Chapter 15

57 2 8
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*












   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)


*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )

*TASKIRA WRITER'S FORUM*
              ( *T.W.F* )

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link

*TALLA!  TALLA! TALLA!*

*Ina kuke masoya💋mutanan arziƙi💃masu ordering snacks da abincin biki 🤭🤭🤭, wani lokacin ku yi ta samun matsala wurin kawo muku ko kuma abinci mai muku ba. To ku sha kurumunku domin nesa ta zo kusa 👉 H.D DELICACY za ta biya muku buƙatunku cikin sauƙi da rahusa ga kuma shegen daɗi kamar kunuwanku za su tsinke🤭. Shin kina buƙatar snacks masu daɗi da sauƙi  ko kuma kina da biki wanda kike so ayi miki abinci sannan a kawo miki har gidanki hankali kwance 💃💃💃Hmmmm ƴar uwa me kike jira ne maza garzayo H.D DELICACY💃💃💃.Muna ordering snacks Kamar haka:*
*Bugger*
*Shawarma*
*Pizza*
*Cincin na amare*
*Spring roll*
*Ceremonial service etc...*
*Kar ku manta a duk inda kuke a faɗin Nigeria zamu je gareku. Domin aikinmu ne mu faranta muku rai ta hanyar kawo muku snacks ɗinmu da ceremonial service masu matuƙar daɗi. Takenmu shi ne DUK WANDA YA CI SAI YA ƘARA.*
*Domin ƙarin bayani sai ku tuntuɓi waɗannan lambobin a ƙasa*
08081930789
07061895039



*BOOK* 1⃣
*chapter 15*

Wata uwar tsawa ya daka mata lokaci guda suka razana, Zaliha tuni ta saki fitsarin da take riƙewa tana ƙanƙame Murja saboda tsoro. Cin amon muryarsa mai cike da ƙaraji ya ci gaba da cewa

"Ƙarya zamu yi miki!!! Kece farkon wacca ta fara rusa mana shiriii!!! A sanadiyyarki wasunmu sun zama guragu saboda azabaaaa!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Ita da ahalinta sunfi ƙarfinmuuuu!!! Dole ne mu ɗauki fansarmu akan babban ɗanki wanda yake hannun yayan mahaifiyarkiii!!! "

Da  sauri Murja ta ɗago da kanta, gabanta sai dukan uku-uku yake.Hannunta ta saka a kai ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin

" Wayyo Allah ni Murjaaa!!! Na... "

Wata uwar tsawa ya sake daka mata yana faɗin

" Kun san da Allah kuka zo wurinmuuu!!! Makiraa mai fuska biyu!!! Ai muna sane da makircin da kike ƙullawa munfukaa!!! Ku tashi kubar min gidaaa tun kafin fushina ya sauka a kanku"

Babu shiri su Murja suka miƙe, rige-rige suka shiga yi wurin fita daga ɗakin, har Zaliha na bigewa a ƙafarta, ta ji zafi sosai amma bata tsaya dubawa ba sai da suka bar gidan tare da yin nisa sosai sannan suka samu wuri suka zauna. Sai a sannan ne Murja ta fashe da matsanancin kuka, Zaliha ƙafarta ta duba d saboda zafin da take mata, ƙila idan sun koma gida sai ta je wurin mai ɗaurin ya duba mata ƙafar ko ta yi targaɗe. Bata damu da kukan da Murja take dirza ba hasalima daɗi ta ji a ranta tana mata Allah ya ƙara. Murja kuwa sai da ta yi kuka ma'ishinta sannan ta tsagaita tana duba Zaliha ta ce

"Yanzu Zaliha ko jimami tare da bani haƙuri ba ki yi ba bayan kin ji da kunnuwanki abin da boka ya ce asirin zai koma akan Jabiru, amma baki damu ba kamar ba ƴar uwarki ba"

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now