*DAGA MARUBUCIYAR.*
*GIDANMU*
*TA FITA ZAKKA.*
*KANA NAKA*
*TSAKA MAI WUYA**JANAFTY*♥️
*AREWABOOKS:Jamilaumarjanafty*
*WATTPAD: JamilaUmar315**ƊANƊANO DAGA LITTAFIN IDAN AN CIZA.*
Gani take yi kamar a mafarki yau ita ce a gaban Aji tana kallon shi yana kallonta. Yau ita ce ga ta ga shi wanda tazaran dake tsakaninsu bai wuce taku biyu ba, sannan yau ita ce take fitar da numfaashi tare da jin ɗumin numfashin Mansoor a cikin nata numfashin. Farinciki ne ya saka ta kuka yau kimanin shekaru goma rabon da ta saka shi a idanuwanta irin haka. Sai dai ta hango shi a hoto daman ya ce ta yi nisa da ganinsa shima zai yi nesa da jinta da ganinta na har abada. Daɗi ne ya cika mata zuciya da ya sa har ta kasa iya rike kanta sai kuka hawaye suna ta faman sintiti saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya mai kayatarwa.
Shi kuma so yake yi ya hana idanuwansa kallonta amman sun ƙi bashi haɗin kai kamar an manne masa idanuwansa daga kallonta ,ga shi kuma kishi ne da wani irin baƙinciki ke yunkuro masa, in da ya binne tasirin soyayyarta ke kokarin taso masa ya hana tasirin haka bayyana, acikin kirjinsa ya ke jin wani irin zafi zafi iskar wajen ta fara masa kaɗan domin ya ji hucin zafin na fita daga cikin wuyansa zuwa cikin bakinsa, jiyoyin kansa sun mike raɗau kirjinsa na sama da kasa alamun bacin ransa da yanayin da yake ciki ya kai makuran kololiya. Bakinsa ya yi wani irin nauyin da ya kasa mgana duk a kokarinsa ya cira kafarsa da sauri ya bar wajen tun kafin sirrin dake cikin zuciyarsa a kulle a wani bangaren ya fallasa kansa.
Yana ƙokarin ɗauke kafarsa daga gabanta ya raɓa ta gefenta ya wuce ya ji maganarta cikin zaƙin muryanta da tun asali wannan muryan ce ke kwantar masa da hankali. Sannan ganin mai murya na saka shi cikin farincikin da bai san iyaka ba, amman sanadin abunda ya faru yanzu jin zaƙin muryan yake yi kamar saukar dalma acikin zuciyarsa sannan ganinta na sanya sa bakinciki yana guje ma ganinta ne kamar mutuwarsa.
"Aji Nah.."
Ta ƙara kiransa cikin rawan murya sai kawai ya yi kamar bai ji ba, ya ɗaga kafarsa da sauri zai wuceta ita kuma da azama ta riko gefen hannun rigansa domin ba za ta taɓa bari ya subuce ma ganinta ba, yadda ta rikesa ne yasa ya tsaya dole hannunta zara zara da yaji kunshi baki da ja ya bi da kallo rike da gefen hannun rigansa na hagu sannan ya sauke saman fuskarta kallon da ya yi mata ne yasa dole ta sake shi wasu hawayen na kara yi mata ambaliya a saman fuskarta. Tana sakin shi ya fara takunsa cikin sassarfa da gifi gif ɗin sa kamar wani sadauki a fagen yaƙi ji yake yi in bai bar shakan numfashi tare da wannan yarinyar ba za a iya samun matsala.
Kuma cikin su Mu'azzam an rasa mai karisowa kowa ya harɗe hannu a kirji yana kallon ikon Allah. Hatta Rukkaya dake gefe ta kasa karisawa. Tsabar mamaki da al'ajabi ya hana ta magana ballantana ta karisa wajen tambayoyi biyu ne acikin ranta."A ina Mimi ta san wannan baƙin mutumin mai bakin rai haka?
"Me ya sa take kuka saboda ta gan shi?
Wata zuciyar daga can gefen ta faɗa mata" ko dai ko dai shi ne?
Shi ne wannan ɗin nan?Sai ta kara kallonsu tana nazarin wani abu dai dai lokacin da Mimi ta kara tattare riganta ta sha gaban Aji a karo na biyu, wannan karon da karfinta ta tare masa gabansa ta kuma saka hannayenta guda biyu ta tare hanyar tana faɗi da ƙarfi.
"Ba za ka bar nan wajen ba har sai ka yi min mgana, ni ce fa Mimin ka Mansoor?.
Ta faɗa kuka na son ƙwace mata, Mimin ka ce? Kalmar ta fi ɓata masa rai da ya sa a fusace ya kalleta cikin kakkausan murya ya ce"Ni na san ki ne? kin sanni ne?
Ya faɗa yana nuna kansa, jikin Mimi ya fara rawa, ta fara nuna kanta tana rawan baki ta ce" Ni ce fa? ba ka gane ni ba ne?
Kai tsaye ya ce"Ba maganar ganewa ba ne, ban san ki ba, ban kuma taɓa ganinki ba kada ki kara ganina ko a hanya irin haka ki ce kin sanni in ba haka ba zan saka rayuwarki a uku, ni kinga na yi miki kama da sakaran namijin da ya san shashashan mata irin ku? Iyayena talakawa ne har yanzu muna lallaɓa rayuwarmu ne a inda Allah ya ijyemu ba zamu faɗa inda ya fi karfin mu ba."
Ya ƙarishe faɗa ya na nuna ta da babban yatsan da ke hannunsa zuwa lokacin tuni su Rukkaya sun ɗumgume wajen dai dai lokacin da Mimi ta fashe da kuka tana faɗin"Ko ba domin soyayyarmu ba, na ci arzikin kaunar da ta haɗamu ka tsaya mu yi gaisuwan mutumci Aji."
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI