NIKAAH
(Marriage for Rent)By
AUTHOR HANAADY
09064767796Follow me on
Whatpad
Rahama000HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?Not edited
Page 15
Saurin ri'ke masa riga Alia tayi cikin rashin fahimta tace wai lafiya ka kawo mun wannan unguwar matsiya tan bai bata ansa ba illa ture hannun ta da yayi had'i da nufar k'ofar gidan Jummai ,jiki a mace Alia ta koma cikin motar domin tsorace take ganin ya nufi k'ofar wani gida, kiran number Karime ya yayi, Jummai ce ta d'aga,zaka iya shugowa, jiki na kyarma ya fad'a gidan Jummai.
Kwance take saman sofa, gashin kanta ya zubo k'asan tiles kasancewar ta bama falon baya ,tsugunnawa yayi had'i da shafa gashin kanta Karima ya furta cikin yanayin tausayin Karimen sa , kasa ansawa tayi because her body is weak so weak that she can't even open her mouth, Karima ya kuma furtawa, still bata ansa masa ba ,bana tunanin zata iya magana Jummai ta fad'a,meke damun ta b'acin ciki ta samu zaro idanuwa waje yayi had'i da cewa me taci daya b'ata mata ciki?Allah masani Jummai ta bashi ansa, how many times ta shiga toilet?
Gaskiya ina ga kusan 15 times koma yafi ,sosai hankalin sa ya tashi why baku kirani ba ,mun kira not reachable Jummai ta fad'a, hannuwa yasa had'i da d'aukar Karime jikina kyarma ya fice da ita he can feel how weak her body is, k'ofar baya ya bud'e had'i da sakata, cikin sauri Jummai ta k'araso wajen motar tasu bag d'in Karime ta mi'ka masa .bayan ya zauna ne yace please drive us to K Dara hospital,baki sake Alia tace wacece wannan matar just drive ya fad'a cikin d'aga murya ba tada za'bi daya wuce tabi umarnin sa, please speed up ya fad'a yana mai shafa fuskar Karime.
Bayan Alia tayi parking,saurin fitowa yayi Karime rungume a jikinsa, cikin nuna kula maikatan hospital d'in su kayo kansa ,saman wani bed aka tura ta biye yake dasu har room d'in da aka kwantar da ita , cikin gaggawa aka saka mata k'arin ruwa , idanuwan ta a lumshe suke sama sama take kallon fuskar mijin Sa'ada
bayan an kammala mata treatment d'in fitowa yayi zuwa falon d'akin kasancewar d'akine na musamman, zaune ya tarar da Alia nesa da ita ya zauna dafe kansa yayi sosai yake jin tsananin tashin hankali what if she did not make it wata zuciyar ta fad'a masa ,saurin tashi yayi had'i da komawa bikin room d'in,bacci take Nurse ta fad'a masa, saurin zama yayi had'i da shafa fuskar ta, kissing hannun ta yayi wanda ba'a sakawa drip ba .
Murmushi Dr Aisha sannan tace idan ba damuwa ka koma gida domin d'auko mata wasu kayan because ba a yau za'ayi discharging naku ba duba da yanda tasha jiki sosai why ku kayi delaying wajen kawo ta hospital please next time you should take it serious, because shi zawo ba'a wasa dashi easily mutum yake rasa ransa . Da kai ya bata ansa ,kiran number Sadiq yayi akan shida Rumaisa su d'auko masu kaya suna hospital Karime ce ba lafiya .
A bangaren Alia kuwa brain d'inta sosai ta cunkushe dan ta rasa ta ina zata fara, waccan yarinyar wacece and menene tsakanin ta da Ramadan d'inta,kiran Hjy Mariya ne ya shugo wayar ta saurin d'agawa tayi had'i da cewa kiran kuma na menene ,kina ina my daughter cikin yanayin lallashi Hjy Mariya tayi maganar,bata bama uwarta ansa ba illa katse kiran da tayi ganin Ramadan ya fito daga room d'in da Karima take , saurin nufar sa tayi cikin yanayin fushi tace na kasa gane inda ka dosa shin waccen yarinyar menene had'in ka da ita .
Banza yayi da ita ganin yanda take huci kaman kububuwa yasa ya d'an sassauta yanayin sa dafa ta yayi please calm down umum ana haka Sadiq ya shugo d'akin,juyawa Ramadan d'in yayi had'i da kallon Sadiq hope duk abunda zamu buk'ata ka taho mun dasu?
YOU ARE READING
NIKAAH ( Marriage For Rent)
RomantikHE HAD THE COURAGE TO REMARRY WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN? NIKAAH (Marriage for rent).