*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*🌍BANI DA MADOGARA🌍*
(Sai Allah.......)*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )*TASKIRA WRITER'S FORUM*
( *T.W.F* )*Saurin me kike y'ar uwa! Ina za ki! Matso kusa domin a yi tafiyar dake,karki wuce ba tare da kin yi following d'aya daga cikin links ďin da suke a k'asa ,kiyi following link ďin da yayi miki don cigaba da karanta k'ayataccen littafina mai suna BANI DA MADOGARA (Sai Allah...),hmmm ba a magana idan ana sallah don sai kin karanta za ki tabbatar kuma za ki shaida had'uwarsa , sannan za ku iya samun littafina na farko mai suna NACINA YA JAWO MIN a kowani link daga cikin huďun nan.Asha karatu lafiya, ta ku har kullum NARRNARHH BUKAR ( *The Amazing Pen ✍️* ). *laaah! Na manta kuyi following ďina ta wa'innan links d'in below don samun ci gaba da karanta littafina, Ina maraba lale marhabin da zuwanku*
*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link*BOOK* 1⃣
*chapter 07*Kamar kullum da yamma Hujayrah ta kai ma masu shaguna abinci wa'inda suke a ɗayan layin,har ta kai ta amsa kuɗin za ta tsallaka titi kamar an ce ta wai ga Rasssss!!! Ƙirjinta ya bada ganin Alhaji Sambo Dala ya fito da rantsattsiyar motarsa mai numfashi ya nufa wani babban pharmacy wanda yake a layin da take, sosai hankalinta ya tashi jikinta har jikin ta ya fara rawa, lokaci guda ta rikice ba tare da ta kalli titin ba ta shigo ciki,sai horn ake mata amma ina hankalin ya daɗe da barin jikinta. Ai da wani irin ƙarfi mai motar ya taka birki ji kaka Ƙiiiiiiiiiiiiiiiiiiii, Allah yasa motar ta tsaya wanda saura ƙiris ta bige Hujayrah.
Da sauri mai motar ya fito a fusace yana cewa
"What the hell is wrong with you, makauniya ce ke, bakya gani ne da kawai za ki shigo titi ba tare da kin duba ko akwai motar da take zuwa ba! "
Still jikinta na rawa sannan bata bar yunƙurin tsallaka titi ba ta ce
"Ka yi Haƙuri"
Daga haka ta tsallake titin a guje tsoran kar Alhaji Sambo Dala ya fito daga shago ya sameta.Wawan tsaki mai motar ya ja sannan ya tada motarsa yabar wajen. Hankali tashe Hujayrah ta kaima Hajiya kuɗin abincin,wanda hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Ganin yadda Hujayrah ta kawo mata kuɗi cikin sanyi jiki ga damuwa kwance a fuskarta yasa Hajiya ta tambayeta ko lafiya take ko akwai abinda ke damunta, girgiza mata kai Hujayrah ta yi tana cewa masassara ce take son kamata. Sosai Hajiya ta tausaya mata tare da ɗauko maganin zazzaɓi ta ce kawai ta wuce ɗaki ta kwanta idan tasha maganin tunda bata da lafiya. Amsar maganin ta yi tana mata godiya tabar ɗakin zuwa ɗakinsu,maganin tasha sannan ta kwanta, don ba ƙarya ta yi ba tabbas masassara ce take son yi mata sallama,don har yanzu jikinta bai bar rawa ba. Nan fa ta fara tunanin anya bazata bar gidan abincin nan ba kar wata rana shi ko yaransa su zo nemanta gidan cin abincin nan,gashi yadda taga Hajiya bata da alamar taimaka mata da kuɗin mota kamar yadda ta ce a baya, kodan taga tana jawo mata Customers ne shiyasa bata son tabar gidan abincin. Matsalar har yanzu kuɗin da take tarawa ba za su isheta kuɗin motar zuwa Kaduna ba. Dole ta samo ma kanta mafita kar mutanan su cimmata tunda har ta iya ganin Alhaji Sambo Dala to yaransa ma za ta iya ganinsu tunda suna da yara ba kuma iya tantance su za ta yi ba.
YOU ARE READING
🌍BANI DA MADOGARA🌍
General FictionHujayrah ta kasance yarinya wacca ta fita zakka a gidansu domin a duk familinsu babu baƙi sai ita,dalilin baƙinta da kuma yanayin idanunta tare da baiwsr da Allah ya mata yasa kowa ya tsane,kowa baya sonta,tana fuskantar ƙalubale sosai,ga ƴan secret...