Chapter 20

56 2 1
                                    

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*










   *🌍BANI DA MADOGARA🌍*
            (Sai Allah.......)


*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen ✍️* )

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
           {T.W.A}

https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima, rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita,da hikimar mu muke Alfahari_
      
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

*FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y

*FOLLOW ME ON WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

*FOLLOW ME ON AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9

*FOLLOW MY TELEGRAM CHANNEL*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk

*FOLLOW ME ON FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/797576755914199/?ref=share_group_link

*BOOK* 1⃣
*chapter 20*

Gaban kowa sai faɗuwa yake yi suna tunanin meke faruwa ne haka da za a tara manyan mutane da kuma ƴan gari, wani tashin hankali daya matuƙar gigita ƙwaƙwalansu shi ne *Gawawwaki* ne har biyu a kwance an rufesu da zani da alamu gawawwakin na yara ne. Kafin su ƙarasa sai yarinyar Zaliha ta rugo da gudu ta faɗa  jikin mahaifiyarta tana matsanancin kuka duk da ƙaracin shekarunta, jijjigata Zaliha ta fara yi  hankali a matuƙar tashe tana faɗin

"Baraka! Baraka lafiya waya rasu? meke faruwa ne?"

Cikin kuka Baraka ta ce

"Mamaaa idanun Ɗahiru aaaaka ciree, gashi can yyayyanaa bacci..."

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba ta sake fashewa da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwar Zaliha ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni,komai ya tsaya mata cak! Ji take duniyar na  mata juyin waina. Wata razananniyar ƙara ta saki tare da ɗora hannayanta sama tana faɗin

"Wayyoooooo Dahiru naaaaaa!!! Na shiga uku na lalace"

Kafin Murja ta gane meke faruwa sai kawai ta tsinci Zaliha ta falla a guje zuwa wurin gawawwakin, kafin ta yi wani motsi sai ta ji wani sabon ihu na tashi daga bayanta kamar haɗin baki, matar mai unguwa ce amaryarsa ita da wasu mata a bayanta tana gudu zuwa wurin da aka ajiye gawawwakin. Kafin Zaliha ta iso wurin mutane suka hanata zuwa sai haƙuri suke bata, ita kuma ta tirje sai ta je wurin gawawwakin. Suna a haka amaryar mai unguwa ta iso wurin da gunjin kukanta, wasu yara ne suka sanar mata abin da ke faruwa, sai bata yi ƙasa a gwiwa ba ta nufa wurin tare da maƙotan da suke mutunci. Isarta wurin ita da maƙarrabanta keda wurin Zaliha ta yaye zanin da aka lulluɓe gawawwakin. Tashin hankali wada ba a saka masa rana, tuni ta zube warwas a ƙasa sumamma, ita amaryar mai unguwa yaronta ta rumgumo tana sake fashewa da matsanancin kuka mai rasa jini da ɓargon duk wani mai sauraronta. Duka gawawwakin yaran an ƙwaƙule musu idanu, da alamu ba idanun kaɗai aka ƙwaƙule ba har da wasu sassan jikinsu, sosai amaryar mai unguwa take rungume da ɗanta tana kuka. Zaliha kuwa mata ne suka taimaka aka cicciɓeta zuwa cikin gidansu sai Murja ya yayyafa mata ruwa a jiki amma shiru babu motsi. Nan da nan ta kira wayar innar Zaliha da Kawu ta sanar musu abin da ke faruwa. Cike da ɗimautuwa suka ce gasu nan zuwa, babu wanda a garin hankalinsa bai tashi ba,domin duk rashin imaninka idan ka yi arba da gawawwakin yaran nan dole hankalinka ya yi ƙololuwan tashi.

A can daidai wata gindin bishiyar mangwaro na hangi mai unguwa da Alhaji Zakari suna tattaunawa, kowanne ka duba fuskarsa shimfiɗe take da damuwa haɗi ta tashin hankali. Cike da tsantsan tashin hankali mai unguwa ya dubi Alhaji Zakari ya ce

🌍BANI DA MADOGARA🌍Where stories live. Discover now