2

127 10 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

02

Top-notch season 2

A hankali Zaynab Qayyisah ta sauke jakarta a kan centre table dake tsakiyar falon gidansu. Ƙirjinta ne yake mata ciwo. Meat pie da nutri milk da ta ci bai wadace ta ba, ga shi tun ba a je ko ina ba ta fara jin heartburn.

Daga ta kicthen ta fara jiyo sizzling na kifin da Anty ke soyawa. A gajiye ta wuce kitchen ɗin ta gaida Antyn dake ta faman soya kifin sukumbiya da za a yi miyar dare da shi.

"Anty ba a aiko min abinci ba" Qayyisah ta faɗa tana kallon kular abincinta dake kife cikin kwandon kwanuka.

"Ba a aiko miki abinci ba ko kuma ƙaninki bai kai miki abinci ba"

"Anty ko Aliyu baya nan ba za a aiko Sagir ya hawo keke ya kawo ba"

"sannu Princess. Sagir zaman ki yake ai da ba zai je Islamiyya ba"

Qayyisah ta girgiza kai ta fice daga kitchen ɗin. Allah ya jiƙan rai kawai, ba dan rasuwan mahaifiyarsu ba mai zai sa Baba ya auro wata gidan nan.

Ba abinda ke ɓatawa Qayyisah rai irin yadda matar nan tazo lokacin da lamurra suka daidaitu musu amma kuma take ƙoƙarin hana su jin daɗi a gidan ubansu. Da ace lokacin da suke kokuwa da talauci da matsin rayuwa tazo tabbas guduwa zata yi.

Qayyisah ta shiga ɗakinta. Kayan dake cure gefe guda da aka rufe da ƙaton mayafi ta fara tozali da shi. Kayan ke tuna mata cewa ita ɗin Amarya marar Ango ce ko kuma dai Amaryar mafarki.

Da gayya Anty ta sa aka maida mata kayan ɗakinta domin ta rinƙa ganinsu tana jin baƙin ciki.

Ranar wani yammaci irin na yau kawai ta shigo ɗakinta taci karo da tarin kayan an barbazazu har kan gadonta.
Data fito ta tambayi dalili Anty tace mata ta gaji da ajiyar gaibu ne. Wai kayan sun cika mata ɗaki.
Amma hakan bai sa lokaci zuwa lokaci ta dinga shigowa tana zaran kayan ɗaya bayan ɗaya ba.

Kwanaki da za a yi bikin 'yar yayanta haka ta shigo ta kwashi kulolin abinci masu kyau ta yi gaba da su wai bata da kuɗi zata bawa Basma gudummawa idan ta samu kuɗi zata maida mata. A haka dai kullum kayan ke ɗaiɗaicewa.

Duk abinda ya fita daga ɗakin ya fita kenan abinda Qayyisah ta sawa ranta kenan. Sai da kayan suka yi kusan sati biyu a ɗakinta kafin Baba ya san da zamansu a ɗakin. Yai wa Anty faɗa sosai yace Zaidu da Aliyu su kwashe kayan su kai ɗakinsa. Qayyisah da ta ji haka tace a bar kayan a ɗakinta. Baba ya ƙi da farko daga baya data dinga yi masa magiya haka ya haƙura aka barsu a wajen.

Abinda Nura ya mata ya isa kaɗai ya sa ta give up da rayuwar jin daɗi amma kuma ba zata bari wani namiji ya mata katanga da farin cikinta ba.

Sai da aka ɗau tsawon lokaci kafin ta warware daga kisan Humairah. Ba zata sake shiga yanayin ƙunci irin na shekarun baya ba. Ba zata shiga ƙunci  saboda wani Nura daya zaɓi yai walagigi da zuciyarta ba.

Banɗaki ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta saka shirt ɗin Zaidu wanda ya kai mata har gwiwa, ta saka dogon wando ta fito ta shiga kitchen. Ta duba ko'ina babu abincin ta na rana da aka ajiye.

"Anty ina abinci na?"

"Na ɗauka ai keda abinci sai dare. Ɗazu nasa aka juyewa Almajiri"

Qayyisah tayi ƙasaƙe tana kallon matar nan. Shekara uku kenan fa da aurota amma zaka ɗauka da ita aka sha baƙar wahala har aka tada arziƙin da take gadara da shi.

"Look Anty Fa'iza. Wannan ne na ƙarshe da zaki min irin haka. Na lura duk lokacin da Baba baya nan kike fito da salon munafurci dan ki muzguna min. Ni ba kishiyar ki bace baki isa ki nuna min isa da iko a gidan Ubana ba"

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Where stories live. Discover now