Zumuncin Zamani.
08033748387.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
Daga k'ungiyar Elegant Online ✍🏽
Masu nemansa daga farko su Duba a wattpad.
@Nazeefah381 nagode.
_____________
Kunya ce sosai ta kamata jin shine da kansa yake gaisheta. Cikin wani salo na jan hankali ta yi k'asa da murya sosai kafin ta ce "Y. Hisham Ina yini?" Murmushi ya saki hankalinsa a yanzu ya d'an kwanta ganin akwai alamun sassauci a tattare da ita ya gyara zamansa sosai, yana dubanta ya ce "Lafiya lau, ya aka ji da fushi da mu? Ban yi tunanin ko mata hud'u na ce zan aura rana d'aya ba za ki guje ni saboda haka, tunda kin san ta ki k'aunar tafi ta su a zuciyata you are so special to me." Ya fad'a yana narkar da idanunsa cikin nata, lamarin da ta ji ya fara d'imautar da tunaninta da ma nutsuwarta gaba d'aya. Amma sai ta bagarar tana d'an b'ata rai ta ce "Ka yi hak'uri na kasa danne kishina ne, ina da zafin kishi sosai da sosai, ga shi zuciyata tana bani ba zaman y'anci zan yi a gidanka ba ganin duk dangi basa bayan aurena da kai. Suna kuma ganin mu ba a bakin komai ba duk a dalilin talauci kamar mu muka d'orawa kan mu." Tsit Hisham ya yi ya kasa ce mata komai don ya san duka zancenta ba bu tasgaro gaskiya ce tsagwaronta, bisa dole ya ce "Ya kamata wannan issue d'in ya zama labari a wajenmu kin san dai ni nake son ki ba danginmu ba, don haka ki dinga tunanin a wajena kad'ai idan kika samu farin ciki kamar kin samu duka farin cikin duniya ne tunda dai ni ne muke tare kullum ki ture kowa a ranki ki saka Hisham d'inki ni kad'ai na isa na shayar da ke tsantsar farin ciki a doron duniyar nan, kin ji ni? Bana son a sake tada wannan maganar please."
D'aga masa kai ta yi kawai zuciyarta tabbas ta sassauta daga b'acin ran da take ciki. Hisham ya saki murmushi don ya hango yanda idanunsa suka mata dabaibayi suka hana ta katab'us shi kad'ai ya san kalar kallon da yake mata yau kallo ne mai nuna zallar muradin zuciyarsa. "Menene tsaratsaren bikin namu?" Ta jiyo muryarsa daga sama yana tambayarta don ita tuni ta lula wata duniya can, tsananin soyayar Hisham d'in ce take neman kawar mata da nutsuwa ban da tana daurewa. Ta d'an langwab'ar da kanta itama tana jifansa da madadin wancan kallon da ya kusa sanya shi ya janyota jikinsa da sauri ya ja A'uziyya ya runtse idanunsa musamman jin muryarta cikin wani salo tana amsa masa tambayarsa "Ba ni da wani tsari Y.Hisham walima kawai zan yi da zan kira Malamai su fad'akar da Mata akan zamantakewar aure sai saukar Alkur'ani da zan saka a yi da niyyar Allah ya albarkaci aurenmu da zuria d'ayyiba." Ya dad'e yana jinjina kai don ba d'an kad'an ba ya burgeshi don samun Mace mai irin halinta a zamanin nan sai an yi mugun dace. Ta san yana da shi amma bata d'orawa kanta wasu bidi'oin banza ba albarkar auren kawai take buk'ata su kuwa bidi'oi babu abinda suke kwashewa sai albarkar aure ina ma mata duka za su koma Sauda da matsalolin aure sun ragu. Ya ce "Shikkenan Allah ya sanya mana albarka zan nema miki guri mai kyau ki yi walimar hakan ya yi?" Ta d'aga kai tana sakar masa murmushi Daga haka ya mata sallama ta fice daga motar shi kuma ya rakata har k'ofar gida inda anan ma sai da ya sake janta da hira.
————————-
Da safiyar kashegarin ranar suka wayi gari da bak'in danginsu, su Inna falmata ne da Yayyan Hajiya Laraba wai suka zo ganin lefe. Umma dai cikin farin ciki ta tarbesu duk da ta san ba alheri ne ya kawo su ba sai son ganin k'waf.A yatsine suke kallon gidan kamar sun gama abin k'yama, Umma sam bata damu ba don gidanta tsaf yake ko tsinke babu a tsakargidan. Baya ga haka sai zabga k'amshin turaren tsinke yake kamar yarda ta saba sakawa a koda yaushe. Ta malala musu tabarma tana kallon yarda suke zama a d'ofane.
Inna Falmatan cikin isa da tak'ama ta kalli Umman Saudan ta ce "Kayan lefen Y'arki muka zo gani, duk da dai ba ki gayyacemu ba muna matsayin dangin ubanta." Umma ta d'an yi yak'en murmushi duk da ta san ba har zuciya Falmatan ta yi maganar ba ta ce "Wallahi ko kad'an ba haka bane, da yake Hisham d'in da abokansa biyu suka kawo kayan ba ma mu san
Da zuwansu ba sai ganinsu mu ka yi da kaya, amma Allah huci zuciyarku a yi hak'uri."
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...