Chapter 17

56 3 3
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*







   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)


*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )

*TASKIRA WRITER'S FORUM*
              ( *T.W.F* )

*Marubuciyyar:*
* NACINA YA JAWO MIN*
               *and*
*BANI DA MADOGARA*
      (Sai Allah... )

*Kar ku manta da following ɗina ta link ɗin da ya yi muku don ci gaba da karanta littafina, kar ku bari a baku labari* 💋💋💋👇👇👇

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link

*BOOK* 1⃣
*chapter 17*

Da matuƙar ƙarfi ƙirjinsa ya bada sautin Dummmmmm! Cike da tashin hankali wanda ke bayyane a fuskarsa ya ɗago da sauri yana duban Hajiya momma, a sanyaye ya ce

"Ammie da mara hankali da kamun kai za ku haɗa ni aure?"

"Wa ya ce maka Tahseen bata da hankali da kamun kai, yarinya mai natsuwa ga sanin ya kamata ka aibata ta" cewar Hajiya momma fuskarta a ɗaure

Kallon Ammiensa yake baya ko ƙyafta ido, ya yi matuƙar mamakinta a ce wacca ta tsana a baya ko sunan Tahseen bata son jin balle uwa-uba maganar auransa da ita. Ko a da can lokacin da ya dawo bautar ƙasa Nijeriya Abba ya so a haɗasu aure da Tahseen tunda tana masifar sonsa amma Ammie ta yi ruwa ta yi tsaki ta hana auran a cewarta ba za ta haɗa jini da mara hankali da natsuwa ba, me ya shiga ran Ammie da ta canja ra'ayinta lokaci guda. What's going on? Anya babu wata a ƙasa kuwa? Sake kallon Ammiensa ya yi fuskarsa a kwaɓe ya ce

"Ammie please give me time to find  the choice of my life"

Ɗaure fuska ta yi tana kallonsa ta ce

"Ka ga duk wani suki-burutsinka ba zai taɓa saka wa mu canja ra'ayinmu akan auranka da Tahseen ba, ka tashi ina so na yi magana da Abbanka"

A sanyaye ya juya ya kalli Abba ya ce

"Abba yanzu kaima ka aminta na auri mahaukaciya ta haifamin yara taɓabɓu marasa hankali da natsuwa?"

Duk maganar da ake yi tun ɗazu Abba yana latsa wayarsa bai tanka musu ba, sai yanzu ya ɗago jin Arqam ya kira shi, ɗan murmushi ya yi sannan ya ce

"Arqam me kake so na ce? You mean I should go against the marriage, Kar ka manta da Ramla da ni ubanmu ɗaya, tana a matsayin ƙanwata ce kamar Nafisa. Tahseen tana a matsayin ɗiyar gareni, taya zan ƙi auranku Arqam, Ammm! Ban hana ka nemo w wacca kake so ba za a iya aura mata biyu a rana ɗaya wannan ba laifi ba ne, kai huɗu ka ce za ka aura  bamu da damuwa tunda kana da halin ciyar dasu. Amma maganar wai a fasa auranka da Tahseen bata ma taso ba, daman a baya mahaifiyarka ce taso hana faruwar hakan amma yanzu kuma ta amince, Ni kasan tun farko ina son auran sosai. Arqam! "

Kasalallun idanunsa ya ɗago wanda sun canja kala saboda ɓacin rai ya dubi Alhaji ba tare da ya ce komai ba. Alhaji bai damu da yanayinsa ya ci gaba da cewa

"Ka yi haƙuri da zaɓinmu a yanzu, idan anyi auran za ka iya daga baya ka auri wacca kake so, yanzu ka tashi ka tafi mun sallameka"

Ba tare da ya ce komai ba yabar ɗakin Melonsa na biye da shi, komai baya masa daɗi ji yake kamar ya kwarma ihu don haushi, shi ba wai baya son bin umarninsu ba ne sai dai wacca suke son haɗa shi da ita baya ƙaunarta saboda babu abin da bai sani akan sharholiyar da ta yi a makaranta ba har ta night clubs ɗin da take zuwa duk ya sani, taya zai zaɓar ma yaransa irin wannan uwar. Sosai lissafinsa ya gama kwancewa ya rasa meke masa daɗi a rai. Kai tsaye ya wuce part ɗinsa saboda kansa yana sara masa, Before, jugging ya so yi amma ya fasa zuwa zai kawai wuce ya kwanta ko kansa zai rage yi masa ciwo.

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now