*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*🌍BANI DA MADOGARA🌍*
(Sai Allah.......)*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )*TASKIRA WRITER'S FORUM*
( *T.W.F* )*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link*TALLA! TALLA! TALLA!*
*Ina kuke masoya💋mutanan arziƙi💃masu ordering snacks da abincin biki 🤭🤭🤭, wani lokacin ku yi ta samun matsala wurin kawo muku ko kuma abinci mai muku ba. To ku sha kurumunku domin nesa ta zo kusa 👉 H.D DELICACY za ta biya muku buƙatunku cikin sauƙi da rahusa ga kuma shegen daɗi kamar kunuwanku za su tsinke🤭. Shin kina buƙatar snacks masu daɗi da sauƙi ko kuma kina da biki wanda kike so ayi miki abinci sannan a kawo miki har gidanki hankali kwance 💃💃💃Hmmmm ƴar uwa me kike jira ne maza garzayo H.D DELICACY💃💃💃.Muna ordering snacks Kamar haka:*
*Bugger*
*Shawarma*
*Pizza*
*Cincin na amare*
*Spring roll*
*Ceremonial service etc...*
*Kar ku manta a duk inda kuke a faɗin Nigeria zamu je gareku. Domin aikinmu ne mu faranta muku rai ta hanyar kawo muku snacks ɗinmu da ceremonial service masu matuƙar daɗi. Takenmu shi ne DUK WANDA YA CI SAI YA ƘARA.*
*Domin ƙarin bayani sai ku tuntuɓi waɗannan lambobin a ƙasa*
08081930789
07061895039*Wannan chapter sadaukarwa ce agareku my aminiyar arziƙi ɗaya tamkar dubu Surayya Abdullahi💋💋,da kuma Kakata Hajiya Habiba Abubakar dattijuwa mai ran ƙarfe, Allah ya ƙara miki nisan kwana tare da lafiya mai amfani sannan Allah ya baku lafiya yasa kaffara ne agareku.🤲🤲🤲*
*BOOK* 1⃣
*chapter 14*Ɗan murmushi wanda bai faɗaɗa ba ya yi yana jinjina mata kai, da yake tasan halinsa yasa bata damu ba,Alhaji ma rungumesa ya yi yana farin ciki, Mas'ud da Mahmoud suka gaisa. Tahseen da saurinta za ta rungume Arqam sai ya ja da baya yana faɗin
"Don't even dare try that illetracy here!"
Tahseen ce kaɗai ta ji maganar saboda bada ƙarfi ya yi ba, Allah yasa lokacin da ta zo rungumesa Alhaji da Hajiya Nafisa hankalinsu baya wurin.Gwalo Fauziyya ta yi mata tare da manna mata ido ɗaya har da kwaso *SHOKI* duk don ta ɓata mata rai. Ai kuwa ta yi nasara domin ta ƙulu iya ƙuluwa don bata yi zaton Arqam zai hanata rungumesa ba, ita a tunaninta asirin da aka yi ma Hajiya momma zai shafi Arqam ɗin, shi yasa ta yi haka amma gashi an samu akasi ya jizgata a gabansu Fauziyya. Wani malolon baƙin ciki ne ta haɗiye, a ranta tana faɗin 'Ka gama izzarka da mulki za ka dawo tafin hannuna ne, sai na juyaka kamar waina a cikin tanada Mts!' juyawa ta yi ta bar wurin zuwa wurin motocinsu. Sai daga baya suka shiga motocinsu sai suka ɗauki hanyar gida.
A can gidan bayan Hujayrah ta sha magani, sai ta kwanta wanda ko mintuna talatin basu cika ba ta ta shi daga kwanciyar ganin marar nata ta ɗan rage mata ciwo.Kai tsaye ta wuce bayi ta yi brush da wanka sannan ta fito. Shiryawa ta yi cikin doguwar rigar abaya mai kalar ruwan madara,ta sha adon stones sai walwali suke. Bayan ta shirya tsaf! Sai ta fito zuwa falon Hajiya momma da sallama a bisa laɓanta ta shiga ciki, babu kowa a falon sai ta samu kujera mai cin mutum ɗaya ta zauna. Ba ta fi mintuna goma da zama ba sai ga sallamar Hajiyan Sama ta ci kwalliya cikin lace mai adon stones, irin ɗaurin A'isha Buhari ta yi. Amsa mata sallamar Hujayrah ta yi ba tare da ta kalleta ba. Wani uban tsaki Hajiyan sama ta ja tana cillama Hujayrah harara kamar idanunta za su fito, Hujayrah ba tare da ta kalleta ba ta saki wani kasalallan murmushi ta ce
YOU ARE READING
🌍BANI DA MADOGARA🌍
General FictionHujayrah ta kasance yarinya wacca ta fita zakka a gidansu domin a duk familinsu babu baƙi sai ita,dalilin baƙinta da kuma yanayin idanunta tare da baiwsr da Allah ya mata yasa kowa ya tsane,kowa baya sonta,tana fuskantar ƙalubale sosai,ga ƴan secret...