Alk'alamin Jikar Nashe
Zumuncin Zamani
Daga k'ungiyar Elegant online✍🏽✍🏽
Ku karanta kyauta..
3
Ina ji Umma na sake yi masa murnar kammala karatu lafiya. "Oh, Hisham tun da ka tafi sai yanzu ka waiwayo gida? Tun fa kana k'aramar sakandire."
Ban ji amsar da ya bata ba, saboda muryarsa ta yi k'asa da yawa. Na ji dai Umma na fad'in "Masha Allah, sai aure kenan ko ka yi auren ne ma babu labari?"
Ji na yi ya ce, "Haba Umma, ya za'ayi na yi aure ba ku sani ba? Khalil ya yi aure ne,"
Umma ta saki dariya ta ce, "Ina fa, shi ko niyyar auren ai ina ji babu shi a zuciyar Yayan Sauda." Kasancewar haka Umma take ce masa.
Ina jinsa ya tintsire da dariya mai d'an sauti kad'an ya ce "Umma ai shi aure lokacine da zarar lokacin sa ya yi ba sai ance ma ya yi ba. Ni kuwa da a gidan nan akwai wata y'ar bak'ar yarinya mai tsiwar tsiya tana ina ne? Ko an mata aure?"Umma da su Khalil suka tuntsire da dariya kafin Umma ta ce "Sauda kenan ai kowa ya santa da wannan tsiwar da rawar kai tun tana yarinya, ba'a yi mata aure ba, tana uwar d'aka tana jinka."
Ina cikin d'akin na ji tamkar na fita in k'unduma masa zagi. Da gaske naji haushin halin da ya jingina ni da shi. Na runtse ido kin Umma na k'walla min kira na tabbata cewa za'a yi na fito na gaisheshi. Murya a ciki-ciki na amsa.
Daga bakin k'ofa na tsaya fuskata a had'e rik'e da k'ugu na ce "Ga ni Umma." Da sauri na ga ya d'ago kai ya zuba min dara-daran idanunsa.
Umma fuskarta a had'e alamar ba wasa ta ce "Ba kiga Yayanki Hisham ba ne?" Ta fad'a tana zabga min harara da take nuni da gargad'inta gareni. Hakan ya sa a dole na kawar da kai na kuma gaisheshi murya a cunkushe.
Murmushi ya saki yana amsa gaisuwata. Ya kalli Umma ya ce "Lallai girman y'a mace ba wuya tamkar ba ita na tafi na bari tana kukan wanka, wasan k'asa da shan majina ba." Da sauri na saki labulan na koma d'aki don ina ji a raina tabbas na cigaba da tsayuwa zan iya k'unduma masa zagi.
"Amma Umma ya aka yi na ga kun dawo nan gidan? Bayan ba a nan na tafi na barku ba? Yau fa har tsohon gidan ku na je na can k'asan layinmu sai aka ce min yanzu ba nan ne gidan ku ba, na zata ma Wani cigaba ne ya samu Malam ya sake Gina muku wani gidan, sai da na dawo na tambayi Mami ta ce min bata san inda kuka koma ba, Yanzu ma Idi driver ne ya rako ni ya koma. Umma wai me ke faruwa ne?" Ya fad'a yana sake k'arewa gidan kallo da alamar yana mamakin yarda muka tsinci kan mu a halin rayuwa irin wannan da muke ciki yanzu.
Umma murmushi kawai ta yi ta ce "Hisham Kenan, shi lamarin ubangiji da kake gani izzar sa da mulkinsa duk ya fi gaban haka, yanzu idan ya ga dama duk sai ya shafe babinmu, ba ma dukiya ba, duk ikonsa ne, mun gode masa ma da ya ba mu lafiya da wadatar zuci, abubuwan da suka yi k'aranci kenan a wajen mutane, bawa ba shi da ikon canja duk wata k'addara da jalla ya hukunto masa Alhamdulillah ala kulli halin." Daga haka ta kawar da maganar ta hanyar tambayarsa wai yaushe za mu sha biki ne Hisham, tunda dai da rai da lafiya da wadata ya kamata ka angwance haka."
Ya sunkuyar da kansa yana shafa k'eyarsa ina kallonsa ta cikin labilai ya ce "Muna nan muna dubawa Umma, kin san y'an matan yanzu ne sai a hankali Umma su ba k'warya ba balle ka k'wank'wasa ka ji ta gari." Umma ta ce "Haka ne kam, to Allah yasa a yi gam da katar da ta garin." Tsaki nasa a raina na ce "Shegen iyayin tsiya, sai kace shi na garin ne."
Ina jiyo sallamarsa yana cewa Yaya Khalil Sai yaushe?" Ya ce "Zan shigo gidan naku ai, Insha Allah ranar da ba lectures."
"Kada ka ce min har yanzu baka gama makaranta ba?" Y.Khalil ya d'aga kai cikin son tabbatar masa da haka ne. "Ka san abubuwan ne sai a hankali ina HND 2." Bai sake cewa komai ba ya juya had'e da furta Allah ya taimaka" suka fice tare da Yaya Khalil.
YOU ARE READING
Zumuncin Zamani
General FictionLabari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha'da aure da y'ar mai ku'di fiye da y'ar 'dan uwa. Ya k'arshen ya zama........ kai dai karance Zumunc...