3

102 9 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

03



Da Asuba kamar kullum Dad ne ya fara tashi daga bacci. Ya shiga banɗaki yai alwala ya fito. Yana fitowa ya ga Mom ta tashi zaune tana mammatsa wuyanta gashinta yayi buzu-buzu.

Tura kekensa yai zuwa gefen gado yai mata sallama.  Hannunsa ta kama ta kissing sannan ta gaida shi. Duk da dai kusan gaba ɗaya rayuwarta tayi shi ne a Nigeria, har yanzu akwai al'adunsu na Larabawan Lebanon da bata dena ba saboda ya riga ya bi mata jiki.

"Ki je ki taso Ashraf ya same ni a falo"

Kafin ya gama maganar ma  ta miƙe. Ta ɗauki robe ɗin rigan baccinta ta fita,  a staircase ta ƙarisa ɗaura robe ɗin yayinda take ƙoƙarin ɗaure dogon gashinta mai tsantsi.

A hankali ta buɗe ɗakin Ashraf ta shiga. Kamar kullum bata tsammanci zai tashi daga barci da wuri haka ba sai kuma ta ga gadonsa wayam ba kowa.

"Ashraf Dad ɗinka yana jiranka a ƙasa" ta furta da ɗan ƙarfi.

Har zata fita ta lura ba fa alamar motsi a banɗaki. Ta je bakin banɗakin ta ƙwanƙwasa.

"Ashraf" "Ashraf" amma shiru.

Ta gwada buɗe ƙofar banɗakin taji shi a buɗe.
Idanunta ta waro waje ganin Ashraf baya banɗakin.
To ina Ashraf ya shiga? ta tambayi kanta.

Tabbas bayan abinda ya faru jiya idan Dad ya gane Ashraf bai kwana a gida ba wani tashin hankalin za a kuma shiga yau a gidan nan.

Ta sauko ƙasa gwiwarta a sace ba tareda ta san ƙaryar da za ta faɗawa Dad ba.

Dad yana zaune a kekensa yana jan carbi duk da ba duka wutan falon aka kunna ba kana iya ganin baƙin carbin daya ke ja.

"Erm, Sayyidi, inaga Ashraf..."

Ɗaga mata hannu yai dan ya riga ya san kwanan zancen tunda ba yau Ashraf ke ƙin kwana a gida ba.

Ya ɗan juyar da kekensa yace " na tafi masallaci"

Mom ta zo da sauri ta buɗe masa ƙofa ya fita.
Yana fita ta sauke ajiyar zuciya. Tabbas idan Ashraf bai nutsu ba kwanan nan hawan jini ne zai kasheta. Ita kanta ta gaji da kare shi a wajen mahaifinsa.

Tana shiga ɗaki numbar wayarsa ta fara kira amma duka numbobinsa uku a kashe suke. Hatta special numbarsa da Dad bai san da shi ba ta kira amma switch off.

Ya Allah! Ta faɗa tana zama bakin gado.

Dad bai dawo daga masallaci ba sai ƙarfe shida da rabi.

Yana zuwa Mom ta haɗa masa ruwan zafi ta taimaka masa yai wanka. Lokacin da suka fito yace wa Mom a shirya masa abin karyawa da wuri zai je office.

Mom ta kalle shi cikin rashin fahimta. Baya zuwa office sai Monday na farkon wata da kuma Friday na ƙarshen wata. In dai yaje ba a waɗannan kwanaki ba to wata matsala ne ta taso ko kuma dai wani taro ne aka shirya na musamman.

Mutane uku ke da ragamar tafiyar masa da Kamfani. Ashraf, Umar da kuma Tahir mijin Zulfa.

"Akwai board meeting ne yau?" Ta tambaya cike da fargaban hasashen da take a zuciyarta.

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Where stories live. Discover now