Zumuncin Zamani.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
...........
A asibitin da aka kwantar da Sa'ad, Abba ne da Muhammad da Sa'id suna tsaye Sun yi cirko-cirko. Har zuwa lokacin sun rasa ku'din da za'a masa aikin a daidaita sahun da suke tak'ama da shi har yanzu ba 'a samu masu siya. Rok'on likitan suke ta yi Akan ya masa aikin daga baya za su kawo ku'din Amma ya k'i.
Ga Sa'ad sai murk'ususu yake cikin matsanancin ciwo. Zuwa lokacin ya fitar da rai da rayuwa. Abba ya matso kusa da shi ya 'dora kan Sa'ad 'din a saman cinyarsa ya rungumeshi yana masa addu'oi a kunne da kalimatushshahada don a jikinsa ya ji tabbas Sa'ad ya zo gangara. Yana kaf-kaf da hak'ora y'a dinga jan Kalmar shahadar a hankali kafin ya yi wata irin shak'uwa sau biyu ji kake 'dif shikkenan rai ya yi halinsa. Sa'ad Ya tafi an dace an yi shahada ya huta da tsanani da k'uncin rayuwa da suke ciki.
Abba ya kalli su Muhammad cikin raunin zuciya matuk'a da gaske ya ce "Shikkenan rayuwar mai rabawa ta raba Sa'ad ya tafi gidan sa na gaskiya."
Kuka sosai suka saka kukan da za su tara masa mutane Abba ya hau fa'da "Bana son rashin hankali ba kukanku yake buk'ata ba addu'arku yake buk'ata."
Likitan Kansa jikinsa ya yi sanyi, ya dinga Dana sani ya yi masa aikin...
Sa'id buga Kansa kawai yake yana fa'din "Why? Why? Sa'ad ne yasa ka yi gaggawar tafiya tun bamu cika burikan mu ba?"A motar asibitin aka sanya gawar Sa'ad 'din suka 'dunguma suka tafi gida cike
Da alhini da kuka. Tabbas ba su ka'dai ba mutuwar ta tab'a Abba shi kansa. Sa'ad ne mafi soyuwa a wajensa a cikin yaransa ta fi su tausayi ya fi su
Hak'uri da jarumta.Gaban Umma ne ya buga rassss
Dama tun safe take Jin bugun zuciya da fa'duwar gaba, ga shi duk jikinta ya yi sanyi kamar Mara lafiya.Jin ana cewa "Ku karkata ku shiga da shi ta karkace..." ta tabbata wani Abu mai girma ya faru da Sa'ad Wanda ta tabbatar mutuwa ce. K'afafunta suka gaza 'd'aukanta musamman lokacin da ta hango makarar asibiti da ake shigo da ita tsakar gidan. Ta daddage ta rusa kuka tana isa wajen da sauri murya na kuka ta ke furta "Malam kada ka ce min Sa'adu na ya mutu?"
Sosai ya shanye nasa kukan, don son kwantar mata da hankali. "Ki ajiye hankalinki Maryama, yanzu ne zaki masa gata ki nutsu addu'arki yafi buk'ata ba kuka ba, addu'a 'da ga iyayensa ba shamaki a cikin ta."
Ta 'daga hannunta cikin kakkarwa ta ce "Allah mun gode maka, Ubangiji ka sadashi da aljannar firdausi na yafe maka Sa'adu, Allah yasa kaje a sa'a, Annabi ya san da zuwanka, bi jahi sayyadil mursalina."
Muhammad ne ya dinga bugawa y'an uwa yana sanar da su mutuwar Sa'adu. An ci sa'a sosai mutane da dama daga cikin dangin Sun halarci jana'izar.
Haka aka yi jana'izarsa ya samu halartar 'daruruwan mutane. Umma tana ji tana gani aka 'dauke mata 'da aka fita da shi zuwa gidansa na gaskiya bata da damar ta ce a bar mata shi mai rabawa ta raba. Tabbas mutuwa akwai ciwo.
Bayan lokaci ka'dan mutane suka watse, musamman ganin ba wata mamora a zaman makokin, ba abinci za'a ci a k'oshi ba.
K'anwarsa Umma Maryam ita ta sa aka kawo shinkafa jallop ita 'din ma ko nama babu haka aka dinga cinta, Amma dai tabbas ya fi babu.
Tun daga ranar mutuwar y'an uwan Abba Mustafan suka masa sallam da cewa ba sai an yi zama ba kai ma kana fama da kanka ga rashin muhalli wadatacce." Murmushi ya yi ka'dan kawai ya girgiza kai ha'de da ce musu "Hakan ma nagode Allah ya saka da alheri."
