Chapter 19

99 1 10
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*







   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)


*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )


*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
           {T.W.A}

https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima, rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita,da hikimar mu muke Alfahari_
      
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link

*BOOK* 1⃣
*chapter 19*

Kamar wacca aka tsikara ta yi wuff! Ta miƙe ta shiga cikin garden ɗin  kasancewar babba ne sosai ga kayan marmari da dama an shuka a ciki, tafiya take yi tana tsinkan duk kayan marmarin ya yi mata ba tare da ta wanke ba take sha. Kamar ance ta juyo gefen hagunta, waro dara-daran idanunta ta yi waje ganin Salame tana haƙon rami a gefanta kuma wata ɓaƙar leda ne a ƙulle. Nan da nan Hujayrah ta ɗaure fuska ta nufi inda Salamen take gadan-gadan. Tana zuwa wurin ta tsaya cak! Hannunta riƙe a ƙugu ta ce

"Kutumar uban me kike yi a nan wurin munafuka?"

Da matuƙar tsoro Salame da ɗago daga duƙyen da ta ke tana kallon Hujayrah gabanta sai lugudan bugu yake. Wata uwar tsawa Hujayrah ta daka ma Salame tana cewa

"Ba da ke nake ba ne! Ko halin da kike ce a baya za ki nunamin, shi yanzu kike shirin nunamin?"

Gyara tsayuwa Salame ta yi don a yanzu ta cire tsoron da ya ɗarsu a zuciyarta lokacin da ta yi arba da Hujayrah. Wani munafikin murmushi Salame ta saki sannan ta dubi Hujayrah ta ce

" Ƙwarai kuwa halin nawa zan nunam..."

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba ta ji saukan nushi a hanci da bakinta kamar walƙiya, ai babu shiri Salame ta saki ƙara ita a tunaninta murmujejen dutse ne Hujayrah ta maka mata. Ta yi taga-taga za ta faɗi sai ta yi saurin daidai tsayuwanta don babu ƙarya nushin ya shigeta sosai. Fitar wani abu mai ruwa-ruwa daga hancinta sannan ɗanɗanon miyon bakinta ya canja ta yi saurin saka hannunta ta taɓa hancinta, tana duba hannunta ta waro idanunta waje ganin jini kwance yana bin hannunta, ƙarin mamaki sai sanda ta zubda miyon bakinta taga jini ne, da sauri da kalli Hujayrah kafin ta ce wani abu Hujayrah ta cakumo wuyan riganta tana mata wata iriyar jijjiga mai saka kayan cikin mutum rayar Naira Marley, tayi-tayi ta ƙwace kanta amma hakan ya faskara, daga bayansu suka ji an ce

"Meke faruwa ne?" cikin sanyin murya ya yi maganar

Juyowa Hujayrah ta yi tare da sakin Salame, kamar jira Salame take yi, da gudu ta koma bayan Arqam tana faɗin

"Yallabai ka yi min rai Hujayrah za ta kasheni! Wayyo Allah!"

Bai ce da ita komai ba sai ya juyo yana kallon Hujayrah alamun neman ƙarin bayani, kamar jira Hujayrah take yi tana haki ta ce

"Ya Raqam qam barni da wannan shegiyar, maciyiya amana, cin amanar Mammi take yi a gidan nan, kalla abin da aka aikota ta birne don a illata Mammi! Ai wallahi yau sai Kinci ubanki da dani, sai kin gwammaci kiɗi akan karatu"

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now