DESTINY LOVE

53 1 0
                                    

DESTINY LOVE

OUMYASMEEN









                Oum yasmeen

Ina masoya novels ɗina wannan ba irin wanda na saba kawo muku ne ba yasha ban ban da sauran ƙar ki yarda ayi tafiyar nan babu ke kudai ku biyoni awannan littafi DESTINY LOVE  bana son kana nan maganganu ku dai 🤐

KING AND Queen WRITING CHAMBER

Perfectly pen's



*EPISODE 1-5*

_____________________________________________________________________________________________

Wata iriyar iska ke kadawa gari yayi duhu estate ɗin yayi shiru bakajin motsin kowa sai kukan tsuntsaye bishiyoyi sai rangaji suke sun sami kyakkyawar ni'ima da guri kafin kace me ruwa ya tsuge kamar da baƙin ƙwarya tuni duk wanda ya buɗe window ɗinsa ya rufe wani yarone ya fito fari tas da shi kyakkyawa yana ruƙe da sanda da alama makawo ne duk da ruwan da ke yawa da bakin kwarya ko ajikin sa tafiya yake yazo dai dai kofar da zata sada shi da shashin uncle din sa ya saki wata ƙara wacce tayi amsa kuwa a estate ɗin duk kuwa da ruwan da ke faɗuwa yayi jini ya fara mulala ko da suka jiyo ƙarar nan kasan cewar ana ruwa ba wanda ya fito ko ba'a ruwa dabi'ar family ne ba ruwan wani da wani tamkar bajini daya ba wata iriyar kaddararriyar rayuwa suke me ban mamaki da tsoro haka ya samo asali daga iyayen su sun nuna son ya'yansu dan uwanka be isa ya tsawatar wa da ya'yan dan uwansa ba ran kakansu amma Allah ya jarrabesu da wata irin kaka kanta kadai ta sani ga son duniya da mulki hakan ya samo asali kasan cewar ta jinin mulki uwar attajirai duk wanda ta tsana tofa ya shiga ukku tun tasowar shi besan mahaifiyar sa ba sai mahaifinsa hakan ya samo asali da irin haihuwar sa da akai wani irin ruɗani ke cikin zuri'ar NADER wani irin boyayyen sirri ga sarkakiya dake cikin gidan NADER bankaɗowarsa dai dai yake da tafiyar da numfashin  koma dai mene kudai ku biyoni 

ɗib ruwa ya ɗauke sai sauran yayyafi da ba'a rasa ba wata mota ce baƙa yar gidan Benz tinted mirror ne a jikinta dan haka bazaka iya gano wanda yake ciki ba parking yayi a dai dai shashinsa saboda takardar da yazo ɗauka buɗe motar yayi fararan kafafuwan sa wanda suke cikin half-shoe Black color kallo daya zakai mai kasan ankashe kuɗi wajan siyan sa meroɗiroɗin fatar kaɗa farin yaɗine a jikin sa expensive filtox me wani irin laushi sai zabga ƙamshi yake kai kai kace ɓarar da turare akai kallo daya zai kai mai ka ƙasa ɗauke ido daga kansa saboda kyen sa farine tas sexy eyes ɗin sa yasa medical glass wanda ya ƙara mai kyau ga wata iriyar saje sai sheƙi yake tafiya yake tamƙar wani ɓauna ko zaki lallai yaci sunan nasa da ake ce mai  king of lion  kuma king of journalist duk wani dan jarida inde a Nigeria yake ta biyo bayan sa chak ya tsaya yayin da gudun zuciyarsa ya ƙaru Sultan shine sunan da ya faɗa bakin sa nawani irin rawa wayar sa ya ɗauko hannunsa na rawa bugu daya ya ɗauka daidaita natsuwarsa yayi yace

"Hello commissioner kuzo gidan mu tare da motar jami'an tsaro anyi ƙisa yana kai wa nan ya katse be tsaya jin me zai ce ba ana kaha abbey ya fito daga shashin sa da alama yau beje aiki ba bakin sa narawa yace

"TARÉÊK ,

be juyo ba sai zuciyarsa da ta ƙara tushewa fusƙarsa tayi ja alama yau an kaishi bango kafin ka gane me wanna ƙamilal fuskar me take ciki to ƙana da aiki domin shi ba wanda yake iya fuskantar halin da yake ciki Allah yayi mai juriya tun yana ƙaramin yaro jirgin kwalekwalan rayuwa yake juyi da shi a cikin ruwa wani irin duhu ne a tare da shi har abbey ya ƙaraso gun ya ƙiɗima ganin Sultan a kwance ba rai duban sa yayi yace

"Waya kashe shi?,

be ce mai ƙala ba sai ma ɗaga kafa da yayi alamar shima be sani ba sanin halin sa abbey ya fara kiran yan uwansa kafin kace me duk sun taro gawar aka ɗauka aka kai floor sa dayake nan ya fi kusa iya dukiya an kashe dukiya wani ƙato frame  ɗine a hanyar dining room ya rungume Sultan suna dariya duk wannan fuskar shanon da yake da ita in ka gansa yana wasa sai ka fara tamtama anya kuwa mutum ne domin shi kamar wahainiya yake gurin can zawa komai na floor fari ne da golding

DESTINY LOVEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora