*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*NA GODE.*
*ZAINAB INUWA(MY ANTY)*
*MARYAM JUMARE*
*NANA HALIMA(MASOYIYA)*
*AISHA ALTO(SISINAH)*
*SURAYYA DEE**KUN YI TA JIMARIN YAƊA WANNAN LITTAFIN TUN DAGA RANAR FARKO HAR ZUWA YAU DA SHAFUKAN KYAUTA SUKA ZO ƘARSHE, NA GODE ALLAH YA BAR ZUMUNCI AMIN*
*Tushen labarin ne a littafi na ɗaya, cin uban sabadan yana cikin littafi na biyu har zuwa na uku, akwai soyayya mai tsayawa a zukata bayan dabarwan dake ciki, ga dai Aji ga Mimi shin me yake shiryawa da ya amince da auranta? Ko yana nufin ya yafe ɗin ne? Akwai sauran rina a kaba tabbas, ku ƙara zaɓa ta ina mai ba ku tabbacin ba zan ba ku kunya ba in sha Allahu. Ku yi tururuwan biya domin sai kun cika adadin sannan zamu fara littafi na biyu, daga yau zuwa gobe da jibi in sha Allahu Na gode.*
*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*07030645342*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.
*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0
*Page 20*
An raba iya ada din dukiyar da Abi ya mutu ya bari, an kuma raba shi dai dai yadda addini ya hukunta. Tare kuma da malamai da alkalai aka yi rabon a gaban Daddy da yaran duka sai Hajiya har da Yaddiko. Hajiya ma ta samu gida tunda ya bar gidaje da motoci da kuɗi ma su yawa a cikin banki, sannan gidan da Mommy ke ciki ita da Sulaiman suka ci gidan shi kuma ya ce ya bar mata halak malak domin ta cika wasiyar mijinta ta ce za ta cigaba da zama a gidan tun da ga aikinta sannan gefe ɗaya ta ce za ta je kano ta ɗauko ƴaƴan ƴan'uwanta saboda su taya ta zama tunda Inna Ladidi za ta koma gida bayan ta fita takaba.
Kwanan su huɗu ne su ka dawo, Mommy kuma washegari ta bi Jirgi zuwa kano ita da Inna Ladidi za ta raka ta sannan itama ta je gida ta gaida ƴan'uwa da iyaye. Rana ɗaya su ka tafi da Khadi ita ta yi kaduna ita kuma Madiha kwananta uku ne ta bi Jirgi ta koma Lagos Mimi da Hajiya da Daddy da Yaddiko tare sua je kuma tare su ka dawo Gombe gabaɗaya. Ko bayan an gama rabon gadon Mommy ta so ta yi mganar Mimi sai kuma ta fasa a cikin ranta ta kuduri niyar daga kano Gombe za ta sauka sai an san yadda za'ayi daga can. Ba ta ɗauka ma za ta jima a kanon ba sai ga shi ta yi sati biyu daga kanon ne ta biyo Gombe Hajiya ma ba ta san tana tafe ba, tunda ba ta faɗa mata ba ta dai san sun rabu akan cewa daga kanon za ta biyo nan. Mimi kuma ba ta ɗauka zuwan Mommy da wani abu ba,ta ɗauka dai ta biyo ne kafin ta koma Abuja ta kuma ji daɗin zuwan Mommy domin hakan ya bayyana har saman fuskarta.
Zuwan Mommy ya sa Hajiya ta ƙara kiran Inna Meri a waya a nan ne ma take jin labarin ashe ta zo ba su nan Hajiya ta ba ta hakuri ta ce ta bar wayar a gida ne, ba ta je da ita ba amman in ta na gida za ta shigo ko yau da yamman ko zuwa gobe. Ita kuma Inna Meri surutun mutane ne ba ta so sai ta ce ma Hajiya ta bari ita za ta zo, Amman Mommy ta nuna gwara su je da kansu su suke nema bai kamata su tsaya jiran sai ta zo ba. Da haka suka tsara zuwa gidan Wanzamai ba tare da kowa ya sani ba ita kanta Mimi ba su yi mgana da ita ba, ba kuma ta san abin da suke shiryawa ba.
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI