Page 18.

238 8 1
                                    

*IDAN AN CIZA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*

*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*

Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls  bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta🥰kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255

*Page 18*

Huci kawai ya ke saki shi kaɗai ransa in ya kai dubu ya ɓaci Inna ba ta kyauta masa ba, ba domin Baba Ɗanjuma ya ga fitowarsa ba, da anguwan zai bari dole ya yi alwala suka  tafi masallaci tare ana idarwa saboda kada ma su Baba Sani su tare shi ya yi saurin tashi yana kara waya a kunne kamar yana waya Baba Ɗanjuma yana can yana musabaha da mutane Baba Sani da Baba Ɗanlami kuma ganinsa ya sa suke Allah Allah su fito domin su haɗu amman ko da suka fito ya bar haraban masallacin ma gabaɗaya.

  Baba Sani ya jinjina kai kafin Ya ce
"Ɗanlami wai ka lura yaro nan yana gudun mu ne yanzu? Baba Danlami ya yi kayfci kafin ya ce"Wlh nima na lura, ka bar mutum kawai saboda kuɗin da yake ba mu ne duk wata sai ɗan taimako in ya taso, ba dole ya ganmu ya yi wucewarsa ba tunda ga yan maula." Baba sani ya yi shuru kafin ya ce"Laifin duk na Yaya Ɗanjuma ne, in da amana muma fa muna da hakki akan dukiyar yaron nan tunda ai gidan uban mu aka riƙe shi, amma ya tattare komai ko nuna masa matsayin mu ba ya yi yadda ake ba ni labarin kuɗin yan ƙwallon kafa wlh zai iya kai mu saudiya ma sannan ya siya mana manyan gidaje a garin Abuja da motoci."

  Baba Ɗanlami sai da ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Haba! to ai naga shi ma Yaya Ɗanjuma bai kai shi Saudiyan ba ma sannan bao sai siya masa mota ba, ya dai gyara gidan ya siya masa mashin itama tunda aka sace ai bai kara siya masa ba, kai ko uwarsa Meri ai ba kai saudiya ba mu kuma a suwa? Karan kaɗa miya."
Baba Sani zai yi mgana kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya zo wajen sai ya yi shuru hannu ya ba suka yi yi musabaha daman tunda ya gan su yasan da wata mgana.
Baba Ɗanlami ne ya fara faɗin.
"Yaya Danjuma gaskiya ka yi ma yaron nan Mansoor mgana, kamar mu zai gani ya rika wulakantawa? Baba Ɗanjuma ya yi saurin cewa"Anya? Ko dai bai gan ku ba ne?
Baba Sani ya ce" Zencen kake so, ya fa ganmu amma sai ya ɗauke kai ya yi wucewarsa in ma saboda ɗan abin da yake ba mu ne ya ke ganin kamar ya na yi mana alfarma gwara ka gaya masa gaskiya muma muna da hakki a kansa tunda ya tashi a ƙarkashin mu, duk tsiya dai a gidan Wanzamai ya tashi kuma da gidan zai yi tutiya yau ko saudiya ya kaimu bai biyamu rikon da mu ka yi masa ba ahto."
Baba Ɗanlami ya ƙarishe da faɗin"Ka ji zencen gaskiya." Baba Ɗanjuma bai yi mamaki ba sanin halin ƴan uwan nashi kamar waɗanda suka taɓa tsinana ma Mansoor ɗin wani abu suna ta kumfar baki,  baya son nana ta mgana ɗaya ya sa ya ba su hakuri yace zai yi masa mgana.

  Ashe korafin na su ba ɗaya ba ne nan take Baba Ɗanlami ya kalli Yayan na shi yana faɗin" Shi kuma Mu'azzamu dai ya manta damu? Ko wancan zuwa ma bai bari mun haɗu ba, ina ga ko ya yi saƙo iya kai da Meri saƙon ke zuwa gare ku, domin ba na jin ko Magajiya tana samun wani abu aciki."
Sai alokacin ya buɗe musu ido cikin gargaɗi ya ce"Ko ni da na haifesu ban kwanta a gida na dogara da su ba, suma ai suna da na su uzurin rayuwar duk abin da kuka ga ba'a baku ba ba'a kawo ba ne, wani abun ma ba na sanin da shi ake ɗauka a baku ba  yaran nan duka biyu daga Mu'azzamu har Mansoor ɗin ba sa yi min abu ba su yi muku ba ko da ɗinki ne na kaya domin ɗaya suke ɗaukan mu, kune da shigen zarge zarge da tsegumin ku da ya sa kuka kasa fahimtar komai ballantana ku godema Allah Bisa ni'imar da ubangiji ya yi muku."

IDAN AN CIZA..!Where stories live. Discover now