Zumuncin Zamani.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Gaba 'd'aya k'wak'walwar kan Saudat ta toshe ta yi 'dif ta daina aiki.
"Ba magana nake miki ba?" Ta ji Umman ta fa'da a tsawace. Da sauri Saudat ta dawo daga tunanin da take ciki. Ta hau diri-diri kafin ta ce "Wallahi Umma ban sani ba, ina ji dai tun kafin a yi biki ne."
Salati Umman ta zabga ha'de da hirji ta ce "Hasbunallah wa ni'imal wakeel, Ubangiji kada ka tabbatar da zargina."
Da sauri Saudat ta ware ido tana son gano me Umman take nufi da ta wannan rikice haka sai dai ta kasa ganewar, hakan yasa ita ma a ru'de ta ce da Umman "Umma menene?"
Umman Jeho mata harara ta yi ta ce "Menene kuwa idan ba ciki ba. Hasbunallah wa ni'imal wakeel."
Ita kanta Saudat 'din bata san sanda a razane ta ce "Ciki Umma?"
"Ciki Saudat, tabbas ciki ne da ke, ki je maza ki dawo daga makarantar ki tafi wajen Sadiya Nurse ta aunaki, kada Allah ya tabbatar da zargina."
Da sauri Saudat ta fice har ga Allah ba wata makaranta da zata je, tuni suka yi covering lecture sai jiran exams burinta kawai ta je ta ga Hisham don haka tana fita ta tare Adaidaita ta sanar da shi inda zai kaita.
Sai da ta tambayi 'dakin aka nuna mata sannan gabanta ya fara fa'duwa a lokacin ta dinga jin tsoron afkuwar matsala. Ta ji kamar ta koma sai dai ina idanunta sun rufe kwa'dayi take kawai ta ga Hisham. Haka ta daure ta k'arasa 'dakin. Ta window take lek'a ta hango mutum uku ne a ciki, ciki kuwa har da Fareeda ta bi ta mak'alk'ale shi a jikinta, haushi ne ya taru ya cunkushe wa Saudat zuciya ta dinga jin kamar ta juya. Tana shirin sakin labulan 'dakin karaf idanunta suka ha'du da na Hisham. Da sauri ya waro ido yana kallonta ta sake labulen. Ta juya ranta a b'ace tafiya zata yi tunda matarsa na nan mak'ale da shi ta lura ma shan soyayyarsu suke, shi yasa ma baya son ta zo asibitin. Wato baya son ran matarsa ya b'aci.
Ta yi k'wafa tuni wasu hawaye suka b'alle mata, takaici take ji ace kai da mijinka sai ka dinga b'oyewa idan zaka gan shi. Da sauri ta yi hanyar fita daga gate 'don asibitin. Sai dai kafin ta fita ta ji sak'onsa ya shigo "Kada ki tafi Wify na! Yanzu zan sallamesu sai ki shigo kin ji Madam. I LOVE YOU."
Tsaki ta ja. Ji shi kamar gaske, yanzu haka ita ma matarsa haka yake saka ta a gaba ya fa'da mata. Ban da tana son ganinsa da tabbas tafiyar ta zata yi, wani bench ta samu ta zauna, tana dakon fitowarsu.
Shi kuwa Hisham yana kwance idonsa a runtse baya gane duk zantukan da Fareeda da Mahmud suke masa don yanzu sun 'd'inke sosai. Mafita kawai yake nema da zai kori Fareeda ya samu Sauda ta shigo. Ya saki ajiyar zuciya da samun fitar da ya yi ya bu'de ido yana kallon Fareeda "Madam tuwo nake sha'awar ci please, ki je Mahmud ya sauke ki sai ya jira ki gama ki dawo tare tunda Naga yanzu kin fi son tuk'insa ba kya son driving."
Murmushi suka sakar wa juna bayan sun ha'da ido, su ka'dai suka San ma'anarsa. Babu wani jinkiri suka mik'e "To kai ka'dai za mu bar ka?" Ya kalli Usman abokinsa "kada ki damu, Usman zai zauna Har ku dawo."
Ta gya'da kai "Shikkenan, dama na ga aikin tuwo da wahala, kada mu je mu shantake, ko Mahmud 'din ya dawo idan na gama na taho."
Hisham ya girgiza kai "A'a, ya tsaya ki gama, za mu tattauna da Usman."
Hisham ya yi saurin girgiza kai. "A'a, ya tsaya ki gama za mu tattauna da Usman."
Ba ta wani ja ba ta yarda, don dama abinda tafi buk'ata kenan, suka fice ita da Mahmud, zuciyarsu fal farin ciki, don yanzu wata zazzafar soyayya suka k'ulla ta haramci ita da Mahmud 'din. Yadda take jin da'din alak'a da shi ko yayansa albarka. A nata hasashen kenan. (Ubangiji yasa mu fi k'arfin zuciyarmu.)
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...