifar mata da wata irin k'una tausayin su take ji sosai bata san k'addarar da ta kawo Hisham cikin rayuwarta ba, ba burinta bane auren mai kud'i tafi son talaka d'an uwanta inda ba yarda zata je a mata gori amma ya ta iya da k'udirar Rabbani. Ta san yanzu Babanta zai d'aga hankalinsa duk da ta san shi ba mutum bane mai sanya damuwa a ransa shi yasa ko hawan jinin nan na zamani ba shi da shi, yana da kyautayi da tawali'u yana maraba da duk abinda Allah ya bashi yana kuma rok'ar Jalla arziki mai amfani kamar yarda yake neman tsari da arzikin da zai zame masa masifa arzikin da zai kasa taimakon mai neman taimako Arzikin da ake kira daga k'auri sai cinya. Ko bashi mahaifinta baya ci koda kuwa za su rasa abin kaiwa baka ya kan ce ku yi hak'uri mu d'ora da azimin tunda dai ku ba yara bane.Ranar sukuku ta wuni, Umma na hankalce da ita, sai dai hats furta mata komai ba tana son hasasho mai ya addabi zuciyar d'iyar tata.
Da yamma Hisham cike da zakwad'i ya yi mata waya cewa ga shi a k'ofar gida kunyar Umma da Abba yake ji shi yasa ba zai shiga ba. Da tana cikin sukunin zuciya da ta zolaye shi sai dai ba wannan damar a ranta. Ta zura hijabinta kawai ta sanar da Umma yana waje yana jifanta Umma ta rik'e hab'a tana cewa "Yau kuma Hisham wani sanaben ya samu? Shi da gidansu zai rakub'e a waje sai Abbanku yazo yana fad'a kice masa ya shigo ciki ai ba shi da maraba da y'ay'an gidan har kullum Abbanku yana fad'a."
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...