Suka ka'da kawunansu suka tafi. Abban Hisham kuwa sai a ranar kwana uku sannan Ya zo musu gaisuwa. Gida Ya zama sai 'daid'aikun jama'a y'an uwan Umman Sauda da wasu tsirari daga cikin na Abba Mustafa. Sam ba su damu ba, Sa'ad dai ya mutu kuma zaman makoki ba shi zai saka Sa'ad ya dawo ba me za'ayi da zaman makoki banda surutan banza da zaman gulma.
_______________________
A hankali take sauka daga cikin jirgin jikinta sam ba laka. Tun a jirgin take jin fa'duwar gaba da tsinkewar zuciya wanda bata haufi wani mummunan abu ne ya faru ko yake shirin faruwa a gida. Ta dinga jan addu'oi kafin ta samu fa'duwar gaba ta daina. Hannunta cikin na Hisham ya jata jikinsa "Yaya dai My flower?" Idanunta ta 'dago da suka jirkice zuwa launin ja har da hawaye a cikinsu ta ce "Gida, something went wrong tabbas, ina jin wani feeling a zuciyata." Ta kama hannunsa ta 'dora a saman k'irjinta "Ka ji ko? Ka ji abinda nake ji? Bugu take sosai ina tsoro Habibi. Ga shi na taho ko sallama ban musu ba." Ya jata jikinsa sosai bayan Sun zauna saman wata kujera kafin motar da zata kai su masauki ta zo yana shafa k'irjin nata a hankali ya ce "Bakomai, Khairan In sha Allah, ki dinga jan Hasbunallah cikin zuciyarki."
K'arfe 8:00 na dare suka isa masaukinsu da yake cikin harami hotel 'din darul tauheed. A gajiye suke sosai don sun sha tafiya tunda sai da suka bi ta egypt kafin su iso Saudiya.
Ta samu sauk'in zuciya sosai musamman da suka je ta ga ka'aba, ta rungumeta cikin shauk'i tana adduointa. Bata tab'a zata ba bata tab'a a ranta zata je makka ba a rayuwarta sai bayan da tazo ta ganta ga ta ga 'dakin Allah anan ta baje jikin addu'ointa. Ta yiwa iyayenta da y'an uwanta sannan ta yiwa kanta da mijinta kafin ta saka 'd'aukacin musulmai baki 'daya. Tana yi hawaye na kwarara daga idanunta.
Towel ne a hannunta tana tsane gashin kanta. Bayan ta fito daga wanka. K'asa-k'asa take kallonsa cikin jin kunyarsa. Don har yau ta kasa sabawa da shi a duk sanda ya kusanceta bayan kammaluwar komai sai ta dinga jin matsananciyar kunyarsa. Ta gefensa zata rab'a ta wuce da sauri ya janyota ta yi masauki a jikinsa Ya dinga binta da wani sihirtaccen kallo. Ta kuwa runtse idanunta gam. Towel 'din ya karb'a ya dinga tsane mata gashin kan cikin wani salo mai tafiya da imanin masoya. Cikin k'asa-k'asa da murya ya ce "My sugar, kin ga wani abu kamar tau-tau a bayanki." Da sauri ta ware idonta ha'de da daka tsalle towel 'din ma ya zame gaba 'd'aya ya bar jikinta cikin tsoro da firgici.
Ya jata jikinsa "Ke stop it, wasa nake miki, ke 'din ce kamar wata munafuka a duk sanda aka gama harka sai ki dinga wani sussunne kai bayan ba abinda ba kya min, to meye na kunyar wani dare ne je mage bai gani ba?" Da sauri ta zabga masa harara cikin muryar shagwab'a ta ce "Yaya Hisham ba na so." Ya sake lalubar ta "Kina so ki sake yaudara ta ko? Ba ki San shagwab'ar nan ita take janyo Miki na kasa hak'uri ba?"
Da sauri ta tureshi "Ni dai ka je ka yi wanka Allah yunwa nake ji?"
Ya shige toilet kafin ya 'dan lek'o ya ce "Babu taimako?" Ta hau dire-dire
"Kai Yaya Hisham please ka daina wallahi kana kashe ni da kunyarka."
Santala-santalan cinyoyinta ya bi da kallo kafin ya ce "Kin ci sa'a ina sauri mu je haram da kin gane wa sarkin garinku."Ita dai ta tsuke bakinta don lamarin Hisham yana bata tsoro Sam baya gajiya.......
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...