Chapter 3

39 0 0
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*










   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
              (Sai Allah...)




*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )



*TASKIRA WRITER'S FORUM*
              ( *T.W.F* )


*Domin ci gaba da karanta ƙayataccen littafina sai kuyi following ɗina a ɗaya daga cikin wa'innan links ɗin, Ina maraba lale marhabin da zuwanku,taku har kullum NARRNARHH BUKAR mai alƙalamin ban mamaki wato THE AMAZING PEN✍️*


*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk


*Ina godiya sosai a gareku my Esteem fans and followers da ɗumbin addu'o'inku, Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci mai ɗorewa,sauƙi ya samu Alhamdulillah to! zamu ci gaba da gashi suya sai ranar sallah💃💃💃💕💕💕❤️❤️💋💋💋*


*BOOK* 1⃣

*Chapter 03*

Hujayrah dai tana a kwance ba ta yi bacci ba tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa wannan bala'in da ya ke shirin tunkarota.Sama-sama take d'an jin kamar ana maganganu,sai a hankula ta mik'e zuwa k'ofar bedroom d'in Allah yasa a lokacin da za su fita basu kulle k'ofar ba sai ta fito zuwa inda take jin kamar ana magana, wani bedroom ne wanda yake kallon nata bedroom sai ta je kusa da ƙofar bedroom ɗin  tare da kai kunnanta daidai inda za ta ji maganar  da kyau,ai kuwa rad'au take jin magaganunsu, natsuwa tayi da kyau don sauraron mai suke tattaunawa a kai, ai da wani irin ƙarfi k'irjinta ya bada Ras! Ras! Rarassssss! ,lokaci guda ƙwaƙwalwarta ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni, komai na duniyar ya koma mata bibbiyu, waro dara-daran idanunta tayi waje tare da rufe bakinta kar tayi ihu su jiyota, a zuciyarta tana cewa' Ni Hujayrah na shiga uku na lalace daman Baba Zakari sai da ni yayi ga wa'innan azzalumin, Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!' sosai jikinta ya fara rawa kamar ɗan mazari, domin kuwa hirarsu ta yi mugun tayar mata da hankali tare da rikirkita mata lissafi.

Alhaji Sambo Dala da abokinsa ne suke tattaunawa a game da batun Hujayrah wanda basu san da wanzuwanta a ƙofarsu ba, abokin Alhaji Sambo Dala ne ya gyara zamansa yana cewa

"Mutumina a gaskiya kai namijin duniya ne,kayi matuƙar ƙoƙari wurin binciko wannan yarinyar, dole Demon king ya ƙara maka matsayi"

Dariya sosai Alhaji Sambo Dala yayi sannan ya ce

"Yoo Senata wa ya ke wasa da ɗaukaka, ai bari ka ji duk inda nasan ɗaukaka ta ke to ina wurin, wai ka manta shekaru kusan ashirin da suka wuce mai girma Demon king ya ce an haiho yarinyar da ɗaukakarmu ke ƙarƙashinta, idanunta da zuciyarta su ne mahaɗar da  ta rage mana mu ɗaukaka har mu wuce tunanin mai tunani"

Jinjina kai Senata yayi tare da cewa
"Tabbas haka ya faɗa Demon king, kenan tun daga ranar ga bazama nemanta "

"Eh tun daga ranar na baza idanuna a duk faɗin Nijeriya nan, birni da ƙauye, lungu da saƙo har da kusufa-kusufa na bi,na baza yarana a duk faɗin Nijeriya har da wajenta,duk da mun daɗe muna neman yarinyar nan kasan sai a wani ƙauye a jihar Kaduna mai suna *KWANAR KWARA ƘWAI* a nan wani yarona da na sakashi aiki a ta ɓangaren ya nemota, ni da kaina na je garin don tabbatarwa, sai kuwa ilai ita ce, mai kalar idanun da Demon king ya suffanta haka idanunta suke exactly, ita a lokacin batafi shekara 12 a duniya ba, sai na haɗa baki da yayan babanta mai shegen son kuɗi, kasan shegiya Nairi, ai baiyi wata-wata ba ya yarda da ƙudirina akan yarinyar,idan baka manta ba Demon king ya ce sai yarinyar takai shekera 23 sannan Za a cire idanunta da zuciyarta don ƙarashe aikin da muka ɗauko na shekaru aru-aru"

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now