8

78 6 0
                                    

ASHRAF: Beauty meets Ugly

08



Yau za a fita a camp. Kowanni ɗan bautan ƙasa ya sha ado cikin 6/7  na kayansu.
Qayyisah dai bata cikin 'yan fareti dan tun ranan farko da ta ji wahala ta gudu ta koma team ɗin 'yan Red cross.

Tana tsaye tana ɗagawa 'yan Platoon ɗinsu hannu dan ba ƙarya sun burge sosai. Ko cikin competitions da aka yi Platoon ɗinsu ta samu kyaututtuka da yawa.

Yau zasu bar camp. Kowa zai karɓi posting letter ɗinsa ya kai ma'aikatar da aka tura shi.

Tuni sun haɗa tafiyarsu da Paul da Lisa da kuma Ramlah, suma 'yan Jos ne da suka haɗu a cikin camp ɗin.

Ba a ƙare parade ba sai kusan ƙarfe shabiyu na rana.

Ana gamawa kuma aka fara rabon posting letter.

Khalifa ne ya fara karɓan nasa. Dama ya sani kamfanin Abba za a tura shi.  Koda ba nan aka tura shi bama dole nan ɗin zai koma.

"Kai! Har yanzu ba a kira sunana ba"

"Ke kam ai ƙauye za a tura ki"

"Mugu saboda kai ka samu naka ko"

"Primary school za a kai ki kiyi ta fama da ABCD"

"Ba ABCD ba carmandudu zan musu"

Khalifa ya fashe da dariya.

Suna tsaye aka kira sunan Paul Ishaleku.  Shi kam hankalinsa na kan Qayyisah ko sunansa bai ji ba. Qayyisah ce ta yi ɗagyalgyal ta karɓi letter ɗin tana dubawa.

Khalifa ya wafce letter ɗin ya miƙawa Paul yana faɗin "ke zaki faɗa masa inda aka tura shi ne. Ki bar shi ya karanta kayansa"

Paul ya karɓa idonsa na wiki-wiki lokacin da yake karanta takardar.

"Paul Ina aka tura ka?"

"Qayyis ki fita harkansa Dan Allah"

Shifa Khalifa tun farkon haɗuwarsu yake ƙoƙarin raba ta da Paul. Ya sha gaya mata cewa baya son alaƙarta da shi wai ta dena yawo da shi.

A gabanta yai wa  Paul warning akan  ya dena kula ƙanwarsa.
Paul ya ce bai isa ba.
Ita Zainab abin ma dariya yake bata. Idan suna gayawa junansu baƙar magana.

Kafin ta karɓi letter a hannun Paul aka kira sunanta.  Aminu Zainab Qayyisah.

"Yes" ta faɗa da ƙarfi.

Khalifa ya karɓi letter ɗin saboda ya fita tsayi.

Bari muga ina aka tura ki.

"Khalifa ka bani abuna bana son gulma"

Yai dariya yace "Kuhuhu Village Primary School aka tura ki fa"

Ta fizgi letter har sai da ƙasan ya yage.

"Kaga abinda ka jawo ko"

ASHRAF -Beauty meets Ugly (Hausa Romance Novel)Where stories live. Discover now