Zumuncin Zamani..
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
(Typing: Fad'ima Sabi'u D'ankaka, ina godiya da k'ok'arin ki gareni jazakillahu bil jannatil firdausiya uwar gidan Isa Dankaka.)
Hisham shiru kawai yayi tare da tsananin mamakin iyayen nasa, tamkar dai Abba mustaphan shi ya d'orawa kansa talaucin. Allah alhakimu, Al'amarin kyamar talauci ya ta'azzara kwarai a zuciyar iyayensa Yana dago Kai ya ga wajen wayam sai shi kad'ai a falon.
Jikinsa a salub'e ya mik'e ya bar wajen, don zuciyar sa tayi nauyi sosai yana tunanin menene mafita kuma?Kashegari duk da ba ya jin dad'i haka ya mik'e ya tafi gidan Abba mustapha, babu mutane ko kad'an sai dangin Umma da Inna sahura, bayan ya gaishe su waya ya yiwa Sauda ya ce Yana jiranta a waje.
Doguwar riga ce a jikinta, hakan yasa mayafi kawai ta nad'a ta nufi k'ofar gidan wajen Hisham, yana cikin mota ta bud'e ta shiga, alamar damuwa ta gani k'arara a Fuskarsa, hakan yasa ta gaishe shi had'e da fad'in "Y.Hisham, meke damunka?"
Murmushi ya dan yi yana sakin ajiyar zuciya ya ce "Babu abinda yake damuna Saudatuna illa tsananin soyayyar ki,Saudatuna please ki tayani addu'a mahaifina ya amince min na aure ki."
D'if ji da ganin ta suka d'auke, jikinta a sanyaye ta dube shi ta ce "Y. Hisham na san za a rina shi ya sa tun farko abinda nake jiye maka tsoro kenan ka kasa fahimtata, na sani a danginmu mun fi kowa bak'in jini duk a dalilin talauci da Allah ya jarrabi mahaifinmu da shi, Y.Hisham dan Allah ka janye daga batun aurena"
Wani kallo ya wurga mata, ya dakatar da ita daga cigaba da magana "Saudatuna za ki iya hak'ura da ni? Ashe akwai abinda zai sa ki janye daga aurena? ki kalleni nan, duk rintsi duk wahala,ni babu abinda zai sa na janye daga zancen aurenki.Ina so ki san haka,kuma ki janye daga ranki duk rintsi duk wahala ba zan fasa auren ki ba, ban fara neman aurenki don na bari ba, zuciya da ruhi gaba d'aya muradinsu aurenki, ba ki san yarda nake son ki a cikin raina bane, da ba ki kawo min maganar na hak'ura da ke ba." Shiru ta yi don kam ita ma yarda ta fad'a cikin soyayyar tsamo tsamo,ba ta jin zata iya rabuwa da shi, a hankali ta ce"Y.Hisham, ka yi addu'a"
Zuwa wani dan lokaci ya sallame ta, yaja mota ya yi gidansu.
Da safe ko da ya yi wanka kamar yadda ya saba karyawa a cikin gidan su, k'a'idarsa ce, ya shiga falon gidan Gaba d'aya iyayensa suna zauna har k'asa ya durk'usa ya gaishe su don kam Hisham yaro ne mai matuk'ar biyayya da sanin darajar iyaye.
Har zai mike Alhaji Hamza ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Kai zo mana"
Hisham ya koma ya zauna
Daddy ya sha mur ya ce,"Kamar yadda na sanar dakai, munyi magana da honourable ya amince da dawo da bikin nan da wata d'aya, haka sai ka bada kud'i mummyn ka taje dubai ta had'o kayan lefe Muryarsa can k'asa kai daga ji ka san ba ya son auren, ya ce "Daddy kamar nawa zaa bayar?" Alhaji hamza yace "Ga tanan ka tambayeta, ita ta san kan harkar kayan mata, abu d'aya na sani aljihunka zai yi kuka sosai, don 'yar gidan manya ce." Hisham a zuciyasa ya ce "Na sani haka dai sai dai nawa yayi kuka,amma wallahi ba zan wahalar da kaina akan wata banza ba, ya d'an kalli mummy yace "Kamar awa za'a bayar Mummy?"
A kaikaice ta ce "Ai da yake ba wata mahashuriyar k'arya za mu yi ba, tunda dai sun fi mu wadatar arziki, don haka sai mu tsaya a matsayinmu saboda haka ina ganin miliyan takwas ma ta Isa."
Da sauri Hisham ya d'ago kai cikin zare ido ya ce, "Million takwas Mummy? Gaskiya ba zan iya ba, akwai wahalwalu da yawa a gabana, ai na yi ma k'arya sai kace wata y'ar Gold".Da sauri Alhaji Hamza ya dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hannu ya ce "Ya isheka, mutumin banza kawai, zaka ce wani sai kace y'ar gold, ai k'anwar y'ar gold d'in ce, tunda ubanta ya raini y'arsa da Naira,Ai dama za ka ce haka mana tunda yanzu idonka ya rufe kana son y'ar talakawa,toh bud'e kunnenka da kyau ka jini,ba gidan kananan mutane xaa kai lefen ba, don haka dole ka ba da kud'in ka aka nema, za kace baka da miliyan takwas, to ka ba da miliyan biyar, ni na cika ukun."
Don dole Hisham ya amsa ya mik'e ya bar wajen zuciyar sa na tuk'uk'in bak'in ciki, wanann shi ake kira k'ara wa mai k'arfi _ k'arfi. Allah na tuba ya raya a ransa. Da na ba da wad'annan mak'udan kud'ad'en a kan wata banzar bidia ba gwara na tara miskinai na raba musu jari ba? Balle ga Abban Sauda da yake cikin yanayin Mai buk'atar a tausaya masa matuk'a,amman babu abinda danginsa suka saka a gabansu sai son zuciya da son a sani, babu mai yin Abu fisabillahi.Don dole ya turawa mahaifinsa kud'in, bayan ya isheshi da waya ko ba don haka ba yana so ya sake lallab'ar su, su amince masa auren Saudat, zuciyarsa ce ta bashi shawara akan ya je ya samu Inna falmata da zancen, ya san mahaifinsa yana sauraron maganarta,kasancewar tana da abin hannunta.
Inna falmata tana ganin sa ta saki fara'a, tana fad'in "Maraba da angon gobe"
Zuciyar sa ce ta karaya don ya san da k'yar zai samu nasara a gurinta, amman bari ya gwada ya gani.
A kan kujera ya zauna yana fuskantar ta. Bayan ya Mik'a gaisuwa ta kalle shi ta ce "Ya aka yi Hisham? Ko kazo mu tattauna zancen bikin ne? Don d'azu Abbanka ya yimin waya yake sanar da ni na fara shirin tafiya dubai hado laifanka, kai fa naji dad'in wanann zancen ai Hisham ka yi dace da gidan arziki, gidan wadata wanda kowa yanzu burinsa kenan a ce ya auri yar gidan wane, duk cikin y'an uwa ma babu wanda yayi dacen da kayi tabbas ka yi auren nasara kai gaba d'aya rayuwarka ma a cikin nasara take masha Allah......
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
Ficción GeneralLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...