*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA, NA GODE BISA YADDA KIKA YI TA JIMARIN BIBIYAN RUBUTU NA. ALLAH YA RAYA MIKI ZURU'A YA KUMA SADA KI DA DUKKAN ALHERI.*
*LABARIN IDAN AN CIZA. NA MUSAMMAN NE ZUWA GA AISHA UMAR IBRAHIM, DALILIN KI NA FARA ƊORA ALƘALAMINA A KAN WANNAN LABARIN, NA GODE DA ƘAUNARKI GA RUBUTUNA. FATAN ALHERI.*
*GARGAƊI*
*LABARIN IDAN AN CIZA HAƘƘIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE. A GUJI JUYA SHI KO SARRAFASHI TA HANYAR TAƁA SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BA NI DA MASANIYA. YIN HAKAN KAMAR SAƁA MA DOKAR HAƘƘIN MALLAKATA NE A KIYAYE.*
*MANUNIYA*
*LABARIN IDAN AN CIZA ƘIRƘIRAREN LABARI NE. DUK ABIN DA A KA CI KARO DA SHI YA YI KAMCECENIYA NA SUNA KO HALLAYA, GARI KO DAƁI'A. TO A YI HAƘURI AN SAKA NE DOMIN ARASHIN LABARI BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WATA ƘABILA KO AL'ADA BA*
*NA GODE*_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI*_
*Page 1*
*GOMBE STATE: Jihar Gombe*
*3rd, FEBUARY 2022: Uku ga watan Fabareru shekara ta dubu biyu da ashirin da Biyu*.
*DAY: WEDNESDSY: Ranar talata*
*TIME: 10:30AM, Ƙarfe goma da rabi na Safe*
*AREA: Wuri: No.442 Karamchi tv. G.R.A state lowcos*
*PROGRAM: Tare da taurarin Karamchi tv*_Sunana *FATIMA KABIR SULAIMAN DABO* wacce kuka fi sani da (MIMIN KARAMCHI). Ni haifaffiyar jihar Gombe ce a jamhuriyar Nageria. Gombe jiha ce dake Arewa maso gabashin Nageria, ta yi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Barno da Yobe, daga kudu kuwa da jihar Taraba daga kudu maso yamma kuwa da jihar Adamawa sannan daga yamma da jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta ne daga babban birninta, kuma yanki mafi girma a jihar wato babban birnin Gombe. Kuma an ƙirƙire ta ne daga shashin Jihar Bauchi._
_Kamar yadda kuka ji sunan Mahaifina Kabir, wato Major Kabir Sulaiman Dabo. Soja ne da ya sha gwagwarmaya a gidan Soja har ya kai matakin Major kafin ya yi_ _Retire(Ritaya), sunan Mahaifiyata Barrister Murjanatu Soron ɗinki. Bakanuwa gaba da bayanta danginta gabaɗaya mazauna soron ɗinki ne da ke babban Jihar Kano._
_Lauya ce mai zaman kanta dake aiki a babban kotun Abuja wato Supreme Court Abuja. Mu huɗu cif iyayenmu suka haifa ni Mimi ne ce autar su_
_Dr. Sulaiman Kabir Dabo shi ne babba a yanzu haka likitan zuciya ne a asibitin Aminu kano._
_Sai mai bi masa Madiha kabir sulaiman Dabo, ita yar kasuwa ce ita da mijinta suke da kamfanin sarrafa cafet da jakunkuna tare da takalma suna zaune a garin Lagos._
_Sai Khadija Kabir sulaiman Dabo Lectureir ce a Kaduna state University, ita da mijinta dukkan su koyarwa suke yi a jami'ar ta kaduna kuma suna zaune a garin kaduna__Sai ni karamar su FATIMA wacce sunan kakarmu naci wacce ta haifi mahaifinmu wato Hajiyar Shagamu._
_Wacce ta samu asalin sunan Hajiyar shagamu dalilin in aka ce mata wani zai je garin lagos a lokacin sai ta ce zai je dai Shagamu shike nan sai sunan Hajiyar Shagamu ya kama sunanta, in ana kiran gata to ni gata ce da kafafunta, na samu sunan Mimi saboda ina da sunan Hajiya yasa Abi ke kirana da Mimi tun ina ƙarama sai kuma sunan ya yi ta bi na har girmana. Iyayena sun yi zama a garuruwa da dama saboda aikin Abi ammh ni na taso na buɗe idanuwana ne a garin Abuja, tare da iyayena da yan'uwa tun da kuma na taso na ke cikin gata mai suna gata, gani ina da sunan Hajiyar shagamu sannan na shiga ran Abi yana kaunata sosai, na yi karatun primary ɗina zuwa matakin Jss3 a wata private school mai suna Regent Collage Abuja, daga nan sai na koma Jihar Gombe wajen kakata Hajiyar Shagamu dake zaune a gidan marigayi Alhaji Sulaiman Dabo da ya kasance fitatten ɗan jarida, kafin rasuwarsa shine shugaban masu yaɗa labarai na gidan gwammatin Jihar Gombe a wancan lokacin baya da ya shuɗe_
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI