9

88 13 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

09


Ƙaran fanka ne ƙiƙit ƙiƙit ya ƙaraɗe ɗakin Baba. Fankan iya gudunsa iya ƙaransa. Baba ya sha cewa za a gyara masa fankar amma har yanzu ba a gyara ba. Sai ma an kawo wuta marar ƙarfi zaka ji ka tsani fankan  saboda ƙiƙit-ƙiƙit-ƙiƙit.

Baba na zaune a bakin gado yayinda Zainab Qayyisah ke zaune a ƙasa.
Jiya ta dawo daga camp. Bata samu magana da Baba ba sai yanzu da ta kawo masa posting letter ɗinta. Ta kuma faɗa masa cewa ta haɗu da Khalifa ɗan Abban Abuja a camp har ma ya kaita wajen Abba sun gaisa.

"Baba idan ba ka so na yi service ɗin a chan zan nemi wanda zai chanja min"

Baba yai shiru yana nazarinta. Ya san halinta sarai. In har ta fara kame-kamen bata son abu to tana so kenan.

Wannan maganan wai zata nemi a chanja mata wajen service shaguɓe ne kawai. Tana son yin service ɗinta a chan.

Sai dai abu ɗaya ne ba zai lamunta ba. Ba zai bari ta yi kusa da Alhaji Sani Muƙaddas ba balle har ayi tunanin walaƙanta masa 'ya.

Yadda Allah ya rufa musu asiri a waɗannan shekaru yana so su cigaba da zaman rufin asiri ba tareda sun yi maula a wajen wasu ba.

Shi bashi da matsala da service ɗinta a Abuja, shi dai kawai ace ta zauna a gidan Kawunta ne ba zai lamunci hakan ba.

Yadda suka yi watsi da 'ya'yan marigayiya babu zumunci shekara da shekaru. Basu cancanci ya tura musu 'yarsa ta zauna da su ba.

"Zainab bana so ki zauna da Kawunki. Ba dan komai ba sai dan ina miki gudun gori da walaƙanci"

"Na sani Baba"

"Idan kamfanin da aka kaiki suna bada wajen zama to sai ki je idan kuma basa bayarwa sai ki haƙura da Abujan amma ba zaki zauna da Alhaji Sani ba"

Qayyisah ta ɗago kai tace zan tambayi Khalifa.

"Baba"

"Na'am"

Tayi shiru tana ƙara nazarin abinda zata faɗa.

"Zainab wani abu ne?"

"Dama...dama maganan kayan da aka aje a ɗakina ne. Ni inaga gara a sayar da su kawai a zuba kuɗin a shago"

"Zainab" ya kira sunanta a hankali.

"Na'am"

"Aure lokacine kin ji. Lokacin da Allah ya rubuta miki ne bai kai ba, idan ya kai zaki ga komai ya zo ya wuce cikin kwanciyar hankali da daɗin rai.

"Bana so ki sakawa ranki cewa dan Nura ya fasa aurenki shikenan ba zaki samu wani mijin ba. Tun ba yau nake faɗa miki wannan ba. Idan Allah ya nuna ƙudurarsa sai kiga kafin ki gama bautar ƙasa Allah ya kawo miki miji, ba abinda ya gagari Allah.

"Maganar da kika yi gaskiya ne, nima nayi tunanin yin haka. Gara a siyar miki da kayan a juya kuɗin. Idan lokaci ya zo sai a sake siyan wasu"

"Nagode Baba" ta faɗa tana jin wani relief a ranta dan ta ɗauka Baba zai yi faɗa.

Ta miƙe fiskarta ɗauke da murmushi ta wuce ɗaki.

Washegari wani dillali ya zo ya kwashe kayan. Duk wani cinikin kaya da Anty Fa'iza aka yi.

Ita kam Zainab tafi damuwa da a fitar da kayan sama da nawa za a  siyar da kayan.
Zaman kayan a ɗakinta a kullum tuni ne ga cewa saura kwanaki tara da aure Nura ya fasa aurenta.

A kullum kayan ke tuna mata irin wahalan da ta sha a soyayya.

Wani lokaci idan ta tuna wasu abubuwan da ta yi da sunan soyayya sai ta ga kamar ita kaɗai take soyayyan Nura ɗan rakiya ne.

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Where stories live. Discover now