Chapter 13

59 2 6
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*







   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)


*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )

*TASKIRA WRITER'S FORUM*
              ( *T.W.F* )

Domin ci gaba da karanta ƙayataccen littafina sai kuyi following ɗina a ɗaya daga cikin wa'innan links ɗin, da littafina na farko mai suna NACINA YA JAWO MIN, Ina maraba lale marhabin da zuwanku,taku har kullum NARRNARHH BUKAR mai alƙalamin ban mamaki wato THE AMAZING PEN✍️*

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link

*BOOK* 1⃣
*chapter 13*

Zaune yake yana wannan tunanin ya ji wayarsa na ringing da sauri ya ɗauki wayar a tunaninsa ko Alhaji Sambo Dala ne ya kira sa don ya shaida masa  ya ganta amma ina sai yaga akasin haka, sunan *MATI* ke yawo a screen ɗin wayarsa nan take jikinsa ya ƙara sanyi hankalinsa ya ƙara tashi, jiki baɓu ƙwari ya ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnansa ba tare da ya ce komai ba. A can Murja ta ce

"Assalamualaikum Alhaji Zakari mai Nairori, kasan hausawa sun ce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, to yau ce ranar, Ina jiranka a inda muka saba haɗuwa"

Ƙit! Ta katse kiran, shiru ya yi ba tare da ya cire wayan daga kunnansa ba, a ransa yana faɗin 'O ni Zakari naga ta kaina, gaba kura baya damisa ban san ina zan saka raina na ji daɗi ba, wacca take saka ni farin ciki yanzu ta canja gaba baki ɗaya, ni yanzuuu ya zan yi da Alhaji Sambo Dala da ya bijiromin da wani sabon tashin hankalin da ban san hawa ba balle sauka, to niii me zan ce ma Murja idan na je wurinta, Mts! Kawai dai don babu yadda zan yi ne zan auri ƙanwarta amma idan da ba haka ba wallahi bazan ƙara wani auran ba, don a gaskiya ban san me zan ce ma Hannatu ba wannan cin amanar da zan yi mata, wayyo ni! haka ya ci gaba da zancen zucinsa daga bisani ya miƙe ya zira mukullin mashin ɗinsa ya nufa kwarin ɗan dodo.

Cikin rabin awa ya isa Kwarin ɗan dodo inda ya samu Murja a daidai inda suke haɗuwa, kamar kodayaushe tana sanye cikin dogon hijab da niƙab tana kalle-kalle. Faka mashin ɗinsa ya yi sannan ya nufa inda take, Murja tunda ta ga ya faka mashin ɗinsa take sakin murmushi a cikin niƙaf ɗinta a ranta tana cewa 'Ka gama kumbura-kumburanka za ka dawo kan hanya ne, da Murja ka ke zancan'  Har inda take ya tako ya tsaya ba tare da ya ce komai ba. Wani ƙasaitaccan murmushi mai sauti ta saki sannan ta ce

"Kai tsaye ba tare da wani ɓata lokaci ba ka sanar min da abin da ka shawarta, shin ka amince za ka auri Zaliha ko kuwa baka amince ba"

Shiru bai tanka mata ba yana tsaye yana kallonta, ya harɗe hannunsa yana taɓa ƙasumbarsa. Kamar ba zai ce komai ba sai can ya fara magana cike da ɓacin rai

"Murja zan amince da auran nan ba don ina so ba, sai don kar ki tona min asiri ne, amma ki sani ina da nawa sharaɗin"

Gyara tsayuwa Murja ta yi sannan ta dubesa ta ce

"Sharaɗi! Sharaɗi kuma? To ina sauraronka "

"Sharaɗin ba komai bane illa idan na auri Zaliha za ki goge waɗannan bideos da yake wurinki, idan baki yarda da wannan Sharaɗin ba to a gaskiya ba zan iya auran ƙanwarki ba"

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now