*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*🌍BANI DA MADOGARA🌍*
(Sai Allah.......)*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )*TASKIRA WRITER'S FORUM*
( *T.W.F* )*Domin ci gaba da karanta ƙayataccen littafina sai kuyi following ɗina a ɗaya daga cikin wa'innan links ɗin, da littafina na farko mai suna NACINA YA JAWO MIN, Ina maraba lale marhabin da zuwanku,taku har kullum NARRNARHH BUKAR mai alƙalamin ban mamaki wato THE AMAZING PEN✍️*
*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link*BOOK* 1⃣
*chapter 09*Dariya sosai suka tuntsire suna yi, ita Hajiya momma har da riƙe ciki har da baba Uwani sai da ta dara, suna cikin dariyar a banko ƙofar, da sauri suka waiwaya ganin waya ya buɗe ƙofar haka, wata kyakkyawar yarinya ce wacca bazata gaza shekara 15 ba ta shigo da uniform a jikinta, fara ce sosai kana ganinta kaga Hajiya momma, cike da shagwaɓa ta tako har inda iyayanta suke, har ta zauna saman kujera sai ta yi saurin Miƙewa tana kallon Hujayrah ta ce
"Ammie ina muka samu model"
"Aiki aka kawota gidan nan, she is so friendly Razina, you will like her" cewar Hajiya momma tana kallon Hujayrah da murmushi
Buɗar bakin Razina ta ce
"A'a gaskiya Ammie ita ba ƴar aiki bace, kawai ta dawo ɗakina da kwana"
Ba Hujayran ba, Alhaji, Hajiya Momma har da Baba Uwani suka cika da mamakin Razina, musamman Hajiya momma da tasan halin autarta bata son mutane balle ƴan aiki, to amma yanzu fa daga ganin Hujayrah har ta ƙaryata ƴar aiki ce son ma take ta dawo ɗakinta da kwana Ikon Allah. Cike da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskar Hajiya momma ta dubi autarta ta ce
"Razina are you really serious kina son ta dawo ɗakinki da kwana, ke da baki son mutane balle ƴan aiki"
Murmushi Razina ta yi sai ta riƙo hannun Hajiya momma ta ce
"Ammie ai ita wannan she is special ba kamarsu bace, she is damm beautiful, baki ga idanunta ba irin na mutane bane, zan iya cewa for the whole of our planet da matuƙar wuya a samu masu kalar idanunta guda uku ƙwarara, so she is very special, zan bata baƙin glass ɗina ta dinga sakawa idan zamu fita saboda mutane masu magana"
Shiru ɗakin ya yi ana sauraron Razina wacca tsakaninta da Allah take ƙaunar Hujayrah.Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan ya dubi Razina da murmushi ya ce
"Yanzu kina son ta zama ƴar gida kenan Autana, ta yi miki sosai babu matsala"
Gyaɗa kanta Razina ta yi tana duban Hujayrah da murmushi, ita ma murmushin Hujayrah ta mayar mata. Gyaran murya Alhaji ya yi sannan ya dubi Hujayrah ya ce
"Autata Razina tana son ki kasance kamar ƴar gidan nan, don haka dole ne musan asalinki saboda yanzu duniya ba abin yarda bane, dole ka kasance kana taka-tsantsan da mutane, inaso ki sanar mana garinku da asalin maƙasudin fitowarki neman aiki"
YOU ARE READING
🌍BANI DA MADOGARA🌍
General FictionHujayrah ta kasance yarinya wacca ta fita zakka a gidansu domin a duk familinsu babu baƙi sai ita,dalilin baƙinta da kuma yanayin idanunta tare da baiwsr da Allah ya mata yasa kowa ya tsane,kowa baya sonta,tana fuskantar ƙalubale sosai,ga ƴan secret...