Chapter 2

40 0 0
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)



*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )


*TASKIRA WRITER'S FORUM*
              ( *T.W.F* )

*Saurin me kike y'ar uwa! Ina za ki! Matso kusa domin a yi tafiyar dake,karki wuce ba tare da kin yi following  d'aya daga cikin links ďin da suke a k'asa ,kiyi following link ďin da yayi miki don cigaba da karanta k'ayataccen littafina mai suna BANI DA MADOGARA  (Sai Allah...),hmmm ba a magana idan ana sallah don sai kin karanta za ki tabbatar kuma za ki shaida had'uwarsa , sannan za ku iya samun littafina na farko mai suna NACINA YA JAWO MIN a kowani link daga cikin huďun nan.Asha karatu lafiya, ta ku har kullum NARRNARHH BUKAR ( *The Amazing Pen ✍️* ). *laaah!  Na manta kuyi following ďina ta wa'innan links d'in below don samun ci gaba da karanta littafina, Ina maraba lale marhabin da zuwanku*

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*BOOK* 1⃣

*Chapter 02*

Daram!!! Dam!!! Dadammmmmm! !! Haka k'irjin Hujayrah ta bada,fashewa tayi da matsanancin  kuka mai ratsa k'ashi da b'argon duk wani mai sauraronta, cikin kuka ta fara magana da  cewa

"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Na shiga uku na lalace  ni Hujayrah  yanzu a rasa wanda za a had'ani dashi sai da wanda ya haifeni kuma mugu"

Daka mata wata uwar tsawa Alhaji Zakari yayi domin yaga alama tana da niyyar b'ata masa plans,cikin kakkausar muryar ya fara magana

"Me kike nufi da tsoho ne, waya ce miki tsoho bai auran galleliyar budurwa sabuwa fil a kwali,mun ce ki kawo wanda kike so ki aura kin ce mana babu, to ya kike so muyi, zuba miki idanu kike so muyi har ki tsufan mana a gida tunda baki da niyyar fidda miji kiyi aure ko kuwa, duk sa'anninki sunyi aure har da yaransu, k'annanki ma haka yanzu suna d'akin mazajensu, a garin nan ban tunanin akwai wacca take da shekaru irin naki wacca batayi aure ba"

"Babu gaskiya" cewar Baba Zubairu wanda sai yanzu ya tofa albarkacin bakinsa

Kakulle ce ta ce

"D'an Inna tunda Hujayrah ta nuna b'ata son auran nan, a k'yaleta kawai,shi aure lokaci ne inda rai da rabo ita ma za ta yi auran kamar sauran y'an uwanta"

"Haba Inna so kike ta dawwama a gida duk sauran y'an uwanta sunyi aure sannan mutanan gari suyi ta gulmarmu , a gaskiya Ina bayan Zakari d'ari bisa d'ari,sai naga a zamanin da can aure ake ma mace ba tare da tasan mijinta ba,kuma ta zauna dashi  lafiya har Allah ya basu haihuwa" cewar Attine k'anwansu wacca take bi ma Baba Musa

Abbu dai shiru yayi domin an zo gab'ar da baisan abinda zai iya  furtawa ba saboda ba gani yake ba balle ya tantance mai kyau ko marar kyau, ganin Alhaji Zakari shi ne babba a d'akinsu sannan shi ya kawo shawarar, hakan yasa bazai yi jayayya dashi a wannan al'amari ba,don kuwa ya yarda dashi a matsayinsa na  d'an uwansa na jini uwa d'aya uba d'aya yasan bazai tab'a zab'arma y'arsa mutumin banza ba ko kuma tumin dare .Mammi abin duniya ya gama dame mata, ta ma rasa abin cewa sai dai kallon yadda Hujayrah take ta faman dirzar kuka mai sauti, gwanin ban tausayi.

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now