Zumuncin Zamani..
Na
Nazeefah Sabo Nashe ✍🏽✍🏽
(Typing: Fad'ima Sab'iu D'ankaka. Ubangiji Allah ya d'aukaka darajarki har a
Aljanna.)08033748387.
A haka Alhaji sule jami'i mutum ne nagari Mai nagartacciyar zuciya, sab'anin matarsa da ita sam ba ta son abin da yake yi tafi son kullum ya yi ta bauta wa danginta babu wajen malamin da ba ta Kai sunansa ba, amma sam ba ta samu sa'a ba, a wannan b'angaren.ta dai yi nasarar hana shi aure, don haka ba ta damu sosai ba, ta sani idan ya mutu babu mai gadon sa daga ita sai ya'y'anta biyu maza da auta fareeda, sai yayyenta Aslam da Akbar.
Koda ya shiga gidansa senator sule Jami'i fuskarsa a d'an had'e ya dubi madam d'insa yana cewa turo min fareeda.Da hanzari ta mik'e don duk abinta tana shakkarsa a wasu lokutan, har d'aki ta samu Fareeda tana sanar mata kiran mahaifinta, "saura idan kin je ya tambayeki ki ce kina son wannn shegen yaron, wallahi sai na sa'bar miki."Ta fad'a tana jan kunnenta sosai
Fareeda ta d'aga kai kawaii, don ita har a lokacin tana son Hisham.
A falo ta samu Daddynta, bayan ta yi masa sannu da zuwa ya ce ba ni numberr Hisham
Da hanzari ta bud'e ta shiga fada masa.
Alhji sule ya saka numberr a wayarsa sananan ya kira ta yi ringing sosaii kafin ya d'aga kasancewar bai San lambar ba.
Bayan musayar sallama Alhaji sule ya sanar da shi yana son ganinsa.
Hisham bai yi niyyar zuwa ba, kasancewar ya zata shima kiran sa zaiyi ya ci masa mutunci amma daga baya zuciyar sa ta amince masa yaje din yaji dalilin kiran. Idan ya so idan ya ji zai raina masa hankali kawai zai sanar da shi ya fasa auren y'arsa don ba yar gwal bace.
Sai da yayi wanka ya shirya cikin had'addiyar farar shaddarsa president, saboda ma ba ya so a raina shi yafi so a san shima a dire yake da k'afafunsa.
A tsadaddiyar motarsa ya fita ya kuma fesa Wani had'adden designer, sananan ya tafi ko a mota tunanin da yake sake yi kenan sam ba zai d'au wula'kanci da rainin hankali ba.
Ko da yaje wayar Alhaji sule ya kira ya sanar da shi yana wajen gidan. Alhaji sule da kansa ya fito waje ya taro shi, har hakan ya dinga bawa Hisham mamaki to yayi mamaki mana babban mutum kamarsa .
Da fara'a ya tare shi yana fadin "welcome my son, mu shiga daga ciki mana."
Hisham duk kunya ta baibaye shi don ganin yadda yake tunanin mutumin ashe sam ba haka yake ba.Bayan zaman sa Alhaji sule ya sa a kawo masa drinks, Hisham kurb'a d'aya ya yi wa lemon sannan ya sake duban senator.
Alhaji sule ya fahimci shi yake Jira,don haka yace "Hisham na san kayi mamaki dana ce ina son ganinka hakane?"
Hisham ya d'aga Kai "k'warai haka ne Alhaji."Senator ya gyad'a Kai yace. "Masha Allah,to daman ba wani abun bane na samu labarin ka sanar da fareeda su biyu zaka aura, har ta tayar da borin k'arya wai ita ba ta sanka." Yaci gaba "Mata kenan, su ba komai a Ransu sai son zuciya in dai a ka zo batun kishiya, amma abinda ya bani mamaki da na samu mahaifinka sai na ji ya ce wai ya hana ka auren yar uwar taka ne duk a bisa wani dalili nasa mara tushe,to Hisham abinda nake so da kai ka je ka ci gaba da neman auranka...."
Da sauri Hisham ya d'ago yana kallansa, Yana son tabbatar da gaskiyar abinda ya fada.Alhaji sule ya sake girgiza kai, k'warai ni nace ka je ka ci gaba da neman aurensu duka biyun Allah ya tabbatar da alkairi babu dalilin da zai sa kana namiji a hana ka abinda ranka ke so,ubangiji da ya halicce mu shi ne ya yarje maka auren mata hud'u,idan dai zaka yi adalci tsakaninsu. Don haka na sanar da mahaifanka tilas ya amince da auranka da duk su biyun idan ba haka ba ita ma fareeda ta hak'ura don babu dalilin da gida bai k'oshi ba za akaiwa dawa, fatana d'aya ka kasance Mai adalci tsakaninsu."
Hisham zubewa ya yi a k'asa sosai yana zuba wa senator godiya,tabbas ya sake ganin girma da mutuncinsa mutumin, Ashe a zamanin nan zaa samu burbushin irinsu?Alhaji sule ya mik'ar da shi sosai yace bakomai Hisham kaje ka ci gaba da shirye shiryen ka In sha Allah nan da wata gudan za a yi komai a gama tunda babanka ya ce ka gama gidanka. Àllàh ya sa ayi a sa'a
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...