7

71 5 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

07



Wata shegiyar lingerie Zulfa ta saka. Tun da ta ga hotonsa a Instagram ta ƙiyasta a ranta yadda zai mata ɗas a jikinta. So take ta birkita Tahir kwana biyun nan maganar zama CEO ya rufe masa ido.

Ta kalli kanta a madubi. Gaskiya kayan sun ci kuɗinsu, babu wani lafiyayyen namiji da zai ga mace cikin wannan kaya da ba zai ji hankalinshi ya tashi ba.
Gata nan kamar wata strip dancer.

Dama tana da shape mai kyau shiyasa a kullum take ƙoƙarin tattalin wannan diri da Allah ya mata.
Saboda kada ta yi tumbi ta sakawa kanta yin diet na dole. Haka nan duk son jikinta sai da ta sawa kanta yin gym sau biyu a sati.

Namiji kamar Tahir sai da tattali.

Ta sani yana neman mata. Amma kwanciyar hankalinta shine Tahir ba zai taɓa kawo mata kishiya ba.

Za ta iya haƙuri da abinda bata gani ba amma duk ranan da Tahir ya kuskura ya auro wata tabbas mutuwar kasko za a yi.

Ta yi wani ƙayataccen murmushi lokacin da ta tabbatarwa kanta ta yi kyau sosai.

Ta saka doguwar robe ɗinta baƙi ta wuce ɗakin Tahir.

"Na ce miki zan zo ai ko. Kiyi haƙuri... Idan na zo ni zan bashi lafiyar ne..."

Yana ganin shigowar Zulfa Tahir ya juya harshensa zuwa yaren Fillanci.

Duk wani ɗoki da Zulfa ta shigo da shi ya gushe lokaci guda.
Wace 'yar iskar ce Tahir ɗinta ke bawa haƙuri.
Wace karuwar ce Tahir ke wa magana a hankali.

Shi da idan yana magana da ita a waya zaka ji yana yi da izza kamar zai doke ta.

Ta hawo kan gadonsa jikinta na rawa idanunta na shirin zubar da hawaye.

Ai da gayya ya juyar da harshe dan kawai kada ta ji abinda yake faɗa.

Baki na rawa ta fara magana lokacin da ya gama wayar.

"T T Tahir da wa kake magana?"

Wani kallo ya mata irin baki isa na baki amsa ɗin nan ba.

"Daddyn Tahlil da Inna kake waya ko?"

Abinda take ta faɗawa zuciyarta kenan saboda ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji a ƙirji.

"Bana son ƙwaƙƙwafi Zulfa. Ki kiyayi bakin ki"

Wani abu ne ya taho mata maƙoshi ya tokareta ya hanata magana.

Bai ko kalleta ba ya cigaba da danne dannen waya.

Gyara kwanciyarta tayi ko cire robe ɗin data saka bata yi ba balle har ta nunawa Tahir kayan data saka.

Shima bai waiwayeta ba ya cigaba da abinda yake a waya.

Chan ya kira wani a wajen aikinsu inda suka tattauna kan shirin da suke yi gobe.
A iya abinda ta fahimta. Tahir ya shirya mutanen da za su yiwa Dad bore matuƙar ya bawa Umar CEO ba shi ba.

Tabbas idan Dad bai bashi CEO ba zata sha gori a wajen Tahir. Ba gori kaɗai ba zata shiga ƙunci ne na lokaci mai tsawo.

Hawaye kaɗan kaɗan ke gangarowa gefen fuskarta.
Ba kukan abinda zai yiwa Dad take ba, tana kukan kishi ne. Kishin koma wacece Tahir yai waya da ita ɗazu.

A hankali bacci yai awun gaba da ita.
Gabannin Asuba ta ji ana taɓa mata ƙirji.
Kafin ta gama buɗe ido Tahir ya fara kunce robe ɗinta yana ƙoƙarin cire mata shi.
Ya ga kayan data saka amma bai ce komai ba. Babu wani reaction daga gare shi da zai nuna yama gane cewa sabon lingerie ta saka.

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang