*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA.*
*MADALLAH DA SURAYYA DEE, ALLAH YA CIKA MIKI DUKA BURIKAN KI NA ALHERI YA BA KI SANYIN IDANIYA AMIN.*
*FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA ƊIN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI*
*NA GAISHE DA IYAYEN ƊAKINA*
*ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA HALIMA ƊALHA SHEHU.*
*ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*ANTY SALAMATU ABUJA.*
*ANTY FADILA KABIR*
*ANTY FIDDAUSI KABIR**FATAN ALHERI NAGODE*
*INA GAIDA MARUBUTA, KARAMCINKU ABUN YAƁO NE. ALLAH YA ƘARA BASIRA ƳAƳAN BAIWA AMIN.*
*Page 2*
A tsakiyar falon ya ci karo da Inna Meri tana tsaye ita da Walida, ya yi sallama suka amsa gabaɗayansu. Tun kafin ya buɗe baki ya fara gaishe da Inna Walida ta yi zaraf ta ce"Yayanmu barka da dare"
Saboda sanin halinsa yanzu tana cewa ina yini sai yace bai ga yinin ba, sai dai ta ce masa barka da dare. Cikin mamakin ganinsu a tsaye ya ce"Barkan mu lafiya na gan ku a tsaye, Innanmu lafiya kuwa?.Inna Meri wata bakar dattijuwa kallon farko za ka yi mata ka fahimci ta fito daga shiyar sokkoto ne, sannan ta haɗa jini da Arawa, saboda gefen bakinta dama da hagu ga zanenta na Arawa nan ɓaro ɓaro ya bayyana duk da ko ta na baƙa na iya ganinsa. Sannan sai alokacin na fahimci in da Mansoor ya ɗauko tsawon sa, Inna Meri doguwa ce sosai mai kaurin jiki kuma.
A shekarunta iyakarta 56 zuwa da bakwai a duniya ba ammh yanayin jikinta bai nuna wahala ba sosai tana sanye da hijabi ne a jikinta hannunta kuma casbaha ne, daga gani ta idar da sallar mangariba ne tana lazimi. Cikin yanayin maganarta ta ce"Tun da naji Kwakwazon Magajiya na ce to Baban Inna ya shigo gidan" Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Walida tayi saurin shimfiɗa masa darduma sanin halinsa bai son zaman kujera duk ko da irin tuma tuman kujerun alfarman dake mamaye da falon na inna Meri ko wata amarya albarka. Cikin natsuwarsa ya zauna itama Inna Meri sai ta samu daga gefensa ta zauna saman cafet mai taushi dake malale a cikin ɗakinta.Cikin yalwataccen fara'an da ba a raba fuskarta da shi ta ce" Tun fa ɗazu muke ta duban hanyan ka ni da Babanku muka ji ka shuru." Daman yasan tuni labarin dawowarsa ya zo musu tunda Mu'azzam ya ji labari. Kansa na kasa ya ce"Innarmu kun yi mgana da Mu'azzam ne?
Cikin jimami ta ce"Ya kirani kamar ya yi kuka Baban Inna ba ka kyauta ma ɗan Innna ba gaskiya, me ya sa ba ka je ka duba ɗan uwanka ba?
Kai tsaye Ya ce"Inna wasa muka je bugawa kamar kuma wani mace sai a ganni daga zuwa wasa ina faman biye biye
Inna Meri ta ce"To menene? ba wajen ɗan uwanka za ka je ba? ya ce matarsa ta kasa zama waje ɗaya saboda zuwanka maganar gaskiya Baban Inna ba ka kyauta ba."Ba ya son jan mganar ya sa Ya ce"Shike nan ki yi hakuri Innarmu, Ina Baba ko a masallaci ban gan sa ba?
Inna Meri tace"Tun ɗazu abokinsa Mallam Hashimu ya kirasa kan dai zaman da ake yi akan auran ƴarsa maigado shi ne ina ga har yanzu ba su kai ga matsaya ba."
Cikin mamaki Ya ce"Auran ya mutu ne?
Tana gyara zama ta ce"To abin dai nasu sanin gaskiya sai Allah ita ta ce ya saketa shi kuma ya yi rantsuwan bai furta mata saki ba sun dai yi sa'insa har ya dake ta"
Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba, yana ji Inna Meri ta cigaba da ba sa labarin yadda akayi jin ta kawai ya ke yi hankalinsa na wani wajen kuma.Walida ya ke hangowa ta cikin uwar ɗakin Inna Meri ta na karatu sai dai baisan me ta ke karantawa ba. Ya buɗe baki zai kwala mata kira kenan Inna ta riga sa, tana fitowa ta kalleta tana faɗin"Ke mara wayau baki kawo ma yayan naku ko ruwa ba?
Da sauri Ya ce"Ba na jin kishi Inna".
Kallonsa ta yi kafin Ta ce"To abinci fa?
Kai tsaye Ya ce"Inna zan ci tuwo ammh ba yanzu ba sai na kusa tafiya."
Daga haka ta girgiza kanta kafin ta ce"Shike nan kun dawo oafiya ko? Ina fatan an samu nasara? Cikin sakin fuska ya ce"Lafiya lau Innarmu, an samu nasara in sha Allahu."
Nan Inna ta cigaba da kwararo addu'o'i yana amsa mata da Amin Amin. Walida kuma tsalle ta buga tana faɗin.
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI