5

91 7 1
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

05

Mom na kitchen tana haɗa special lunch wa Ashraf Jemilah ta shigo.
Tana saukowa daga sama ta haɗu da Zulfa tsaye a tsakiyan falo tana waya.

Bata ma gaida Zulfan ba ta wuco kitchen dan ta kai rahoto.
Kusan shekaran Jemilah goma tana aiki a gidan dan haka ta san irin zamantakewar dake tsakanin Mom da 'ya'yanta.

Lokacin da ta fara aiki babbar 'yar Mom wato Su'ad tayi aure ita da mijinta suna Germany. Sai a bikin Zulfa ne ma ta fara haɗuwa da ita.

Kusan zata ce akwai shaƙuwa sosai tsakanin Su'ad da iyayenta musamman ma Dad.

Duk cikin yaran ita kaɗai ne zaka ga idan tana tareda Dad suna hira sosai irin na Uba da 'ya,  har ka ga Dad yana sheƙa dariya.

Tana da faran-faran da mutane, bata da rena na ƙasa da ita.
Ko aikan Jemilah za ta yi sai ta haɗa da 'please'.

Yaranta uku biyu mata ɗaya namiji. Idan ka ganta zaka iya rantsewa bata jima da aure ba. Tana kama da Mom sosai, kawai tsayi ta fi Mom, sai kuma ita bata da jikin Mom ɗin.

Jemilah tana gidan aka yi auren Zulfa. Lokacin bata cika shekara ɗaya a gidan ba.
Abinda ta lura tun a lokacin shine Mom da sauran 'yan'uwanta basa son auren Zulfa da Tahir.

Hajiya Halima da Mom haka suke sakata a gaba akan ta haƙura da Tahir. Amma sam ta ƙi.

Ba dan Dad ya taka musu birki ba da babu yadda za a yi auren ya yiwu.

Tunda aka yi auren kuwa kusan zaka iya cewa ta ja jikinta ne daga iyayenta.

Ga shi dai iyayenta a Abuja su ke, minti ishirin zai iya kawota gidansu daga gidanta amma sai ta doshi wata shida bata leƙo gidan ba.

Asali ma lokacin sallah kawai take zuwa  ta gaishe su sama-sama ta tafi.

Idan kaga ta zo ba a sallah ba to wani abu ne ya taso aka kirata ko kuma Su'ad ta shigo ƙasar zata zo su gaisa.

Daga bakin Su'ad ɗinne ma take jin wai Tahir ɗinne ya ke hana Zulfa zuwa gida.

Itama Mom ɗin da ta kan ɗan je gidan Zulfa, amma tun wani lokaci da ta je ta gidan duba ɗanta Tahlil da ba lafiya bata sake zuwa ba.

Kusan watanni goma kenan.

Jemilah ta san wani abu ya faru a gidan amma har yau bata gano menene ba.
Bata tunanin ko Hajiya Halima Mom ta faɗawa. Balle dama Dad kam ba komai ta ke faɗa masa ba tunda ta san halinsa baya son ƙananun maganganu.

Idan bata manta ba ranan ɗin Mom ko abinci bata ci ba tun da ta dawo har washegari.  Ta wuni a ɗaki wai bata jin daɗi.

Koma menene dai ya faru tsakanin 'ya da uwa a lokacin to yanzu kam basa ga maciji.

Rabon Zulfa a gidansu tun sallar layya da suka zo da mijinta gaishe da Dad.

Kafin ta gama bawa Mom rahoto Zulfa ta ƙwala mata kira.

"Jemilah!"

Jemilah ta kalli Mom tana jiran umurni.

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang