*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*🌍BANI DA MADOGARA🌍*
(Sai Allah.......)*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
( *T.W.A* )*Marubuciyyar:*
*NACINA YA JAWO MIN*
*and*
*BANI DA MADOGARA*
(Sai Allah... )*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link*BOOK* 1⃣
*chapter 18*Daram! Dam! Dammm! Haka zuciyar Murja ta bada, notikan kanta sun fara kwancewa, hankalinta ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, ƙirjinta sai bugawa yake yana bada sautin Fat! Fat! Fat! Ji take duniyar ta juya mata babu sauran komai, hantar cikin tuni ta fara waƙa da rawar wizkid na *ALL MY LADIES* cikinta ya bada sautin ƙulululuuu! Nan take ta fara jin kashi, kai in taƙaice muku Murja bata taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba jin aikinta ba zai yiwu ba, ke nan Jabirunta zai dawwama a ɗan daudu. Nan take Murja ta fashe da matsanancin kuka, cikin kukan ta dubi Malam Tani ta ce
"Yanzu Malam babu abin da za ka iya yi a nan"
Girgiza mata kai ya yi sai ya ce
"Babu abin da zan iya saboda ke ce silar komai, banda makarin wannan asirin, ki tashi ki bani wuri, annamimiyaaa!"
A zafafe ya ƙarashe maganar yana cilla mata wata uwar harara. Jiki na rawa su Murja suka bar ɗakin hankali tashe musamman ita Murja. Koda suka fito kuka Murja take yi sosai su Inna da Zaliha na bata haƙuri. Suna tafiya kafin su samu mashin Murja ta dubi Inna cikin muryar kuka ta ce
"Yanzu Inna shikenan Jabiruna ya koma ɗan daudu gabaɗaya?"
"A'a Murja kin manta Kawunki ya ce yana da wani malamin mai aiki kamar yankan wuƙa,sai muje Maraba daga nan muji ta bakinsa, idan dama taƙi ai sai mu koma hagu. A tunanina za mu samu biyan buƙata a nan shi yasa naga dacewar mu zo nan tunda ba yau ya saba yi mana aiki ba har da Innarki kafin ta rasu, kuma aikinsa na yi sai dai yau na yi mamakinsa wallahi " cewar Inna tana taɓe baki.
Cikin kuka Murja ta ce
"Inna! wallahi ji nake yi kamar duniyar na juyani irin juyin wainar Bauchi, yanzu idan Kawu ya kaimu wurin malamin shi ma ya ce aikin ba zai..."
"A kul ɗinki Murja! Karki ma fara yi ma kanki wannan fatar" Faɗin Inna gyara riƙon ƴar Jakarta.
"Inna zuciyata cike take da tsoro da taraddudi akan wannan aikin" tana maganar hawaye na zuba a bisa kuncinta.
"Ni dai na faɗa miki Murja, ki daina ma kanki mugun fata, atoh!"
Duk wannan hirar tsakanin Inna ne da Murja domin Zaliha ta lula kogin tunanin sahibinta Alhaji Zakari, sai ayyana abubuwa kala-kala take yi a ranta na yadda zamantakewarsu za ta kasance. Ɗan bubbugata Murja ta yi tana faɗin
" Wai ke Zaliha lafiya kike kuwa?"
Kamar wacca aka tsikara firgigit ta dawo cikin hankalinta tana cewa
YOU ARE READING
🌍BANI DA MADOGARA🌍
General FictionHujayrah ta kasance yarinya wacca ta fita zakka a gidansu domin a duk familinsu babu baƙi sai ita,dalilin baƙinta da kuma yanayin idanunta tare da baiwsr da Allah ya mata yasa kowa ya tsane,kowa baya sonta,tana fuskantar ƙalubale sosai,ga ƴan secret...