1

425 11 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

01


Plz follow me on
Arewabooks: Azizat Hamza
Wattpad: Azizat_Hamza

Ƙaran kiɗa ne ya karaɗe ilahirin ɗakin. Yadda speakers ke bugawa gin gin gin kace wani ƙaramin club aka buɗe a wajen. Yadda aka yi kiɗan bai tashi mutumin dake kwance a kan wani makeken gado ba sai Allah.  Babu mamaki shi ya kunna kiɗar kuma ya saba da hakan.

Ashraf! Ashraf Habibi! Habibi!

Wata mata ce tsaye a bakin ƙofar ɗakin tana ta bubbuga ƙofar amma ƙaran kiɗan ya hana wanda yake cikin ɗakin ya jiyo ta.

Da sauri ta juya ganin fa ihun da take ko kusa bai isa kunnen wanda yake ɗakin ba, duk ihun da take ita kaɗai ke jin abinta.
Yadda ta koma wani corridor ta dinga saukowa daga stairs da sauri sauri zai tabbatar maka ta ƙosa tayi magana da mutumin dake ɗakin sama.

Kai tsaye drawer dake wajen dressing mirror ɗinta ta nufa ta jawo na ƙasan ta zura hannu da sauri ta ɗauko wasu keys a ciki. Kan kace kwabo ta fita ta sake haurawa matakalar, da alama ta saba da irin haka jiba da yadda ƙibar data haɗa bai hanata hawa saman da sauri ba.

Matar ta saka key ta buɗe ɗakin da kiɗan ke fitowa. Hmmm! Har lokacin mamallakin ɗakin bai san wainar da ake toyawa ba.

Ta haura tsakiyan gadon ta fara makan bayan mutumin dake kwance yana sharan barci abinsa.

"Habibi wake up, Ashraf Habibi"

Mutumin da aka kira da Ashraf ya fara motsa idanunsa a hankali.

"Ashraf your Dad is coming, ka tashi kafin ya ƙaraso"

Kaman wadda aka watsawa ruwan sanyi haka ya tashi a firgice.

"Mom, Dad ya shigo Abuja?"

"Shit!" ya tashi da sauri ya fara dube-dube yana neman abinda zai ɓoye. Duk da dai yana wahala Dad ɗin nasa ya hauro saman saboda lalurarsa, but you never know.

Daga shi sai wandon pyjamas ɗinsa kalar navy blue ya shiga banɗaki ya fara ƙoƙarin wanke fiska. Sai daya gama wanke fiskan ya tabbatar baccin ya watse a idanunsa ya fara tunanin me ya kamata yayi. Bai yi sallan Asuba ba. Jiya daya dawo daga club kusan ƙarfe ɗaya na dare ya gota.
Bai yarda da kansa ba ko jiya yayi wanka a chan hotel ɗin ko bai yi ba dan haka ya kunna ruwa ya fara ƙoƙarin wanka.

Kafin ya fito Mom ɗinsa ta gyara masa  gado ta kashe kiɗan dake tashi ta fita. Kamar mai kokawa da agogo haka ya dinga komai a kakkauce, yai sallar Asuba cikin ƙasa da minti uku. Kafin kace me yai jefi da sallayar ya ƙarisa wajen closet ɗinsa yana neman kayan da zai saka. Tabbas idan Dad ya ga bai je aiki a wannan lokacin ba kashinsa ya bushe.

Ya fito da grey blazer da white shirt da light blue pants ya ajiye a kan gadonsa.

Cikin sauri ya fara shafa mayuka kala-kala a jikinsa. Fiskarsa kaɗai sai da ya shafa kala uku ya haɗa da sunscreen dan zafin Abuja ba zai bar shi ya fita babu suncreen ba. Fiskar sa yai kyau sai wani sheƙi yake kaman wani model.

A hankali ya fara saukowa daga matattakala yana ƙoƙarin ɗaura agogo a hannunsa.

Jemilah mai aikinsu itada Mom na ƙoƙarin jera abinci a dining.

Ashraf ya ƙariso ya rungumi Mom ɗinsa yana faɗin thank you. Tabbas ba dan ita ba da Dad ya iso ya same shi yana tsaka da barci.

Jin an buɗe gate shi da Mom suka wani kalli juna kaman wasu munafukai.

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Where stories live. Discover now